Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sa'insar Atiku da Tinubu, rufe kasuwannin canji a Abuja da Kano
Da ba a cire tallafin mai ba da wahalar Najeriya ta fi ta yanzu - Gwamnatin tarayya
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a na Najeriya, Alhaji Mohammed Idris Malagi ya ce, da gwamnati ba ta cire tallafin mai ba da wahalar da ake ciki a ƙasar ta fi haka a yanzu.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake kare matakin gwamnatin ƙasar na cire tallafin mai a yayin wata hira da tashar talabijin ta Channels.
A lokacin jawabinsa na farko bayan rantsuwa, a Abuja, a watan Mayu na 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu sauran tallafin mai.
Tun daga lokacin da shugaban ya sanar da janye tallafin man kayayyaki da sauran harkokin rayuwa a Najeriya suke ta tashin gwauron zabo, rayuwa take ta kara tsada ga jama'a.
'Kashi 81 cikin ɗari na ma'aikatan Najeriya ba su da amfani'
Kusan kashi 81 cikin ɗari na ma'aikatan Najeriya ba sa wani ɓangare da ke samar da cigaba ga tattalin arziƙin ƙasar, in ji shugaban kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa na manufofi da tsare-tsaren kuɗi da sauye-sauye a haraji, Taiwo Oyedele.
Oyedele ya ce duk da cewa yawan marassa aiki a Najeriya kaɗan ne inda yake kashi 4.2 cikin ɗari, yawancin 'yan ƙasar masu aiki ba su da wani amfani na ƙwarai ga tattalin arziƙin ƙasar.
Mista Oyedele ya ce Najeriya na mataki ɗaya ne da Birtaniya wajen yawan kashin marassa aikin yi wato 4.2 cikin ɗari, kuma abin da ya sa kenan har yanzu Najeriya ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fi talauci a duniya.
Ya ce akwai mutum sama da miliyan 113 da ke cikin fatara a Najeriya a shekara ta 2022, kuma yana ganin shakka babu yawan a yanzu ya fi haka domin a lokacin ba a janye tallafin mai ba da kuma daidaita farashin canjin dala.
Shugaban kwamitin na magana ne a wajen taron ƙoli na kasuwanci da zuba jari na Afirka a yau Alhamis, a Lagos.
Ƴan Arewa ba sa goyon bayan dattawan Katsina a kan Tinubu da zaɓen 2027 - Matawalle
Ƴan kasuwar Kantin kwari sun yi addu'a kan matsin rayuwa a Najeriya
Wasu ƴan kasuwa da ke hada-hada a kasuwar Kantin kwari da ke birnin Kano sun gudanar da addu'o'in neman samun sauƙi kan matsin tattalin arziƙi da ake ciki a Najeriya.
Ƴan kasuwar sun fito daga kantunansu inda suka gudanar da sallah da addu'o'i tare da neman ɗauki daga ubangiji.
Ɗaya daga cikin ƴan kasuwar mai suna Hamisu Sani ya shaida wa BBC cewa al'amura sun rincaɓe inda yanzu haka abinci ke gagarar al'umma.
Ya ce "mun gudanar da addu'o'i domin samun ɗauki daga ubangiji kan wannan hali, domin ba mu san abin da shugabanni ke yi kan wannan hali ba."
Ya ƙara da cewa "Buhun shinkafa da na sukari a yanzu haka sun gagari talaka."
Dakatar da hada-hadar musayar kuɗi a Najeriya
Kungiyar yan canji a Abuja, babban birnin Najeriya ta dakatar da hada-hadar musayar kudi har sai baba ta gani sakamakon karancin dala.
Yan Najeriya dai sun dogara kacokan kan kudin Amurka - dala domin tafiyar da harkokin da suka shafi kudi.
Abdullahi Dauran, shugaban yan canji a Abuja, ya shaida wa BBC cewa sun dauki matakin ne domin nuna wa yan Najeriya cewa sun damu da yadda ake samun karancin dala matsalar da ya dora kan ayyukan kamfanin da ke hada-hadar kuɗaɗe ta Intanet irin na Crypto.
