WhatsApp zai fitar da sabbin tsare-tsaren kare sirrin mutane

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban kamfanin Meta da kuma manhajar Whatsapp, Mark Zuckerberg, ya ce sun kawo sabbin tsare-tsaren da za su kare bayanan masu amfani da shafin na Whatsapp.
Daga yanzu, masu amfani da Whatsapp za su iya barin zaurukan sada zumuntar ba tare da kowa ya sani ba, sannan za su iya tantance wanda zai sani idan suka hau dandalin da kuma toshe masu kallon sako sau daya.
Mark Zuckerberg ya ce hakan zai taimaka wajen sanya bayanan Whatsapp zama sirri, da ba wanda zai iya gani sai wanda ya aike da bayanan.
Kamfanin zai fara amfani da sabbin tsare-tsaren ne a wannan wata na Agusta, a wani shirin kamfe da zai fara daga Burtaniya.
Barin zaurukan sada zumunta ba tare da kowa ya sani ba
Dandalin na Whatsapp dai na da wata alama da ke sanar da dukkan mambobin zaurukan sada zumuntar da zarar wani ya fice ko kuma an cire shi daga zauren.
Duk da cewa akwai hanyoyi da mutum zai iya ficewa daga zaurukan ba tare da an sani ba, amma manhajar Whatsapp bai bullo da tsarin ba ga masu amfani da shafin, inda wani lokaci ake samun sabani daga wadanda ke son ficewa daga zauren da kuma mambobi da ke ciki.
Amma a yanzu, masu son fita zaurukan za su iya yin haka ba tare da mambobin zauren sun sani ba, sai dai wanda ya kirkiro da zauren ne kadai zai sani.
Wata shugaba a kamfanin, Ami Vora, ta ce hakan na cikin yunkurin kamfanin na kirkiro da sabbin tsare-tsaren da za su kare sakonnin sirri na masu amfani da dandalin na Whatsapp''.
"Mun yi imanin cewa dandalin Whatsapp shi ne wuri mafi sirri da mutane za su iya tattauna al'amura,'' a cewarta.''
"Babu wata manhajar aike da sakonni a fadin duniya da ke da kare sirrin masu amfani da manhajar kamar sakonni da hotuna na kiran bidiyo da sauransu.''

Asalin hoton, WHATSAPP
Hakan kuma zai iya bai wa masu amfani da dandalin damar zabar lambobin mutane da za su iya sani idan suka hau dandalin.
Janis Wong, wata mai bincike a cibiyar The Alan Turing , ta shaida wa BBC cewa ''abun farin-ciki ne bai wa masu amfani da manhaja damar mallakar sakonninsu - saboda masu amfani da dandalin sada zumunta na son yin iko da bayanan su.''
Sai dai, muddin ba an samar da tsare-tsaren ba ko kuma sanar da masu amfani da manhajoji kasancewarsu, to tasirin su zai takaita a waje daya.
"Idan ba a sanar da mabiya dandalin su sake yin la'akari da dama da suke da ita ba, to ba shi da wani amfani a gare su in har basu san wannan abu ne da za su iya yi ba,'' a cewarta.










