Manyan sauye-sauyen da za a iya samu a siyasar Kano idan Kwankwaso ya koma APC

    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Saboda ɗaukar hankali da kuma tasirin siyasar jihar Kano a Najeriya, waɗanda ke bibiyar harkokin ke cewa siyasar Kano sai Kanon.

Maganganun da jagoran jam'iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ke yi a baya-bayan nan game da niyyarsa ta komawa APC mai mulkin Najeriya na ƙara tabbatar da hakan.

Ana yi wa Kwankwaso kallon daya daga cikin ‘yansiyasa masu tasiri a arewacin Najeriya saboda yadda yake da ɗumbin mabiya a Kano, jiha ɗaya tilo da NNPP ta ci a zaɓen 2023.

Yayin da 'yan hamayya ke ci gaba da shirin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, Kwankwaso ya ja daga tsakanin jam'iyyar haɗaka ta ADC da PDP a ɓangaren adawa, da kuma APC mai mulki kuma kowane ɓangare na kwaɗayin ya koma cikinsu a yanzu.

A makon da ya gabata Kwankwaso ya nuna cewa yana da sha'awar komawa APC ɗin, amma rashin samun abin da yake nema ne ya hana shi komawa.

"Ina son shiga APC, kuma har yanzu ban ce ba zan shiga jam'iyyar ba, amma a wane matsayi?" kamar yadda ya bayyana yayin da shugabannin jam'iyyar NNPP na Kano suka kai masa ziyara.

Tuni wasu rahotonni suka ce har ma ya fara tattaunawa da shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, domin ƙarƙare komawar tasa da jama'arsa. Sai dai ya musanta cewa ya miƙa buƙatar shiga jam'iyyar cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukan zumunta ranar Juma'a.

Idan har kwankwaso ya koma APC kafin zaɓen 2027, siyasar Kano za ta fuskanci gagarumin sauyi.

Mun duba wasu daga cikin sauye-sauyen da komawar tasa za ta iya haifarwa a siyasar jihar da ta fi kowacce yawan masu katin zaɓe.

Adawa tsakanin Kwankwaso da Ganduje

Abu na farko dai shi ne, Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje sun shafe aƙalla wa'adin mulki biyu na shekara takwas tare a kan mulki - a 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015, Kwankwaso yana gwamna ganduje yana mataimakinsa.

Tun bayan da Ganduje ya zama gwamna a 2015 ne kuma alaƙa ta sauya, inda abota ta koma adawa tsakanin shugabannin biyu a cikin jam'iyyar APC, kafin Kwankwaso ya koma PDP.

Tun daga lokacin Kwankwaso yake adawa da Ganduje a jam'iyyun adawa na PDP da NNPP. Abin tambaya a nan shi ne, yaya adawar za ta koma idan suka koma inuwar jam'iyya ɗaya?

"Yanzu sabuwar dambarwa ce za ta ɓarke tsakaninsa da Ganduje," kamar yadda Dr Saidu Ahmad Dukawa na Jami'ar Bayero ya shaida wa BBC.

"Za su zauna ne su gwada ƙwanji a cikin APC. Hanya ɗaya da Kwankwaso zai rayu a APC ita ce a cika masa sharuɗɗansa, kuma sharuɗɗansa su ne karɓe duk wasu muƙamai ta yadda sauran za su zama mabiya kawai."

Dr Dukawa ya ce yana ganin "su Ganduje ba za su yarda da wannan ba".

Sai dai Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa a kwalejin share fagen shiga jami'a da ke Kano, ya ce idan Shugaba Tinubu ya yi ƙoƙari zai iya bai wa kowannensu dalilin zama a inuwa ɗaya.

"Ya danganta da irin daidaiton da aka samu bayan ya shiga jam'iyyar. Idan fadar shugaban ƙasa ta samar da daidaiton da kowannensu zai gamsu za su ci gaba da zama tare ko da kuwa a ce ta ciki na ciki ne," a cewarsa.

"Idan ma suka fuskanci wani ƙalubale mai girma daga jam'iyyar adawa za su iya komwa ɗasawa da juna duk da abubuwan da suka faru a baya."

Makomar adawa a Kano

Jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya, ita ce mai mulki a jihar Kano bayan Abba Kabir Yusuf ya yi nasarar doke Nasiru Gawuna na APC a zaɓen 2023.

Kafin lokacin, PDP ce babbar jam'iyyar adawa a Kano, wadda tsohon gwamna Ibrahim Shekarau ke jagoranta. Amma ita ce ta zo ta uku a zaɓen na 2023, kuma tun kafin haka jam'iyyar ta daina tasiri a jihar.

Wani abu da zai fi jan hankalin 'yansiyar Kano yanzu shi ne jam'iyyar da za ta ɗauki gabarar yin adawa da APC.

"ADC ce za ta cike gurbin yanzu, amma ya danganta da wane ne jagoranta a matakin tarayya da kuma waɗanda suka shige ta a mataki na jiha," in ji Kabiru Sufi.

Game da jam'iyyar PDP kuma, masanin ya ce dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan a matsayin ɗantakararta na shugaban ƙasa zai iya taimaka mata dawowa kan ganiya.

"Saboda irin su Atiku Abukabar da sauransu sun fita daga jam'iyyar, ana ganin dawowar Jonathan za ta iya dawo mata da tagomashi a Kanon da ma arewacin Najeriya," kamar yadda ya bayyana.

Makomar jam'iyyar NNPP

Ana hasashen cewa da zarar tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya koma jam'iyyar APC to jam'iyyarsa ta NNPP mai alamar kayan daɗi za ta suma idan ma har ba ta mutu gabaɗaya ba.

Dama dai akwai kwantaccen rikici a jam'iyyar tsakanin ɓangaren Kwankwaso da waɗanda ke kiran kansu su ne ƴan asalin jam'iyyar, wani abu da ya kai har ga dakatar da shugaban Kwankwasiyyar.

Sai dai kuma rikicin ya janyo darewar jam'iyyar biyu, mai alamar kayan daɗi da mai alamar alƙalami, inda kuma Kwankwason ke jagorancin mai kayan daɗin.

Kasancewar a jihar Kano ne kawai jam'iyyar take da gwamna da ƴanmajalisa da sanatoci, ficewa daga cikinta da Kwankwaso da muƙarrabansa za su yi ka iya mayar da jam'iyyar kufai.