Shatale-talen da aka yi wa laƙabi da kwanar mutuwa

Shatale-talen da ke kusa da gidan mai na Total da ke karamar Keffi a jihar Nasarawa waje ne da aka yi wa laƙabi da kwanar mutuwa saboda yawan haɗarin motar da ke faruwa a dai-dai wajen.
A dai-dai wajen dai akwai ƙaramar kasuwa da ke ci ba dare ba rana ga kuma cunkoson mutane da ababan hawa abin da ake ganin na ɗaya daga cikin abin da ke janyo afkuwar haɗari ke nan a wajen.
Da wuya a yi mako guda ba a samu afkuwar haɗarin mota kona mashin a wajen ba kuma a yawancin lokuta haɗarin kan yi muni sosai harma ta kan kai ga rasa rai da kuma jikkata mutane.
Mutanen da ke zaune a kusa da shatale-talen dama wadanda ke kasuwanci a kasuwar kusa da wajen na kokawa da yawan haɗuran da ake yawan samu a wajen.
Ɗanladi Lawan, yana zaune a wajen, ya shaida wa BBC cewa a kodayaushe suna faɗawa mutanen da suka gansu sun tsaya a dai-dai shatale-talen da su bar wajen domin idan ba su yi aune ba za su iya ganin mota ta yiwo kansu.
Ya ce,"Mummunan wuri ne wajen saboda idan mota ta gangaro ba a iya sani sai dai kawai kaji ana ihu kuma kafin kace meye wannan lamari ya lalace."

Ɗanladi Lawan ya ce, manyan motoci sune suka fi haddasa haɗari a wajen saboda birkinsu bashi da tabbas.
Shima Magaji Small, ya shaida wa BBC cewa, irin abubuwan da ke faruwa a shatale-talen Total ya ɓaci sosai don har abin ma ya fara basu tsoro ma.
Ya ce,"Tankar mai sun fi goma da suka faɗi a wajen a kan idona, kuma idan tankar man ta faɗi jama'a na zuwa su ɗebi mai."
Isma'ila Isa kuwa kira ya yi ga gwamnatin jihar dama ta tarayyar a kan a ɗauki mataki na gyara shatale-talen saboda irin illar da ya ke janyowa.
Hukumomi a jihar ta Nasarawa dai na cewa suna sane da abubuwan da ke faruwa a wannan shatale-tale, to amma suna ɗaukar matakai wajen kawo karshen hakan.
Asst Kwamanda Awwal Magaji Muhammad, jami'I ne a hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta Najeriya reshen jihar Nasarawa ya ce, suna iya bakin ƙoƙarinsu wajen wayar da kan mutane a kan yadda za su yi tuƙi musamman akan manyan hanyoyi.
Ya ce,"Muna faɗawa mutane a kodayaushe akan su rinka kula da dokokin hanya tare da bin ƙa'ida.Abin da muke gani yakamata ayi a wannan waje shi ne gadar sama don hakan ya kawo sauƙi da kuma raguwar afkuwar haɗura a wannan shatale-tale."
Yawanci dai ana danganta faɗuwar motoci musamman manya da kuma afkuwar haɗura a titunan Najeriya da rashin kyauwn titunan, yayin da wasu ke ganin rashin bin ka'idojin hanyar ce ke haddasawa.
Masana dai na da yaƙin cewa kamata ya yi hukumomin Najeriya su ɗauki matakan ilimantar da direbobi wajen yi musu bita a koda yaushe kan yadda za su riƙa tafiyar da sana'ar su cikin ka'ida, kana a ci gaba da nuna wa al'umma haɗarin zuwa kusa da babbar mota bayan ta fadi musamman don ɗibar kayan da take ɗauke da shi.











