Shin Isra'ila da Hamas za su kawo ƙarshen yaƙin da aka shekara biyu ana gwabzawa?

    • Marubuci, Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International editor, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 5

Bayan shekara biyu ana gwabza yaƙi, alamu na nuna cewa za a cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da kashe-kashe a Gaza tare da sakin Isra'ilawa da Hamas ta yi garkuwa da su, su koma wajen iyalansu.

Wannan wata dama ce babba, amma har yanzu babu tabbacin Hamas da Isra'ila za su yi amfani da ita domin magance yaƙin.

Wani abun mamaki shi ne yadda tattaunawar sasanci ta zo a daidai lokacin da ake cika shekara biyu da harin na Hamas.

A harin na ranar 7a ga Oktoba, Hamas ta kashe kusan mutum 1,200, yawanci fararen hula, sannan ta yi garkuwa da mutum 251.

Isra'ila ta ce har yanzu akwai aƙalla ƴan ƙasarta 20 da suke raye a hannun Hamas, sannan tana so a mayar mata da gawar mutum 28.

Martanin Isra'ila na ramakon gayya ya yi sanadiyar ɗaiɗaita Gaza, sannan ta kashe kusan mutum 66,000 yawanci fararen hula, ciki har da ƙananan yara 18,000.

Wannan adadi ne da ya fito daga ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin Hamas, kuma akan amince da alƙalumanta.

Amma wani bincike da mujallar Lancet ta Landan ta ce kashe-kashen ya wuce haka.

Isra'ilawa da Falasɗinawa duk suna so a kawo ƙarshen yaƙi. Wani bincike ya nuna cewa mafi yawan ƴan Isra'aila suna so a shiga yarjejeniyar mayar musu da ƴanuwansu da Hamas ta yi garkuwa da su sannan a kawo ƙarshen yaƙin.

Haka kuma dubban sojojin kar-ta-kwana na Isra'ila da ke fagen daga sun ƙosa su koma wajen iyalansu bayan watanni suna gwabza yaƙi.

Aƙalla Falaɗinawa miliyan biyu ne suke cikin mayuwacin hali a Gaza da suke neman agajin gaggawa, inda suke tsakiyar luguden wuta daga sojojin IDF da kuma yunwa da ta musu katutu a sanadiyar hana shigar da kayan agaji da Isra'ila ta yi zuwa zirin.

Asalin rundunar Hamas ɗin mai ƙarfi da ta kai hari a Isra'ila shekara biyu da suka gabata ta riga ta ragargaje, inda yanzu dakarunta ne suke ci gaba a yaƙin sari ka noƙe da sojojin IDF na Isra'ila a Gaza.

Hamas na neman hanyoyin da za ta ci gaba da wanzuwa, duk da cewa ta amince ta ba shugabannin Falasɗinu mulki, ta kuma amince za ta miƙa wasu daga makamanta.

Amma ta ce za ta ajiye wasu daga cikin manyan makamanta domin kare kanta daga Falasɗinawa da take fargabar za su iya kai mata harin ramako saboda shekarun da ƙungiyar ta yi tana mulkinsu.

Ba wai magana ba kawai, amma lallai ƙungiyar da take da ɗimbin masoya da kuma burin ganin bayan Isra'ila ba za ta iya sakin layin da ta ginu a kai ba.

Isra'ila za ta so a ce ita ce kan gaba wajen tsara yadda Hamas za ta miƙa wuya.

Amma dai yanzu Hamas na da damar tattaunawa domin tsara yarjejeniya sama da yadda abin yake a watan jiya a lokacin da Isra'ila ta yi yunƙurin kashe jagororin Hamas a wani hari da ta kai a Doha na Qatar, wanda ba ta samu nasara ba.

Babban wanda Isra'ila ta hara shi ne wani babban jigo na Hamas Khalil al-Hayya wanda ya jagoranci tawagar wakilan Hamas.

Ɗansa Al-Hayya na cikin waɗanda suka rasu, amma da shi da sauran jagororin ƙungiyar sun tsira.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana da abubuwa da ke gabansa.

