'Raba mana gwangwanin shinkafa a matsayin tallafi raini ne'

- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
''Na yi matukar mamaki lokacin da na ci karo da mutane wasu dauke da kunshin shinkafa da ba ta fi gwangwani biyu ba, wasu kuma ɗan manja ne ɗaure a ledar da ke hannusu, wasu kuma 'yar taliya ce da aka raba fakitinta'',
Kalmomin Muhamud Tanimu ke nan mazaunin garin Keffi da ke jihar Nasarawa.
Muhamud da ke tattaunawa da BBC cikin yanayi na fusata ya nuna takaici da alla-wadai da rabon tallafi da gwamnatin Nasarawa ke yi amma cikin yanayi na raini kamar yadda yake cewa.
Tun bayan janye tallafin man fetur al'ummar Najeriya musaman masu ƙaramin ƙarfi suka shiga cikin wahalhalu na rayuwa sakamakon yadda aka samu hauhawar farashin da aka jima ƙasar bata gani ba.
Kusan farashin komai ya tashi a kasuwa, daga fannin kayan abinci zuwa abubuwan amfanin yau da kullum da sauran bukatun rayuwa.
Sai dai kuma gwamnati na cewa duk waɗannan matakai nata nan gaba za a ga alfannunsu.
Yawan korafe-korafe da neman sassauci da yekuwar da 'yan kasa suka rinka yi ga gwamnati, ya sa shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu alkawarta daukan matakan rage raɗaɗin matsin da ake ciki bayan janye tallafin mai.
Cikin tsarin da mahukunta ko gwamnati ta fito da shi akwai batun rabon tallafin kayan abinci domin samarwa 'yan kasar sauƙi da kuma karya tsadar kayan abinci da rage kuncin talauci da 'yan kasa suka faɗa a ciki.
Duk da cewa an jima ana jiran yadda rabon tallafin zai kasance, wasu jihohi an soma jin motsin abubuwan da suke rabawa, amma na jihar Nasarawa a yanzu shi ne ya fi daukar hankali.
An wayi gari da batutuwa daban-daban a shafukan sada zumunta, inda aka riƙa yaɗa hotunan ƙullin shinkafa da sunƙin taliyar da aka raba gida biyu zuwa uku da manja a leda, da sunan tallafin da gwamnati ta raba a sassan jihar.
Wannan abu kusan ya ɗiga ayar tambaya da haifar da shakku a zukatan wasu ƴan kasa da al'umma da ke tunanin anya kuwa wannan batu da gaske ne?
Amma binciken da BBC ta yi ya tabbatar da cewa an yi wannan rabo na kayan abinci tsili-tsili a yankunan Nasarawa.
Wasu mazauna jihohin da muka tattauna da su da ɓangaren gwamnati duk sun tabbatar da wannan rabon tallafi.
'Na yi mamaki lokacin da na ci karo da ƙullin shinkafa a leda'

Muhamud Tanimu mazaunin unguwar Kongo a Karamar Hukumar Keffi ya shaida wa BBC cewa da farko taro aka haɗa wanda mataimakin gwamna ya kaddamar, inda aka bayyana buhun shinkafa 100, kowane mai cin kwano aƙalla shida, da kuma jarkokin man girki da taliya wanda aka shaida cewa na karamar hukumarsu ce.
Sannan aka ce haka za a rinƙa zagaye kowacce Karamar Hukuma da irin waɗannan kaya da suka haɗa da Toto, Nasarawa da Keane, Wamba da dai sauransu
A cewarsa an so a raba kayan tallafin a wajen taron da mataimakin gwamna ya halarta, amma saboda yawan mutane da guje wa wawaso sai aka yanke shawarar cewa a ware wa kowanne yanki da mazaɓa nasa kason daban.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Muhamud ya ce shi dai a nasu mazaɓar mai mutum 700 an kai musu buhun Shinkafa biyu da ledar Taliya biyu da man Gyaɗa a robar swan guda ɗaya.
Ya ce; "mutane da dama sun yi mamaki saboda abin ya kasance kamar wani cin mutunci ko wulaƙanci a gare su. Sannan da suka yi korafi sai aka ce su yi hakuri wannan somin-taɓi ne".
"Mun ba wa mai unguwa shawarar cewa a mayar da abinci saboda ganin ba zai wadatar ba, amma sai aka ce a dai raba kayan duk yanda ya samu kada a raina.
"Shi yasa da aka tashi kasaftawa aka kulla a ledoji, kowa da abin da ya samu.
"Kowanne mazaɓa an kai musu abu iri guda ne, akwai ire-ire na da muka ki karbar rabon nasu. Saboda mu wannan ba ragE raɗaɗi ba ne. Kawai sake ta'azzara matsaloli ne".
A cewar Muhamud an shaida musu cewa asalin shinkafar rabon na tafe nan gaba, saboda haka su karbi wannan rabon a matsayin somin taɓi.
Amma a cewarsa wannan abinci yawansa bai cancanci a shirya babban taro da suka hada da mataimakin gwamna da ciyamomi da kansiloli da sarakuna da kuma masu unguwanni ba.

