Yadda za ku kare kanku daga cutukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i

Asalin hoton, Getty Images
Cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i, cutuka ne da ake yaɗawa daga mutum zuwa mutum bayan yin mu'amalar saduwa.
Ana ɗaukar cutuka sama da miliyan ɗaya a kowace rana a faɗin duniya ta hanyar jima'i, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.
Waɗannan cutuka ba su cika nuna wasu alamomi ba kuma suna da wuyar gane wa. Idan cutukan suka fara bayyana tare da wasu cutuka na daban, to daga nan za a iya cewa mutum ya ɗauki cuta daga yin jima'i.
Yawancin cutukan da ake ɗauka a ɓangaren jima'i na yaɗuwa, sai dai wasu lokutan ana ɗaukarsu ne ta hanyar jima'i na fata-da-fata.
Wasu cutukan kuma su kan yaɗu daga uwa zuwa ƴarta lokacin da take da juna biyu, haihuwa, ko kuma shayarwa.
Wasu hanyoyi da cutukan ke yaɗuwa sun kunshi bayar da gudummawar jini, ko kuma amfani da allura ɗaya.
Cutukan da ake ɗauka wajen jima'i suna iy rikiɗe wa su janyo cutar kansa, da matsanancin ciwon kugu da kuma rashin haihuwa.
Waɗanne irin cutuka ne ake ɗauka wajen jima'i?
Akwai nau'in ƙwayoyin bacteria sama da 30, waɗanda za a iya yaɗa su ta hanyar jima'i.
Ɗaiɗaikun mutane za su iya ɗaukar cutukan jima'i fiye da ɗaya a lokaci guda.
Cutukan da suka yawaita waɗanda ake ɗauka wajen jima'i sun haɗa da ciwon sanyi na 'gonorrhoea' da kuma yankan gashi wato 'syphilis.
Ana iya warkewa daga dukkan waɗannan cutuka.
Yaya alamomin cutukan suke?
Cutukan da ake ɗauka wajen jima'i yawanci ba sa nuna alamomi a fili ko kuma alamomin ba sa yin tsanani.
Mutum zai iya ɗaukar cuta ba tare da ya sani ba.
Sai dai ko da babu wasu alamomi, ana ɗaukar cutukan ta wajen jima'i kuma za su iya masu haɗari.
Idan akwai alamomi, za su kunshi:
- Jin zafi a gaban namiji ko na mace
- Fitar kuraje a al'aura
- Jin zafi ko fitsari akai akai
- Kaikayi da fitar ja a fata
- Zafi ko tsotsewa a ciki da wajen baki
- Fitar wari a al'aurar mata
- Kaikayin gaba da fitar jini
- Ciwon ciki
Me ya sa cutukan jima'i suka yawaita?
A shekarar 2020, Hukumar Lafiya ta Duniya ta kiyasta cewa akwai mutum miliyan 374 da suka kamu da akalla ɗaya daga cikin cutukan da ake ɗauka wajen jima'i: irin ciwon sanyi na 'gonorrhoea' da yankan gashi wato 'syphilis da kuma chlamydia.
An kiyata cewa sama da mutum miliyan 490 ne ke rayuwa da matsala a al'aura wanda ake ɗauka wajen jima'i a 2016, an kuma kiyasta cewa mutum miliyan 300 na ɗauke da wani nau'in cuta na jima'i, abin da ke janyo cutar sankarar bakin mahaifa a tsakanin mata da kuma sankarar dubura tsakanin maza da suka yi jima'i da ƴan uwansu maza, a cewar alkaluman WHO.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
“Jima'i abu ne da mutane ke buƙata. Yana kamar ci da sha, ya kasance ɗaya daga cikin ɓangaren rayuwar ɗan'adam," a cewar Dakta Teodora Elvira C. Wi, jagorar shirin yaki da cutukan da ake ɗauka wajen jima'i, HIV, da kuma ciwon hanta na WHO.
"Kana jima, idan ka yi jima'i za ka iya ɗaukar cuta. Shiyasa alkaluman masu cutar ke ƙaruwa."
Dakta Wi ta kuma ce duba da ganin ba a iya gane alamomi a wajen wanda ya ɗauki cuta a wajen jima'i, hakan ya sa mutane za su rika yaɗa su ba tare da sun sani ba.
Barazanar kamuwa da cutukan jima'i na ƙaruwa saboda sauyawar al'adar jima'i ta sha'awa kawai, mutane na samun damar yin jima'i a saukake kuma suna yin jima'i da mace fiye da ɗaya a lokaci guda, sannan da ƙaruwar amfani da manhajojin soyayya na zamani, a cewar Dr Wi.
