Kenya na son rage yadda ake shan barasa a kasar

.

Asalin hoton, Getty Images

Mataimakin shugaban ƙasar Kenya ya yi kokarin ɗaukar matakai da za su rage yadda mutane ke shan barasa a yanin tsakiyar ƙasar, inda ya ce gwamnatin ƙasar za ta rika barin mashaya ɗaya kaɗai a kowani gari, sai dai ba kowa ne ya amince da hakan a matsayin wani yunkuri mai kyau ba.

"Ko da sun rufe dukkan wuraren shan barasa, sai mun sha,'' in ji Charles Ngugi lokacin da yake kurɓar barasa a wani kofi.

"Wannan barasa ba ta da tsada, me ya sa za su takurawa rayuwata da kuma jin dadi da nake ciki?" ya faɗa tare ɗaga muryarsa har take son fin karfin wakar da ke tashi a lokacin.

Akwai mutane guda huɗu a cikin mashayar, dukkansu suna zaune rike da barasa a hannunsu.

Wani mutumi ne ya shigo cikin wurin sayar da barasar, inda yake ta tika rawa daga wakar da ke tashi a wurin da aka rera cikin yaren Kikuyu, kafin shi ma ya zo ya samu wurin zama tare da karɓar tasa barasa don sha.

Mintuna kaɗan bayan nan, kawai sai ya shiga yin barci.

Karfe 11 na safe. Doka ta yi tanadin cewa ba za a sake buɗe wannan mashaya ba har sai bayan sa'o'i shida. A kuma rufe da karfe 11 na dare.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana iya ganin illar da shan barasa ke yi wa mutane a kan tituna

Wasu wuraren sayar da barasa guda uku a ƙauyen Kanderendu da ke lardin Muranga mai kilomita 70 da Nairobi babban birnin ƙasar su ma suna buɗe, inda suke cike da mutane masu shan ta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Irin waɗannan wurare ne mataimakin shugaban ƙasar Rigathi Gachagua ke son ragewa. A watan Janairu, ya ce za a rage gidajen shan barasa da kuma gidajen sayar da abinci zuwa ɗaya a kowane gari.

Sai dai masu shan barasar ba su amince cewa wannan matakin zai sa su rage shan ta.

"Idan aka rufe wuraren sayar da barasa irin wannan, mutane da dama kamar ni, za su koma zuwa bakin kogi don shan ta gargajiya,'' in ji mista Ngugi.

Masu sayar da barasa ta gargajiya ta haramtacciyar hanya na amfani da bakin kogi wajen sayar da ita. Akwai sauki wajen samun barasar a yawancin wurare, inda wuraren ke bai wa hukumomi wahalar kai wa.

Tsakiyar kasar Kenya na fama da yawan masu shan barasa a abin da gwamnatin ƙasar ta yi gargaɗi a kai.

Sai dai hukumomi ba su gabatar da alkaluma domin tabbatar da haka, amma sun ce akwai matsala, inda suka ɗora laifin shan barasa a kan rashin tantance gidajen sayar da barasar da kuma shigo da wadda ba ta da tsada.

Ba a dai san me ya sa aka ambaci tsakiyar Kenya shi kaɗai ba - amma a wata ziyara zuwa yankin, ya nuna cewa ana samun ƙaruwar masu shan barasa. Hukumomi a lardin na Muranga sun ce yawan gidajen sayar da barasa ya ƙaru sosai tun bayan kullen korona.

'Lalata zuri'a'

Lasisin mallakar gidajen sayar da barasa ya zamo abin da aka fi nemansa a lardin, kamar yadda mutanen wurin suka faɗa wa BBC.

Lardunan su ke da alhakin bayar da lasisin, amma ganin mataimakin shugaban ƙasar ya fito ne daga yankin, hakan ya sa yana da tasiri a can.

"Ya kamata gwamnonin larduna su ɗauki mataki, don a kokarin samun kuɗaɗen shiga da samar da lasisi ga shaguna, haka na nufin kowane wuri da ya zama wajen sayar da barasa, hanya ce ta lalata ɗaukacin zuri'a kuma hakan ba daidai bane,'' in ji mista Ngugi.

Rosemary Kimani, mai shekara 58, ta bayyana tasirin shan barasa a kanta.

