Za a fara cin tarar masu amfani da waya lokacin tsallaka titi a Zambia

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Zambia sun amince da wata doka da ta haramta wa masu tsallaka titi amfani da wayar hannu ko kuma jin wakoki.
Wani sashi na dokar ya ce duk mutumin da aka samu da laifi zai biya tarar 1,000 na kuɗin ƙasar kwacha.
Ta kuma ce dole ne mai tsallake titi ya tsaya har sai fiitilun kan hanya sun koma launin ja da ke nufin ababen hawa su tsaya, kafin ya tsallake hanyar.
Mai magana da yawun hukumar kiyaye haɗura ta ƙasar, Frederick Mubanga, ya ce an yi dokar ne domin takaita yawan haɗura a kan hanyoyin ƙasar.
“Alkaluman bincike da muka samu, sun nuna cewa kashi 50 na waɗanda ke rasuwa a haɗuran kan hanya, sun kasance mutane ne da ke tsallake titi, inda a yawancin lokuta mutane ba su bin dokokin hanya yadda ya kamata,'' in ji Mubanga.
“Mun yi wannan dokar ne domin tsara yanda masu amfani da gefen titi za su bi, inda waɗanda kuma suka saɓa wa hakan za su fuskanci hukunci."
Ya ce a can baya, an fi mayar da hankali kan masu ababen hawa, amma a yanzu ba kansu kaɗai wayar da kai zai tsaya ba.
Mista Mubanga ya ce 'yan sanda za su kama waɗanda suka ki biyan tarar.
Ya ce an bai wa 'yan sandan ƙasar da kuma hukumar kiyaye haɗura ikon tabbatar da ganin an bi dokar.