Yana so ya ci gaba a zama a mulki, yana so ya ci gaba da ɗage zaman sauraron ƙarar zarginsa da cin hanci, sannan yana so ya lashe zaɓen baɗi, sannan ba ya so a tarihi ya kasance shugaban da aka kai hari mafi muni a ƙasar tun bayan harin kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa.

Domin samun wannan nasarar, dole yana buƙatar hanyoyin da zai bi wajen sanar da "cin nasara baki ɗaya" kamar yadda ya ke yawan faɗa.

Ya ce wannan nasarar ita ce kuɓutar da waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su, wargaza Hamas da tsame Gaza daga masu riƙe da makamai.

Idan bai samu hakan ba, ba zai samu hujjojin da zai bayyana ba ba a matsayin cikakkiyar nasara duk da irin yaƙin da ya yi a Lebanon da Iran a cikin shekara biyu ɗin.

Hamas da Isra'ila ba za su haɗu ƙeƙe da ƙeƙe ba, sai dai wakilan Masar da Qatar ne za su kasance masu shiga tsakani, sai kuma Amurka da za ta sa ido.

Yanzu dai kallo ya koma kan batun yarjejeniyar. Akwai yiwuwar a samu maslaha domin yaƙin ya tsaya.

Babban ƙalubalen shi ne tsarin sakin waɗanda Hamas ke garkuwa da su tare da musayarsu da Falasɗinawa da ke kurkukun Isra'ila da ma wasu da ake tsare da su ba tare da hukunci ba tun farkon yaƙin. Wannan abu ne mai sauƙi.

Shugaba Trump yana so a gudanar da komai cikin sauri, yana so ya sake yunƙurinsa na gyara al'amura a Gabas ta Tsakiya, musamman gyara alaƙa tsakanin Isra'ila da Saudiyya.

Wannan zai yi wahalar gaske matuƙar Isra'ila na ci gaba da luguden wuta a Gaza tare da hana shigar da kayan agaji.

Haka kuma Saudiya ta sha bayyana cewa hakan ba zai yiwuwa ba har sai an tabbatar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu.

Trump ya tursasa Netanyahu sanya hannu a wasu takardu da a ciki akwai alamun kama hanyar samar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu.

Amma a sanarwar bayan taron sai Trump ya waske, inda ya sake nanata cewa Falasɗinu ba za ta samu ƴanci ba.

Haka kuma Trump ya tursasa Netanyahu ya kira tare da neman afuwar Firaministan Qatar kan hare-haren da ya kai a ƙasar kan jagororin Hamas.

Abin tambayar a nan shi ne me ya sa Hamas ta amince ta bayar da Isra'ilawan da take garkuwa da su ba tare da an bayyana yaushe sojojin IDF za su fice daga Gaza ba?

Wataƙila Qatar ta taka rawa a nan wajen gamsar da ita cewa Trump zai tabbatar da yiwuwar hakan.

Haka kuma Trump na amfani da yaren da Netanyahu ke so, kamar barazanar da yake yi wa Hamas cewa zai ba Isra'ila goyon baya domin kawo ƙarshen Hamas.

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce nan da kwanaki kaɗan za a tantance idan Hamas da gaske ta ke.

Trump ya yarda kana wajen cimma yarjejeniyar sulhu. A diflomasiyyar ƙasashen waje, har yanzu dai ba a gani a ƙasa ba domin har yanzu bai cimma nasara ba.

Ya gaza wajen sasanta yaƙin Rasha a Ukraine bayan ya yi alƙawarin yi a ranar farko a mulki, amma wata ƙwarewa da Trump yake da ita ita ce samun abin da yake so ta hanyar tursasawa.

Babban bambancin Trump da sauran shugabannin Amurka irin Clinton da Obama da Biden shi ne yadda Benjamin Netanyahu ba ya iya juya shi yadda yake so.

Isra'ila da Amurka ƙawayen juna ne. Amurka na matuƙar taimakon Isra'ila a yaƙin, domin ba don taimakon Amurka ba, Isra'ila ba za ta iya yaƙin nan ba saboda yawancin makamanta daga Amurka take samu.