Ta ce ta rasa mijinta sakamakon shan barasa da yake yi. 'Ya'yanta guda uku, ciki har da 'yarta sun dogara ne da ita.

"Kogin da kuma wuraren sayar da barasa za su iya zama ajalinmu gaba ɗaya,'' in ji Rosemary da ke zaune a ƙauyen Kiunyu. Ta koma da zama a wurin a farkon shekarun 1990 bayan aure da ta yi.

"Ba mu iya ɗiba ko da ruwan sha a wurin saboda gungun mutane masu sayar da barasa ta haramtacciyar hanya sune ke da iko da wuraren.

"Ba za ka iya ganin samari da ƴan matansu ba a nan Kiunyu, ko kuma da iyalansu. Abin da suke yi kawai shi ne zuwa wuraren sayar da barasa,'' in ji ta.

"Ta ya ya za mu samu jikoki idan mutanen mu suka ƙauracewa matansu, da rashin nuna bukatar saduwa, sai kawai shan barasa da kuma yin barci tsawon rana??" kamar yadda Rosemary ta tambaya.

Ms Kimani ta goyi bayan matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na rufe gidajen sayar da barasa.

Gwamnatin na kuma son dukkan wuraren sayar da barasa su rage lokutan yin aiki, inda za su rika sayar da ita daga karfe 5 na yamma zuwa tsakar dare.

Akwai wasu hujjoji da suka nuna cewa sannu a hankali masu gidajen sayar da barasa sun daina sabunta lasisinsu, amma duk da haka babu wanda aka rufe.

Masu gidajen sayar da barasa da kuma na abinci sun ce matakan da gwamnati basu kamata ba saboda an ta'allaka su ne kan masu sana'o'i da ke samun abin dogaro.

"Matsalar ba ta sayar da barasa bane, saboda muna samar da wuraren da mutane za su haɗu su yi mu'amala daban-daban, muna biyan haraji da ake amfani da shi wajen raya ƙasa, mun kuma samar wa dubun-dubatar mutane aikin yi,'' in ji Simon Mwangi Njoroge, shugaban kungiyar masu gidajen sayar da barasa.

"A yankin tsakiyar ƙasar kaɗai, muna da wuraren kasuwanci sama da 17,000 tare da samar wa mutum 100,000 aikin yi."

Kungiyoyi masu zaman kansu da kuma shugabannin coci, sun shigo cikin lamarin ta hanyar kirkiro da cibiyoyin sauya tunanin mutane, sai dai cibiyoyin na da tsada da kuma suka fi karfin masu shan barasa da dama.

"Muna son magance matsalar shan barasa da irin illar da take da shi kan rayuwar mutane, amma ya kamata mu yi taka-tsan-tsan wajen ɗaukar matakin. Shin matsalar mu ta tsaya ne kan sana'o'in da aka kafa ba bisa ka'ida ba?" in ji Steven Kimani, ɗan siyasar da alhakin kare lafiya ya rataya a wuyansu a lardin Muranga.

"A halin yanzu, ba mu da cibiyar sake sauya tunani da gwamnati ta ɗauki nauyinsa, saboda wannan ba shi ne abin da muka saka a gaba ba. Abin da muka mayar da hankali a kai shi ne rage wuraren shan barasa na aka kafa ba bisa ka'ida ba da ya addabi lardin mu da kuma sauran yankin tsakiyar Kenya.

"Amma an fi tattaunawa kan batun rufe gidajen sayar da barasa. Wane abu za a yi amfani da shi wajen rufe wuraren kasuwancin? Waɗanne alkaluma za a yi amfani da su wajen nuna cewa mu abin ya fi shafa? Babu ko ɗaya,'' in ji Mwangi yayin tattaunawa da BBC.

Hukumar kula da kamfe kan tu'ammali da shan barasa na tattara alkaluma a yanzu, sai dai ta nuna damuwa kan ƙaruwar gidajen sayar da barasa da kuma shan ta a yakin tsakiyar ƙasar.

Masana sun yi gargaɗin cewa za a iya rasa ɗaukacin zuri'a idan ba a yi wani abu don magance matsalar ba.

Ga waɗanda matsalar ta shan barasa ta riga ta shafa, sauyi ba zai zo nan take ba.

"Bala'i ne na ƙasa baki ɗaya,'' in ji Rosemary Kimani.