Vinicius ne gwarzon Champions League Bellingham matashin gasar

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa ta bayyana ɗan ƙwallon Real Madrid Vinicius Junior a matakin Gwarzon Champions League na 2023/24.
Haka kuma hukumar ta sanar da Jude Bellingham na Real Madrid da tawagar Ingila a matakin fitatcen matashin gasar na bana.
Ɗan kasar Brazil ya taka rawar gani a kakar nan da Real Madrid ta kai ga lashe Champions League na 15 jimilla da ake kira La Decimoquinta.
Real Madrid ta doke Borussia Dortmund 2-0 ranar Asabar a wasan karshe a babbar gasar ta zakarun Turai.
Vinicius ya ci ƙwallo shida ya kuma bayar da 10 aka zura a raga a Champions League a kakar nan.
Shi ne ya ci Bayern Munich ƙwallo biyu a Allianze Arena a wasan farko a daf da karshe da suka tashi 2-2 ranar 30 ga watan Mayu.
Haka kuma shi ne ya zura na biyu a ragar Borussia Dortmund a Wembley ranar Asabar, hakan ya sa ƙungiyar ta Sifaniya ta ɗauki Champions League na 15 jimilla.
Shi kuwa Bellingham ya buga wa Real Madrid wasa 11 a Champions League da cin ƙwwallo hudu da bayar da bayar da hudu aka zura a raga.
Kafin fara kakar da aka kammala Bellingham ya koma Real Madrid daga Borussia Dortmund, wanda ya ci ƙwallo 19 da ta kai ƙungiyar Bernabeu ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla.











