Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da muka sani game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Isra'ila da Hamas sun amince da zangon farko na yarjejeniyar zaman lafiya ta Gaza.
Wannan dai na zuwa ne bayan shekaru biyu bayan ƙaddamar da yakin da Isra'ila ta yi a Gaza martani kan harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da ƙungiyar Hamas ta kai Isra'ilar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 1,200.
Aƙalla Falasɗinawa 67,183 ne dakarun Isra'ila suka kashe a yayin yaƙin kuma ciki har da ƙananan yara 20,179 kamar yadda ma'aikatar lafiyar Gaza ta ayyana.
Ga abubuwan da muka sani dangane da yarjejeniyar da ma abubuwan da ba su fito fili ba.
Me aka sanar?
Bayan tattaunawa mai tsawo a Misra, Isra'ila da Hamas sun maince da zangon farko na yarjejeniyar da Amurka ta tsara, in ji shugaban Amurka.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Isra'ila da Hamas sun amince da matakin farko na yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
A wani saƙo da ya wallafa a kafarsa ta sada zumunta ya ce hakan na nufin nan ba da daɗewa ba za a saki dukkanin wadanda ake garkuwa, sannan Isra'ila za ta janye dakarunta.
Ya ce wannan mataki ne na farko na tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa. "Za a yi wa kowane ɓangare adalci," in ji Trump.
Kungiyar Hamas ta tabbayar da cimma yarjejeniyar ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza bayan tattaunawa kan yarjejeniyar Donald Trump.
Hamas ta ce yarjejeniyar ta ƙunshi janyewar Isra'ila daga yankin da kuma musayar fursunoni da kuma mutanen da aka yi garkuwa da su.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce zai jagoranci taron gwamnatinsa domin amincewa da yarjejeniyar da kuma dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su.
"Wannan babbar rana ce ga Isra'ila," in ji Netanyahu tare da gode wa shugaba Trump.
Donald Trump ya ce wannan babbar rana ce ga kasashen Larawaba da na Musulmi da Isra'ila da dukkanin ƙasashe da kuma Amurka. Sannan ya gode wa ƙasashen Qatar da Masar da Turkiya da ke shiga tsakani a tattaunawar tsakanin Hamas da wakilan Isra'ila da na Amurka.
Wannan na zuwa a yayin da shugaba Trump ya ce yana tunanin kai ziyara yankin Gabas Ta Tsakiya a ƙarshen mako domin halartar Masar inda ake gudanar da tattaunawar.
Tatattaunawar a rana ta uku tsakanin Isra'ila da Hamas ta mayar da hankali kan fursunonin Falasdinawan da za a yi musayarsu da waɗanda Hamas ke garkuwa da su.
Me zai faru nan gaba?
A ranar Alhamis ɗin nan ne gwamnatin Isra'ila za ta kaɗa ƙuri'ar amincewa ko watsi da yarjejeniyar.
Idan suka amince da ita a hukumance, to Isra'ila dole ne ta janye dakarunta daga Gaza zuwa wajen da aka yarda su tsaya, in ji wani babban jami'in Fadar White House kamar yadda ya shaida wa gidan talbijin na CBS, mai ƙawance da BBC. Akwai yiwuwar jaye sojojin na Isra'ila ka iya wakana a cikin sa'o'i 24, in ji jami'in.
Bayan faruwar hakan, dole ne Hamas ta saki ƴan Isra'ilan da take riƙe da su a cikin sa'a 72.
Akwai yiwuwar sakin mutanen ya fara ranar Litinin, kamar yadda babban jami'in na Fadar White House ya shaida.
Abin da muka sani
Abin da aka sanar yanzu kashin farko ne na abubuwa 20 da yarjejeniyar da Trump ya tsara, wanda Isra'ila ta amince da ita sannan Hamas ta amince da wani ɓangare na yarjejeniyar.
Sai dai kuma sanarwar ba ta haɗa da wasu batutuwa masu sarƙaƙiya ba daga dukkannin ɓangarorin ba su cimma matsaya a kai ba.
Misali babu cikakken bayani dangane da ajiye makaman Hamas wadda babban batu ne a tsarin yarjejeniyar ta Trump.
A baya dai Hamas ta sha ƙin amincewa ta ajiye makamanta, inda take cewa za ta yi hakan ne kawai bayan cimma ƙasasr Falasɗinu mai zaman kanta.
Jagorancin Gaza a nan gaba ma batu ne da ke da sarƙaƙiya. Tsarin na Trump ya nuna Hamas ba ta cikin ɗaunin mulkin zirin Gaza, inda tsarin ya bayar da shawarar kafa wani ƙwarya-ƙwaryar kwamitin ƙwararru da zai jagoranci yankin kafin miƙa mulki ga gwamnatin Falasɗinawa.
Da alama Netanyahu ya yi watsi da shigar da gwamnatin Falasiɗinawa ta Palestinian Authority cikin tsarin mulkin zirin duk da cewa akwai hakan a tsare-tsaren na Trump.
Masu tsattsauran ra'ayi na gwamnatin haɗaka ta Netanyahu waɗanda da dama daga cikin su suke son sake gina matsugunan Yahudawa ƴan kama wuri zauna a Gaza, su ma akwai yiwuwar za su yi watsi da wannan batun.
A martaninta, Hamas, ta ce har yanzu tana sa ran a dama da ita a jagorancin Gaza.
Bugu da ƙari, ya zuwa daren ranar Laraba, Hamas ba ta samu jerin sunayen fursunonin Falasɗinawa da Isra'ila za ta saki domin musayar Isra'ilawar da Hamas ɗin ke garkuwa da su a Gaza, kamar yadda wani ɗn Falasɗinu ya shaida wa BBC.
Daftarin mai sassa 20 ya shimfiɗa cewa za a saki Falasɗinawa 250 da suke zaman ɗaurin rai da rai tare da ƴan Gaza 1,700 da Isra'ila take tsare da su bayan ranar 7 ga watan Okotoban 2023.