Talauci ya sa mu karɓar kayan tallafin
Wasu mazauna Keffi irin su Muhamud da BBC ta tattauna da su, sun shaida cewa yanayin talauci ne ya tilasta musu karbar wannan ƙullin.
Galibi, da fari sun yi tunanin samun mudu aƙalla goma, amma abin mamaki sai suka ga da gwangwanin madara aka riƙa yi musu awo.
"Akwai unguwar da aka rinƙa raba leda ɗaya na taliya gida biyar, wasu yankunan ma mutanen sun ki karɓar kayan, inda suka rinka cewa a kai wa marayu".
Hajiya Hadiza ita ma mazauniyar Keffi ce da ta je ta karɓar wannan tallafi, amma sai ta yi karo da wani abin mamaki a cewarta.
"Gidanmu mun kai mutum shida, amma ni kaɗai na samu tallafin shinkafar gwanwani biyu da man da bai zarta na naira ɗari ba, sai talliya da aka karya ta kashi-kashi."
Ta ce ita da maigidanta su goma ne don haka ba ta ga alfannun abin da aka ba ta ba.
Shi ma Abdulkarim Muhammad mai mata biyu da yara ashirin ya ce, "ni shirme aka ba ni ba tallafi ba, saboda cokali biyar aka ba ni na man gyaɗa, taliya kuma silli bakwai da shinkafa gwangwani biyu".
Ya ce maimakon a ba su abin da zai amfane su na kwana biyu, sai suka karkare da abin alla-wadai.
Halima ta ce sun shafe kwanaki cikin yunwa, maigidanta ba ya iya komai saboda ba shi da lafiya, ga shi tallafin ya gaggara.
Ta ce su dai suna rokon a duba a gyara wannan batu.

Asalin hoton, BBC
Me gwamnati ke cewa?
Barrister Yusuf Musa wanda ya kasance babban sakatare a ma'aikatar watsa labarai ta jihar Nasrawa kuma dan kwamitin raba tallafin na Jihar ya bayar da hakurin yadda al'amura suka wakana.
Ya ce "Iyakar abin da muka samu ke nan amma kuma muna fatan nan gaba komai zai inganta. A yi mana uzuri."
Irin wannan rabon tallafi kusan ana iya cewa ya karya gwiwar mutane da dama a Keffi da wasu yankunan Nasarawa da kuma fatarsu ta samun sauki a wannan yanayin da ake ciki.
Ko da yake al'umma irin su Muhamud da sauran al'ummar Nasarawa na fatan ganin sauyi da kuma rokon mahukunta da su kwatanta adalci.
Yanzu haka dai akwai miliyoyin al'umma da ke dakon irin waɗannan kayan tallafi da gwamnati ta yi musu alƙawari.
A tsakiyar watan Agusta ne, bayan kammala taron majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa za ta bai wa kowace jiha naira biliyar biyar domin samar wa al'umma sauƙin matsin da suka shiga sakamakon janye tallafin man fetur.











