Halin da ake ciki a Mayotte bayan mahaukaciyar guguwar Chido

Mayotte tsibiri ne a Faransa
Lokacin karatu: Minti 2

An gaggauta tura dakarun Faransa da ma'aikatan ceto da na agaji Mayotte ta jirgin sama da na ruwa domin taimakawa mutane da mahaukaciyar gugguwa ta afkawa, irinta mafi muni a cikin karni, a yankin da ke tekun Indiya.

Guguwar da aka yi wa laƙabi da Chido ta yi kaca-kaca da tsibirin a ranar Asabar, sannan ana fargabar ɗaruruwan mutane sun mutu.

Ɗaruruwan ma'aikatan agaji ne har ma da ƙarin wasu da aka turo daga Faransa ke ta aiki ba ji ba gani suna ta tona ɓaraguzai da tarkace, inda suke neman mutanen da ake sa ran suna da sauran numfashi, bayan da mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwan sama ta yi kaca-kaca da yankin Mayotte wanda ke ƙarƙashin Faransa a yankin tekun Indiya.

Guguwar ta baje kusan gaba ɗaya garuruwan da yawanci aka gina gidajensu da langa-langa ko kwano a kai da jikin tsaunuka

Guguwar da ke tafiyar kilomita 225 a cikin sa'a ɗaya, ta yi kaca-kaca da waɗannan yankunan da ke ɗauke da kusan ɗaya bisa uku na yawan al'ummar Mayotte.

Aikin agajin ya gamu da cikas sosai saboda ɓarnar da guguwar ta yi wa kusan duk wasu abubuwa na jin daɗin al'umma.

Turaku da wayoyin lantarki da kuma kayan sadarwa sun zube, tituna sun toshe da tarkace da ɓuraguzai – ba hanya, sannan kuma gine-gine da dama sun lalace.

Filin jirgin sama da asibitoci duk sun gamu da mummunar barna. Jama'a na kokawa da rashin kayayyaki ciki har da ruwa.

A yau Litinin ake sa ran ministoci biyu ciki har da ministan cikin gida na Faransa za su je yankin na Mayotte domin duba irin ta'annatin da guguwar ta yi, da kuma tsara karin aikin agaji.

A halin da ake ciki kuma mahaukaciyar guguwar mai tafe da ruwan sama da ta yi wannan barna- da aka yi lakabi da Chido ta sauka a birnin Pemba da ke gabar teku a kasar Mozambique tun a jiya Lahadi – inda ta tuge bishiyoyi da barnata gine-gine ta kuma haddasa ambaliya.

Yayin da karfinta ke raguwa kuma – yanzu ruwan sama da iska mai karfin gaske na durfafar yankunan kudancin Malawi da Zimbabwe.

Mayotte

Asalin hoton, Getty Images