Wace ce Claudia Sheinbaum, mace ta farko shugabar ƙasa a Mexico?

Claudia Sheinbaum ta shahara a bangon jaridar The Stanfod Daily lokacin zanga-zangar ɗalibai a 1991

Asalin hoton, Personal archive

Bayanan hoto, Claudia Sheinbaum ta shahara a bangon jaridar The Stanfod Daily lokacin zanga-zangar ɗalibai a 1991
    • Marubuci, Daniel Pardo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Mundo, Mexico City

A watan Janairun 1987, ɗalibai ne ke zanga-zangar tir da yunƙurin tilasta musu biyan kuɗin karatu a jami'ar UNAM - jami'ar gwamnati mafi girma a ƙasar Mexico.

Nan take masu zanga-zangar suka fara neman: "Wane ne zai maƙala tutar yajin aiki a kan ofishin shugaban sashen ɗalibai?"

Sai wata ɗalibar Physics ta matso gaba ta ce: "Ni!."

Fiye da shekara 40 bayan haka, ɗalibar - Claudia Sheinbaum Pardo - an zaɓe ta a matsayin sabuwar shugabar Mexico a ƙarƙashin jam'iyyar masu neman sauyi ta Morena.

'Yan Mexico na kiran ta "Claudia". Mahaifiyar yara biyun mai shekara 61 na da digirin digirgir a fannin muhallai, kuma tsohowar magajiyar garin Mexico City ce - wanda ke da mazauna sama da miliyan biyar.

Ya zuwa 1 ga watan Oktoba, za a rantsar da ita a matsayin mace ta farko shugabar ƙasar.

"Ni kodayaushe haka nake, mai son sanin ƙwaƙwaf," in ji Sheinbaum game da zanga-zangar ɗaliban nan. "Amma dai ba kamar da ba. Yanzu ina da abubuwa sosai a kaina."

Sheinbaum za ta jagoranci ƙasa mai mutum miliyan 130, mai yawan talaucin da ya kai kashi 36 cikin 100, mai iyaka da Amurka, da kuma yawan kashe mata da tayar da fitina.

Claudia Sheinbaum kenan yayin yawon yaƙin neman zaɓe a Taxcoco

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Claudia Sheinbaum kenan yayin yawon yaƙin neman zaɓe a Taxcoco

Duk da irin wannan abubuwan da ke kan ta a yazu, abokiyar Sheinbaum Diana Alarcón ta ce za ta ci gaba da abin da ta saba.

"Ba wai ta daina nuna tirjiya ba ne. Kawai rawar da take takawa ce ta sauya, amma aniyarta ta kare haƙƙin al'umma da ta fara tana yarinya yana nan."

Cikin shekara shida da suka wuce, Andrés Manuel López Obrador ne ya jagoranci ƙasar a ƙarƙashin jam'iyyar.

Kundin mulkin ƙasar ya tanadi zangon mulki sau ɗaya na shekara shida ga shugaban ƙasa, abin da ke nufin Mista Obrador ba zai iya sake neman takara ba. Akwai ƴan takara aƙalla shida da suka nemi su gaje shi, amma ɗaya ce mace a cikinsu: ita ce Sheinbaum.

Ta kasance ta gaba-gaba a manufar Obrador ta sauya Mexico. Amma tana da wani abu daban da za ta iya kawowa: mai riƙe da lambar yabo ce a fannin kimiyya wadda ta yi bincike kan cigaban al'umma.

Siyasa a yarinta

Claudia Sheinbaum kenan lokacin da take yarinya

Asalin hoton, Personal archive

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An haifi Sheinbaum ranar 24 ga watan Yuni na 1962 a birnin Mexico City. Iyayenta 'yan gwagwarmyar kawo sauyi ne a fannin ayyukansu.

Mahaifinta Carlos Sheinbaum ɗan kasuwa ne kuma mai sayar da magunguna, wanda iyayensa Yahudawan Ashkenazi ne da suka je Mexico daga Lithuania a shekarun 1920. Mahaifiyarta Annie Pardo masaniyar lafiyar tsirrai ce kuma likita, wadda iyayenta Yahudawan Sephardic ne, waɗanda suka je ƙasar daga Bulgaria a shekarun 1940.

Sheinbaum ta girma a unguwar masu kuɗi da ke kudancin babban birnin ƙasar, inda ake yawan tattauna harkokin siyasa a kodayaushe. Iyayenta kan kai ta don ganin abokansu 'yan gwagwarmaya.

Sheinbaum ta je makarantar da babu ruwanta da addini da ke rainon ɗalibai su zama abin da suke so a rayuwa, wanda abu ne da ba a saba gani ba a ƙasar da ke bin ɗariƙar Katolika ta Kiristanci.

Abokin Sheinbaum tun shekarun 1970, Alarcón ya ce: "Tana da kunya. Shi ya sa wasu ke mata gani-gani, amma idan kuka zauna da ita za ku gane tana da daɗin mu'amala."

