Kalmomi 7 da Kwankwaso ya furta suka zama sara

    • Marubuci, Usman MINJIBIR
    • Aiko rahoto daga, Abuja, Najeriya
  • Lokacin karatu: Minti 4

A yanzu haka za a iya cewa mabiya Kwankwasiyya da ma masu sha'awar siyasa na dakon sabbin kalamai ko kuma furuci daga tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso a daidai lokacin da ake gani a matsayin babban yaronsa a siyasa zai guje masa.

A kusan kowane yanayi na siyasa walau dai na kamfe ko zaɓe ko kuma tattaunawa da ƴan siyasa, Injiniya Rabi'u Kwankwaso kan hau duro ya rinƙa sakin kalamai da furuci da suka taƙaita ga shi shi kaɗai.

Masana harshe na alaƙanta kalaman na Kwankwaso da dabarun siyasa na kame zukatan masu sauraro shigen irin waɗanda ƴan siyasar farko-farko kamar Malam Aminu Kano da Abubakar Rimi suka rinƙa yi a duk lokacin da suka hau duro.

BBC ta yi nazari kan kalamai da furucin na Kwankwaso inda kuma ta tsamo guda bakwai.

A ci daɗi lafiya

Wannan shi ne kalami na baya-bayan da matasa da ƴan siyasa a jihar Kano ke ta amfani da ita tun bayan da bayanai suka fito cewa gwamna Abba Kabir Yusuf zai bar jam'iyyar NNPP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Kuma ana amfani da ita ne domin yi wa waɗanda za su bi gwamna Abba zuwa APC musamman waɗanda ake yi wa kallon za su bi gwamnan ne saboda mulki.

Wata majiya dai ta shaida wa BBC cewa Rabi'u Musa Kwankwaso ya furta magana ne a wani lokaci da yake yi wa waɗanda ake kira da "Kwankwasiyya Scholar" jawabi dangane da waɗansunsu da suka bar tafiyar.

Sai dai wata majiyar ta ce ba wannan ba ne karo na farko da Kwankwaso ya fara furta maganar, domin a cewar majiyar, a lokacin da aka fara samun saɓani tsakanin Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje ne ya fara cewa: "A ci daɗi lafiya."

Butulawa

A daidaitacciyar Hausa dai an san kalmar butulu da ke nufin mutumin da ka yi wa alkairi shi kuma ya saka maka da sharri to amma kalmar "butulawa" wadda bisa fahimta ke nufin masu yin butulci ta ksance baƙuwa a tsakanin masana harshen na Hausa.

An sha jin jagoran na Kwankwasiyya yana yawaita nanata wannan kalma kan waɗanda yake ganin ya yi wa dare a siyasance amma kuma suka yi masa rana.

Mutane masu daraja

Wannan ce kalmar da aka fi ji tsohon gwamnan na Kano na yawaita maimaitawa a jawabai da kalamansa walau a kan duro na siyasa ko kuma a hirarrakinsa da ƴan jarida.

Jumlar ta "mutane masu daraja" wadda ma'anarta a fayyace take na nuni da mutanen da shi Kwankwason ke yi wa kallon ƙima.

Sai dai kuma Kwankwaso lokaci zuwa lokaci kan juya jumlar zuwa

Ƴan Amana

Wannan kalma sananniya a tsakanin Hausa da ma masu magana da harshen Hausa, inda asalin kalmar ita ce "amana" wadda daga Larabci ta samo tushe kuma ke nufin riƙo da zumunci a Hausa.

To idan aka yi wa kalmar ɗafi ma'anar ka iya sauyawa zuwa mutum ko mutane masu riƙe wannan zumunci.

Kwankwaso na yawan furta kalmar ƴan'amana domin kambama waɗanda yake ganin suna tare da shi a siyasa ba su bar shi ko kuma a ta bakinsa ba su "tsallaka titi" ba.

Tsallaka titi

Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso mutum ne mai son barkwanci musamman a jawabai da hirarrakinsa da ƴan jarida kuma a cikin irin wannan halayyar tasa ne ya bai wa kalmar tsallaka titi ma'ana irin ta siyasa.

A zahiri idan aka ce mutum ya tsallaka titi to ana nufin ya ƙetara hanya. To amma shi Kwankwaso yana ba ta ma'anar siyasa da ke nuni da wadanda suka sauya sheƙa daga wurinsa zuwa abokan hamayyarsa.

Mahaha

Kawo yanzu dai za a iya cewa babu wanda ya san ma'anar wannan kurmar kalmar da Injiniya Rabi'u Musa ya furta a shekaru fiye da 10 da suka gabata.

Kwankwaso ya fara furta kalmar ne a 2011 lokacin da aka ba shi tutar takarar gwamna a karo na biyu bayan da farko an hana shi.

Kwankwaso ya shiga Kano a ranar Lahadi domin yin taron siyasa to amma ya haɗu da fushin gwamnatin jiha a lokacin inda aka hana shi filin wasa na Sani Abacha da na Sabon Gari.

To sai dai ya samu damar yin taron ne a filin ƙofar Na'isa inda a nan ne ya yi kalaman ciki har da Mahaha.

"...Maganin mayu...maganin Mahaha.."

Masu fashin baƙi na cewa Kwankwason yana son faɗin "mahassada" ne amma kuma sai ya lauye ko kuma kalmar ta ƙi fita.

Bayan Kwankwaso ya samu nasarar komawa kujerar gwamnan Kano sai ya raɗa wa filin na Ƙofar Na'isa sunan "Filin Mahaha" inda a nan ne a kowace shekara ake yin bikin shigar sabuwar shekara.

Wuju-wuju

Ita ma wannan kalma na ɗaya daga cikin kalmomin da Kwankwaso ya yi amfani da su a filin.

"..Kwankwaso ya lashe zaɓe...idan ba a ba shi ba yaro zai ji wuju-wuju ko kuma mu shafa masa goro ɗan ujule.," in ji Kwankwaso.

Wuju-wuju dai kalma ce da ka iya nufin jin babu daɗi ko kuma jin hajijiya. Amma ma'ana ta zahiri na nufin jefa mutum cikin wani yanayi na rashin jin daɗi.

Tun bayan furta wannan kalmar wadda matasa a lokacin ko dai ba su taɓa jin ta ko kuma su manta da ita, ta zamo sara a tsakanin matasan jihar Kano.

To amma sakamakon furta wasu sabbin kalmomin da jimloli da jagoran Kwankwasiyyar yake yawan yi ya sa wannan kalma na ɗaya daga cikin kalmomin da kusan a yau ba a cika jin amonsu ba.