Yadda za ku iya gyara kuskuren da kuka yi a saƙon Whatsapp da kuka tura

...

Asalin hoton, WHATSAPP

Kamfanin da ya mallaki manhajar Whatsapp ya ce yanzu mutane za su iya gyara kuskuren da suka a saƙon da suka tura, kamar yadda akan iya yi a wasu mahajojin irin su Telegram da Signal.

Kamfanin ya ce za a iya gyara kuskuren da aka yin ne a cikin minti 15 bayan tura saƙon.

Whatsapp manhaja ce mallakar kamfanin Meta na murka, wanda shi ne ya mallaki Facebook da Instagram.

A cikin makonni masu zuwa ne za a samar da tsarin iya gyara kura-kuren ga mutane biliyan biyu da ke amfani da Whatsapp a faɗin duniya.

Indiya ce ƙasa mafi yawan al’umma da ke amfani da manhajar, inda indiyawa miliyan 487 ke amfani da ita.

Masu manhajar sun ce "Za a iya gyara kuskuren da aka yi wajen rubutu ko a yi ƙarin bayani a kan saƙon, wannan wata dama ce da za ta ba ku ikon sarrafa saƙonninku yadda kuke so.”

Saƙon ya ƙara da cewa hanyar da za a bi wajen gyara kuskuren ita ce “A danna kan saƙon na tsawon daƙiƙu, sai a zaɓi ‘Edit’ daga cikin saƙon da zai fito, ana iya yin haka a cikin minti 15 bayan tura saƙo.”

Sai dai za a nuna wa wanda aka tura wa chat ɗin cewa an yi gyara a saƙon.

Amma ba za a nuna masa tsohon bayanin ba.

Ƙarin bayani:
...

Asalin hoton, Reuters

Kimanin shekaru goma da suka gabata ne aka samar da irin wannan tsarin a manhajar facebook.

A wancan lokacin kamfanin na facebook ya ce ya samar da tsarin ne saboda mafi yawan masu amfani da shi suna shiga ne ta wayoyinsu na hannu, abin da ke sa suna yawan yin kuskure wajen rubutu.

A bara ne ita ma mahajar Twitter ta fito da tsarin yin gyara a saƙonnin da aka yi kuskure wajen rubuta su, inda ake iya yin gyaran cikin minti talatin bayan wallafa saƙo.