Duk da cewa bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa alkaluman matasa masu yin jima'i ba tare da aure ba na raguwa, akwai kuma raguwar amfani da kororon roba.
Dakta Wi ta nanata cewa lokacin da babu maganin HIV da aka samar, mutane na taka tsantsan wajen yin jima'i ta sha'awa kawai, musamman ba tare da amfani da condom ba.
Ta ƙara da cewa mutane da dama daga sassan duniya sun yi imanin cewa za su iya gwajin cutar HIV, su karɓi magani don samun waraka. "Don haka, amfani da condom ya yi ƙasa matuka," in ji ta.
A 2022, mutum miliyan 1.3 suka kamu da HIV, a cewar alkaluman WHO.
Sama da mutum 600,000 ke mutuwa duk shekara daga cutar saboda ba su san cewa suna ɗauke da cutar ta HIV ba kuma ba sa shan magani, ko kuma sun fara shan magani a kurarren lokaci, a cewar hukumar.
Ta ya za ka kare kanka daga cutukan jima'i?
“Ka yi amfani da kororon roba. Shi za kare ka daga kamuwa da cutukan da ake ɗauka wajen jima'i," in ji Dr Wi.
"Idan za ka yi jima'i da wanda ba ka sani ba ko kuma yin jima'i ta sha'awa, ya kamata ka kula. Zai fi kyau ka koyi yadda ake amfani da condom da kuma jin daɗinsa."
Amfani da condom nau'in latex yadda ya kamata yana rage barazanar kamuwa da cuta ainun, amma ba ya rage barazanar kamuwa ko kuma yaɗa cutukan jima'i kwata-kwata a cewar kwararru a fannin lafiya.
Idan aka ga alamomin cutukan da ake ɗauka wajen jima'i, yana da muhimmanci a tafi zuwa wajen jami'in lafiya nan take domin yin gwaji da kuma samun magani.
"Kada mutum ya je kemis inda zai karɓi magani ba tare da gwaji ba saboda hakan ba zai taimaka ba. Idan ba ka samu magani yadda ya dace ba, hakan zai janyo abubuwa mara kyau, kamar rashin haihuwa," in ji Dr Wi.
"Yin watsi da cutuka wajen jima'i na yi wa jiki lahani: Zai janyo matsanancin ciwon kugu da haihuwar bakwaini, da kuma mutum kusan miliyan biyu da ba za su iya haihuwa ba a kowace shekara, musamman daga cutukan sanyi na gonoriya ko chlamydia a tsakanin mata wanda kuma ba a yi wa magani ba," in ji ta.

Asalin hoton, Getty Images
Ta yaya ake magance cutukan da ake ɗauka wajen jima'i ?
Akwai magunguna da za a iya amfani da su wajen warkar da cutukan da ake ɗauka wajen jima'i waɗanda kwayoyin bacteria ke haifarwa, sai dai wasu cutukan ba sa warkewa musamman kansar bakin mahaifa.
Magunguna suna taimakawa wajen rage alamomi da kuma barazanar yaduwar cutukan.
Akwai alluran riga-kafi da ke taimakawa wajen kaucewa kamuwa da cutar kansar bakin mahaifa da kuma ciwon hanta.
Dakta Wi ta ce WHO na duba yiwuwar ƙirƙiro da riga-kafin gonoriya da kuma ta kansar al'aura.
Likitar ta kuma ce an fara aiki don samar da riga-kafin cutar sanyi na chlamydia da kuma yin bincike don samar da riga-kafin ɗaya cutar sanyin wato syphilis.
Me ya kamata gwamnati ta yi don rage cutukan jima'i?
A yawancin wurare a duniya, akwai ƙarancin kuɗaɗe da ake warewa shirye-shiryen gwamnati na dakile cutukan da ake ɗauka wajen jima'i.
"Saboda tsangwamar da ake yi wa masu cutukan jima'i, ba a ba da fifiko yadda ya kamata wajen samar da kuɗaɗe a ɓangaren, ba zai kawo maka kuri'u a zaɓe ba," in ji Dr Wi.
Ta nanata cewa gwamnatoci su samar hanyoyi masu sauki na samun lafiya da samar da kuɗaɗe masu yawa domin kirkiro da cibiyoyin gwaji da kuma warkar da cutukan jima'i - kamar samar da wuraren gwaji da yawa da kuma alluran riga-kafi.
"Ana yawan watsi da cutukan da ake ɗauka wajen jima'i. Ya kamata mu rage tsangwamar da ake nunawa masu ɗauke da cutukan jima'i da kuma magance sa kamar kowane irin cuta," in ji ta.










