Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ƴan jari-hujjan Abuja da suka bar talaka cikin wahala za su ga sakayya'
Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, kuma jagoran jam'iyyar NNPP, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi dirar mikiya a kan mutanen da ya kira 'yan jari-hujjan da suka gudu Abuja, babban birnin ƙasar, suka bar talakawa a cikin wahala.
A cewarsa, "Allah ba zai bar su ba".
Ya zargi 'yan siyasar ƙasar da mantawa da talakawa, inda ya ce suna can "sun samu manya-manyan gidaje sun zauna a ciki. "Waɗansu 'yan majalisa ne, waɗansu sanatoci ne, waɗansu ministoci ne".
"Babu abin da ya shafe su, sai ɗiban kuɗi suke, suna sayen gidaje," in ji tsohon gwamnan na jihar Kano.
Ya ce hakan na faruwa ne daidai lokacin da talakawa a wasu jihohin ƙasar ciki har da Sokoto da Zamfara da Katsina da Neja da Filato ke fama da matsalolin tsaro, inda 'yan fashin daji da sauran masu aikata laifi ke kai hari kan fararen hula musamman a yankunan karkara.
Kwankwaso wanda shi ma ana iya cewa yanzu haka, ya fi zama a Abuja, ya ce ba shakka Allah sai ya yi sakayya a kan halin da aka bar talaka ciki a Najeriya.
Yana jawabi ne yayin zantawa da manema labarai a Kano, a wani ɓangare na bikin cikarsa shekara 69 a duniya, inda aka tambaye shi a kan ko har yanzu ƙofarsu ta NNPP a buɗe take, za su yi haɗaka da wata jam'iyya a zaɓen 2027.
Kwankwaso ya ce a shirye suna jiran duk wata jam'iyya da ta tunkare su domin yin tafiya tare. "Har yanzu, ko APC ne, ko PDP ce, ko ADC ce, ko Jonathan ne, ko Peter Obi ne. In muka ga ka dace mu bi ka sai mu zo haɗu, ta yadda yake za mu kai ga nasara".
Sai dai ya ce ko da wacce jam'iyya za su haɗaka, "ko APCn ne, to mu muna da abin da muke so mu yi wa Najeriya. Idan muka za ka yi saɓanin haka, to gaskiya ba za mu yarda ba.
A cewar jagoran na Kwankwasiyya: "Talaka dai sai ya ji daɗi. Sai an sakam masa mara, ya huta. Matasanmu sai sun yi ilmi. Tsaron nan da ake ta fama da shi.... ana kashe mana mutane, mafi yawansu namu ne talakawa".
'Waɗanda suka yi mana tawaye sun zarge wuyansu'
Jigon adawar a Najeriya ya ce mutanen da suke barin jam'iyyarsa ta NNPP ko kuma tafiyar Kwankwasiyya, "sun sayi igiyar zarge wuyansu a zaɓukan gaba".
"A wannan zamanin da muke ciki idan wani yana tunanin zai tsallaka titi koma ba ma tare da shi ya zo Kano ya ce zai ciri wata kujera...to idan da wanda kansa ya ɗaure to wannan mutumin ne kuma tafiyarmu za ta ci gaba da hukunta su."
Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso wanda ya bayyana wa BBC hakan jim kaɗan bayan kammala tattaunawa da manema labarai a Kano, ya kuma yi ƙarin haske dangane da dalilin da ya sa mabiyansa ke raba gari da shi.
"Mu ba so muke mu ɓata da kowa ba. Duk wanda ka ga ya bar mu ko dai shi ya bari da kansa ko kuma ya wuce gona da iri. Ko kuma idan kana wulaƙanta mu ko kana zazzare idanu a talbijin da rediyo kana nuna kai wani ne mu ba komai ba ne. Bayan mun san tarihinka...to ka ga sai mu ɗauki mataki.
Dangane kuma da alƙarsa da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Kwankwaso ya ce babu wata matsala tsakaninsa da gwamnan Kanon da kuma sauran maƙarraban gwamnatin kamar yadda wasu 'yan siyasa ke ƙoƙarin kunna rikici.
Kwankwaso ya ce sun bai wa gwamna Abba Kabir dama ya yi aiki yadda ya kamata, kawai wasu 'yan gutsiri tsoma ne ke kokarin haddasa fitina.
"Abin da na sani mun duba mun ga wanda ya fi cancanta a lokacin da za a yi zaɓe tun 2019 kuma mun ga shi ne ya fi cancanta. Kuma mun ba shi dama ya yi abubuwan da ya dace.
"Da yawa mutanen sun yi munafirci iri-iri cewa ni nake kwangila. Ko ni nake tafiyar da gwamnati..babu buƙatar mutum ya yi magana...koma dai mene ne nan gaba komai zai fito...kawai dai abin da na sani shi ne tsarin idan ya tambayi shawara sai a abshi." In ji Kwankwaso.
Zaɓen 2027
Da aka tamabyi Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya kuma bayyana ra'ayinsa dangane da tunanin ko za a iya samun maguɗin zaɓe a shekarar 2027.
"Masu hayaniyyar ko za su kayar da mu zaɓe. Akwai masu tunanin ƙwata to amma matasa suna ganin su ai.
Ni na sani zaɓen da za a yi a 2027 ba irin na baya ba ne domin kowa mafiya yake nema saboda haka ba wanda zai zo ranar zaɓe ya ce za a ba shi kuɗi ya yi zaɓe, "in ji Kwankwaso.