Claudia Sheinbaum da mijinta Jesús María Tarriba yayin yaƙin neman zaɓe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Claudia Sheinbaum da mijinta Jesús María Tarriba yayin yaƙin neman zaɓe

Sheinbaum kan ce "ni 'ya ce da aka haifa a shekarun 1968," tana nufin irin gwagwarmayar da iyayenta suka yi a lokacin.

Ta daɗe tana marmarin siyasa. Mijinta na farko shi ne Carlos Ímaz, ɗan siyasa mai sassauƙan ra'ayi. Sun rabu kafin ta auri Jesús María Tarriba a 2023.

Ta shafe mafi yawan shekarunta a fannin koyarwa. Baya ga kammala digiri na uku, ta kuma wallafa bincike da dama kan maudu'ai musamman a ɓangaren muhalli.

Sheinbaum ta shiga siyasa

Claudia Sheinbaum take tuƙa keke

Asalin hoton, Personal archive

A shekarar 2000, abubuwan siyasa biyu sun faru da suka taimaka wa Sheinbaum zama shugabar ƙasa.

Jam'iyyar Institutional Revolutionary Party (PRI) ta faɗi a zaɓen shugaban ƙasa a karon farko cikin sama da shekara 70. Sai kuma a Mexico City inda wani mai neman kawo sauyi daga Tabasco ya ci zaɓen magajin gari. Magajin garin shi ne Andrés Manuel López Obrador.

A wannan lokacin ne Mista Obrador da Sheinbaum suka haɗu bayan wani farfesan lissafi ya ba da shawarar a naɗa ta sakatariyar muhalli a gwamnatinsa.

Ya naɗa ta muƙamin kuma ya ba ta aiki biyu: ta tsaftace ɗaya daga cikin biranen duniya mafiya gurɓacewa da kuma gina layi na biyu na titin Periférico, wanda ya fi kowanne girma a birnin. Ta yi nasarar yin duka biyun.

Tana cikin tawagar da suka ci nasarar lashe kyautar Nobel ta Zaman Lafiya kan wani binciken sauyin yanayi da suka yi.

Ta ci gaba da bin harkokin siyasa har ma ta zama mai magana da yawun tawagar kamfe ɗin mista Obrador a 2006 da 2012.

Sai kuma a 2015 ta tsinduma siyasa da kanta. Ta tsaya takara kuma ta ci zaɓen magajiyar gari a Tlalpan, garin da ta girma.

Shekara uku bayan Obrador ya zama shugaban ƙasa, Sheinbaum ta zama magajiyar garin Mexico City, inda ta zama cikin masu neman gadar sa cikin sauri.

Claudia Sheinbaum da tsohon shugaban ƙasa Andrés Manuel López Obrador, wanda ake yi wa labi da Amlo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Claudia Sheinbaum da tsohon shugaban ƙasa Andrés Manuel López Obrador, wanda ake yi wa laƙabi da Amlo

Zama shugabar ƙasa

.

Asalin hoton, Getty Images

Duk da abubuwan da suka faru, sama da kashi 60 cikin 100 na mazauna Mexico City ne suka amince da takararta. An ɗan samu raguwar tashe-tashen hankali, an ƙara yawan titunan keke, sannan aka gina layin motar da ke tafiya a kan waya mafi tsawo a dunya - kilomita 4.8.

Amma yadda ta yi yaƙi da annobar korona a Mexico City ya zamar mata abin alfahari a siyasance. A nan ne kuma ta nuna cewa salon shugabancinta da na Obrador ya bambanta.

Yayin da Sheinbaum ta saka dokar kulle a Mexico City, Obrador ya yi watsi da haɗarin cutar. Yayin da take saka takunkumi, bai saka ba, kuma ya ƙi cewa komai a daidai lokacin da take ƙarfafa yin rigakafi.

Amma hakan bai hana shi ya goyi bayanta ba.

"Mista Obrador na girmama ta kodayaushe," in ji Jorge Zepeda Patterson, wani ɗan jarida kuma mai sharhi kan siyasa. "Ya fahimci cewa mutum ce da ke ɗaukar aikinta da muhimmanci, wadda ba lallai ta zama 'yar siyasa ba amma kuma ta ƙware a fannin shugabanci."

An yi ta yaɗa jita-jita kan shugabancinta - ko Obrador ne zai mamaye mulki, ko za ta iya tsawatar wa gwamnoni da sojoji, ko kuma za ta iya ci gaba da mu'amalantar Amurka ba da tsoro ba kamar yadda yake yi.

"Abin da zan tabbatar muku shi ne ba za ta sauya ba," a cewar Alarcon, daɗaɗɗen abokinta. "A shekarun 1980, ita ce ta ɗora tutar yajin aiki a kan ofishin shugaban jami'ar UNAM, kuma ita ce yanzu za ta gina jami'o'i.

"Ba ni da wata tantama cewa za ta yi hakan, ta ƙi sauya hali, ta zauna a Claudia ɗinta."