Wace ce Nancy Pelosi?

Asalin hoton, Getty Images
Ziyarar Nancy Pelosi mai cike da ce-ce-ku-ce zuwa Taiwan - ƙasar da China ke kallo a matsayin yankin da ya ɓalle amma kuma take samun goyon bayan Amurka na soji - ba ta zo wa masu bibiyar al'amuran siyasarta da mamaki ba.
Cikin kusan shekara 40 ɗin da ta shafe ana damawa da ita a matakan gwamnati, shugabar majalisar dokokin ta yi fice kan sukar China.
Wasu abubuwa da ta yi a wasu lokuta sun fi nuna matsayinta bisa ga abin da ta yi a shekarar 1991 a ziyarar da ta kai Beijing inda ta tunzura hukumomin ƙasar bayan da ta buɗe wata tuta don nuna goyon bayan waɗanda aka yi wa kisan kiyashin rikicin Dandalin Tianmen.
A lokacin ta tsaya ne a wajen da abin ya faru inda jami'an tsaro suka kai wa masu zanga-zanga da ke goyon bayan dimokraɗiyya hari, shekara biyu bayan nan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ko da yake ta kai shekara 82, Pelosi ta kasance wata mai matuƙar sukar gwamnatain kwaminisanci ta China, kuma fito na fiton da take yi da ƙasar ya haɗa da dangantakar ƙut da ke tsakanin da shugaban Tibet da ke neman mafaka wato Dalai Lama.
Sannan kuma tana ɗaya daga cikin masu hannu a matakin da gwamnatin Amurka ta ɗauka a bara na kallon cuzgunawar da China ke yi wa Musulman Uighur a matsayin kisan kiyashi.
"Idan ba za ka iya tashi tsaye don kare haƙƙin ɗan adam ba a China saboda batun kasuwanci, to ka rasa duk wata daraja a hukumance ta yin magana kan hakan a wasu wuraren," in ji Pelosi a wata hira da ta yi da kafar yaɗa labaran Politico ranar 28 ga watan Yuli.
Bulaguron nata zuwa Taiwan zai sa ta zama babbar jami'ar Amurka ta farko da ta ziyarci ƙasar tun shekarar 1997.
Matakin Pelosi ba harzuƙa gwamnatin China kawai ya yi ba, ko a kusa da gida ma ta gamu da suka: Shugaban Amurka Joe Biden a ranar 22 ga watan Yuli ya ce Amurka ta na tunanin ziyarar "ba ta dace ba", yana mai nuna damuwa kan cewa China na iya kallon ziyarar shugabar majalisar a matsayin tsokana.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa ba ta kammala tabbatar da tafiyar ba, Pelosi ta mayar da martani.
"Ina ganin yana da muhimmanci a gare mu mu nuna goyon baya ga Taiwan," a cewarta.
Yadda ta samu ƙwarewa a siyasa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Pelosi wacce aka haida a shekarar 1940, ƴa ce ga tsohon magajin garin Baltimore Thomas D'Alesandro Jr.
Shekararta 12 kacal a lokacin da ta fara halartar babban taron jam'iyya, sannan tana shekara 20 ta halarci taron rantsar da Shugaba John Kennedy.
Da fari tana shiga harkokin siyasa ne ta bayan fage, inda take shiga kamfe da tattara tallafi ga jam'iyyar Democrats a jihar California.
Tana da shekara 47 lokacin da ɗan autanta cikin ƴaƴanta biyar da mijinta mai ɗaukar nauyin harkokin siyasarta Paul Pelosi suka shiga jami'a ne ta fara takara, sakamakon wasiyyar da ƴar majalisar San Francisco, Sala Burton ta bar mata na cewa ta gaje ta.
A yanzu haka tana kan wa'adi na uku a matsayin shugabar majalisar dooki, muƙamin da ya sa ta shiga jerin magadan shugabancin ƙasar bayan mataimakin shugaban ƙasa.
Sannan kuma Pelosi ce mace ta farko da ta zama shugabar majalisar dokokin Amurka.
Sai dai ba batun China ne kawai ya mamaye batun harkokin siyasarta ba.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 2003 ƙiri-ƙiri Pelosi ta nuna adawarta da yaƙin Iraƙi, kuma tana kan gaba wajen neman kare ƴancin ƴan luwadi da madigo a shekarun 1980 da 1990, a waɗannan lokuta kuwa ba a faye mayar da hankali kan irin batutuwan ba a fagen siyasar Amurka.
Sannan ta yi matuƙar sukar matakin Kotun Ƙolin Amurka a watan Yuni na son sauya shari'ar Roe v Wade, hukuncin da ya ce ƴancin mata na zubar da ciki na ƙunshe cikin kundin tsarin mulkin ƙasar.
"A yau Amurkawa ba su da cikakken ƴanci kamar iyayensu mata," in ji Pelosi bayan da aka sanar da hukuncin.
"Matakin tamkar a mare ka ne."
Babbar akidar siyasar Pelosi ita ce adawa da shugabannin mulkin kwaminisanci na China, kuma ziyarar da ta kai Taiwan ta fito da hakan a fili.