Lamarin na zuwa ne daidai lokacin da Babban bankin Najeriya ke kokari na daidaita kasuwar musayar kudaden waje.
A gefe guda kuma, Kungiyar yan canji a jihar Kano ta ce daga yanzu za ta rika bude kasuwar hada-hadar canji daga karfe 12 na rana zuwa 6 na yammacin kowace rana.
Yan canjin da ke kasuwar wapa sun dauki matakin rage lokutan da kasuwar ke ci a wani bangare na nuna fushi da yadda farashin dala ke ci gaba da hauhawa.
Kungiyar ta ce za ta ci gaba da yin haka ne har sai farashin dala ya sauka.
A baya kungiyar tana bude kasuwar ne da karfe 8 na safe zuwa 9 na dare.
EFCC na bincike kan yarjejeniyar Nigeria Air - Keyamo
Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Festur Keyamo ya ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC na gudanar da bincike kan yarjejeniyar kamfanin jiragen sama na ƙasar wato 'Nagerian Air' mai cike da ce-ce-ku-ce da gwamnatin tarayya ta ƙulla ƙarƙashin tsohon ministan kula da sufurin jiragen sama na ƙasar Hadi Sirika
Yayin da yake zantawa da gidan talbijin na Channels ranar Laraba, mista Keyamo ya ce “EFCC na bincike kan yarjejeniyar.
''Ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma muna jiran rahoton binciken''.
Mista Keyamo wanda ya yi aiki tare da Sirika a matsayin ministocin gwamnatin Buhari, ya ce babu wani kamfanin jirage da ke aiki a matsayin kamfanin jirage na ƙasa, amma ya ce za a samar da nagartaccen kamfanin jirage na ƙasa.
Kaddamar da rundunar jami'an tsaron sa-kai a Zamfara
Gwamnatin jihar Zamfara ta kaddamar da wata rundunar `yan sa-kai don yaki da `yan bindiga da saura miyagun laifuka a jihar, wadda aka yi wa lakabi da `Askarawan Zamfara`.
Jihar Zamfara dai na cikin jihohin da matsalar `yan bindiga masu satar mutane don karbar kudin fansa ta yi kamari a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.
Rundunar mai suna Askarawan Zamfara ta kunshi zarata 2,646, wadanda aka harhada daga kananan hukumomin jihar 14, wadanda suka samu horo na musamman daga jami`na tsaro da kwararru daban-daban a fannin tsaro don tunkarar matsalar `yan bindiga masu satar mutane da dabbobi a jihar Zamfara.
Rikici tsakanin Atiku da Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya mayar wa babban mai hamayya da shi na Jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da martani bayan sukar gwamnatinsa.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa na babbar jami'iyyar hamayya ta PDP a zaben da ya gabata, ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya sauka daga shugabancin kasar idan ba zai iya shawo kan matsalolin tsaron da kasar ke fama da su ba.
Atiku Abubakar, wanda shugaba Tinubu ya kayar a zaben da ya gabata, ya zargi shugaban da yin wasa da aikinsa yayin da kasar ke nutsewa cikin matsalar tsaro da ta tabarbarewar tattalin arziki.
Sai dai fadar shugaban Najeriyar ta yi watsi da kalaman na Atiku tana mai cewa wata suka ce irin ta 'yan hamayya
Sojoji sun kuɓutar da mutum 35 tare da kashe ƴan bindiga biyu a Katsina
Rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) ta ce ta yi nasarar kashe ƴan bindiga biyu a jihar Katsina tare da kuɓutar da wasu mutum 35 da aka yi garkuwa da su a wani samame da sojojin suka yi a jihar a ranar 27 ga watan Janairu.
Kakakin Rundunar, Kyaftin Yahaya Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Ya bayyana cewa wasu 'ƴan ta’adda' da dama sun tsere da raunukan harbin bindiga.
Sanarwar ta kara da cewa "A yayin farmakin, sojojin sun yi arangama da masu ɗauke da makamai, inda suka kashe biyu daga cikinsu yayin da wasu suka tsere da mummunan raunin bindiga."