Wasannin da ke gaban Real Madrid cikin watan Satumba

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid FC

Real Madrid za ta buga wasa biyar a cikin watan Satumba nan gaba, ciki har da hudu a gasar La Liga da daya a Champions League.

Kenan cikin mako biyu za ta yi karawa biyar, wadda za ta fara da karɓar bakuncin Real Sociedad ranar Lahadi 17 ga wata a wasan mako na biyar a La Liga.

Real Madrid, wadda take ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya na fatan lashe karawar domin ta ci gaba da jan ragama.

Kwana uku tsakani da fuskantar Sociedad za ta buga wasan farko a cikin rukuni a Champions League da Union Berlin ranar Laraba 20 ga watan a Santiago Bernabeu.

Bayan kammala wasan gasar zakarun Turai za ta fuskanci Atletico Madrid a fafatawar hamayya a La Liga wasan mako na shida ranar Lahadi 24 ga watan.

Daga nan ne Real za ta ƙarƙare da wasa biyu a gasar La Liga da UD Las Palmas ranar Laraba 27 ga wata da kuma kece raini da Girona ranar Asabar 30 ga watan.

Wasannin da Real Madrid za ta buga cikin Satumba:

Real Madrid da Real Sociedad (Ranar Lahadi 17 ga watan Satumba).

Real Madrid da Union Berlin (Ranar Laraba 20 ga watan Satumba).

Atletico Madrid da Real Madrid (Ranar Lahadi 24 ga watan Satumba).

Real Madrid da UD Las Palmas (Ranar Laraba 27 ga watan Satumba).

Girona da Real Madrid (Ranar Asabar 30 ga watan Satumba).