Mutum-mutumin da ke gano bututan ruwan da suka huje

.

Asalin hoton, Victoria Gill

Kusan litar ruwa biliyan uku ake asara a kullum a faɗin Ingila da Wales sakamakon fasassun bututan ruwa, kamar yadda hukumar da ke sa ido kan harkokin ruwa ta Ofwat ta bayyana.

Sai dai a halin yanzu an samu injiniyoyi da suka samar da wani ɗan ƙaramin mutum-mutumi mai kama da motar wasan yara da ake sakawa a cikin bututun ruwa wanda ke shawagi a ciki domin ya tabbatar da ko akwai wurin da bututu ya huje.

Hukumar ta ce ba zai yiwu a kula da bututan ruwan ba tare da irin wannan fasahar ba.

Hukumar ruwa ta Birtaniya ta shaida wa BBC cewa tuni kamfanoni suka soma zuba biliyoyin kuɗi domin magance zurarewar ruwa.

Amma wani rahoto na baya-bayan nan da Ofwat ya fitar ya ce akwai ƙarancin zuba jari daga ɓangaren kamfanonin ruwa.

Hukumar ta Ofwat ta lissafo kamfanoni da dama da ta ce ba su kyauta wa kwastamominsu da kuma muhallansu sakamakon ba su kashe kuɗi yadda ya kamata domin a samu ci gaba.

Amma kamfanin Water UK ya mayar da martani ta hanyar cewa hujewar bututai ta ragu matuƙa tun bayan da aka mayar da ruwa wurin kamfanoni masu zaman kansu.

Hujewar bututu dai matsala ce mai girma da kuma sarƙaƙiya.

A faɗin Birtaniya, akwai bututai da aka shimfiɗa masu tsawon dubu ɗaruruwan kilomitoci waɗanda suka shafe shekaru daban-daban da ke ba miliyoyin wurare ruwa.

Colin Day daga kamfanin Essex and Suffolk Water ya bayyana cewa:

"A wannan yankin kawai, muna kula da kusan sama bututai masu tsawon kilomita 8,500 kuma kusan rabi daga cikin irin hujewar da suka yi ne kawai ake iya gani wanda hakan ke nufin wani abu ne mai sarƙaƙiya."

Mutum-mutumin da ke shawagi a bututai

Tuni wasu kamfanoni suka soma amfani da mutum-mutumi da za suke sa ido kan bututai waɗanda ba a iya zuwa inda suke.

Sai dai akasarin bututan ba a iya ganinsu sai an tona rami. Sakamakon haka ne ake buƙatar ƙirƙirarriyar basira.

Ana gwajin wasu sabbin mutum-mutumi a wata cibiyar bincike da ke Jami'ar Sheffield.

Na'urorin ko mutum-mutumin mai suna "Pipebots" ƴan ƙanana ne kamar motocin wasan yara da ke ɗauke da kyamara da ƙafafuwa.

Ana yin su ne da tallafin kamfanonin ruwa domin sa ido da kuma shawagi domin gano idan akwai wani wuri da ya huje ko kuma ya tsage a cikin bututan.

Farfesa Kirill Horoshenkov ya bayyana cewa akwai buƙatar a ƙara samun irin waɗannan mutum-mutuman domin tattaro bayanai game da matsalolin da ake da su.

,.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ɓarnar ruwa ya kasance wani muhimmin lamari a bana.

Kamar yadda kamfanin Water UK ya bayyana, kamfanoni uku da suka haɗa da South East Water da South West Water da Yorkshire Water duk sun haramta amfani da tiyo na ban ruwa tun bayan rashin ruwan da aka yi fama da shi a lokacin hunturu.

Kuma duk da ƙaruwar tsadar rayuwa, Ofwat ta yi ƙiyasin cewa kashi 20 cikin 100 na kwastamomi a Ingila da Wales suna shan wahala kafin su biya kuɗin ruwa.

A bara kamar yadda Ofwat ɗin ta bayyana, kamfanoni sun rage zurarewar ruwa sakamakon hujewar bututu da kashi 6 cikin 100.

Kamfanonin samar da ruwan sun lashi takobin cimma manufar gwamnati ta rage kaso 50 cikin 100 na hujewar bututan ruwan da ake samu zuwa shekarar 2050.

Kamfanin Water UK ya amince da cewa akwai buƙatar samun ci gaba.

"Muna samar da sabbin dabarun kimiyya kamar samar da kemarori waɗanda za a saka a cikin bututai da kuma na'urar hoto daga tauraron ɗan adam," kamar yadda kamfanin ya shaida wa BBC.