Me ya sa muke tunanin cewa mage ba ta son mutane?

Asalin hoton, Getty Images
A iya cewa karnuka sun fi sajewa cikin al'umma , ba sa kuma iya boye halin da suke ciki, su na nuna alamu da kada jela, sunsuna, kebe kai wuri guda, alamun rashin farin ciki da sauransu.
Duk da hakan abin da ake shirin yin bayani akai ko zane na nufin ba kowanne yanayi ko wasa karnuka ke yi ba.
Su ma maguna su na da yanayin da suke nunawa tamkar magana ga mai kallo, yanayinsu na bakin ciki da farin ciki ba ya buya, sukan kada jela har ma da kunnuwa ko su yi dan kuka.
Sukan nuna alamun son kulla abokata amma ba sosai ba. An fi jin dadinsu a wuri idan masu faran-faran da jama'a ne da son wasa, a wasu lokutan kuma a bar su ba tare da an dame su ba.
Yayin da muke iya bayani kai tsaye kan alaka da shakuwar da ke tsakaninmu da karnuka, duk kuwa da dubban shekarun da maguna suka shafe cikin bil'adam, akwai abubuwan da muke bukatar sani game da su.
Masana sun bayyana ana gane yanayinsu da zarar abinci ya kare cikin kwanosu.
Masu kiwon maguna na ikirarin duk wannan zancen wofi ne, kuma shakuwa tsakaninsu da mage ya wuce tunani, kuma kwatan-kwacin wadda ke tsakanin masu kiwon karnuka.
A Birtaniya akawai sama da magunan da ake kiwonsu a gida miliyan 10. Binciken da aka yi a shekarar 2012, kashi 25 cikin gidaje su na kiwon akalla mage guda.
Da farko ba sa dogaro da iyayen gidansu, wajen cin abinci, ana ba su kwarin giwar nema da kan su, ana kauda abincin da aka san bera zai shiga ciki domin kar ya cutar da su.
Muna kulla alaka da su daga nesa kafin su matso kusa da mu, a hankali suke zama wani bangare na rayuwarmu, kuma su na dadewa fiye da karnuka, wanda yawanci su ke mana farauta, sun kuma dogara da bil'adam wajen samun abin kai wa baka.
Magen da watakil ke nadewa kan kujerarka, ko hawa jikinka, ko bin ka har daki, ba ta cika son fita waje ta yi mu'amala da sauran maguna 'yan uwanta ba.
Sun fi zama cikin nutsuwa, ba kuma tare da an sanya wani ya kula da su ba, idan aka kwatanta da karnuka.
Mutane na son ganin maguna sun yi mu'amala kamar karnuka
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Yawancin lokuta, 'yan adam su na yi wa a bin mummunar fahimta, da gane ainahin yadda za mu rayu da su," in ji Karen Hiestand.
"Karnuka da kamanceceniya da bil'adam, sun kuma dade su na tare. Ta wata fuskar sai mu ce sun fi shakuwa da su fiye da komai.
Amma maguna ba su jima da shiga jikinmu ba, mun gajesu daga iyaye da kakanni amma kuma ba sa daga cikin na hannun damansu."
Hiestand ta kara da cewa, "Saboda su na da kwarin gwiwa da karfin halin kula da kan su, maguna na kara samun daukaka da yin suna.
Amma ko da yanayin rayuwa bai musu dadi ba, ba abin tambaya ba ne. Bil'adama su na sa ran maguna su na rayuwa cikin mu kamar yadda karnuka ke yi. Alhalin mun san ba haka ba ne."
Bincike kan rayuwar maguna, da yadda suke nuna alhini ko farin ciki ko akasin hakan ya tara sakamako mai yawan gaske.
Yawanci tun su na kanana, amma bincike ya gano maguna suna da wata al'ada da dabi'a ta sauyawa daga mutum zuwa mutumin da suke mu'amala da shi.

Asalin hoton, Getty Images
"Wannan na faruwa daga zuriya zuwa zuriya, lokaci zuwa lokaci, musamman daga makwanni shida zuwa takwas.
Idan tun farko sun samu kyakkyawar rayuwa, da shakuwa da mutane, nan da nan za ka ga su na son yin wasanni da su."
A wurare kamar wurare kamar Mediterranean da Japan, masunta na amfani da kyanwa wajen kamun kifi, su na kuma da kyakkyawar alaka da mazauna yankunan da suke ba su abinci.
Amma a Santambul, ana bai wa manyan maguna abinci, ya yin da su kuma ke taimakawa da ayyukan da su ka fi kama da aike, kamar yadda wani shiri na musamman ya nuna.
Shakuwa da mage?
Idan muna son shaƙuwa sosai da magunan mu me ya kamata mu yi?
Kamar karnuka, su ma maguna suna da hanyoyin da suke sadarwa tsakaninsu da mutane, misali ta amfani da kada jiki.
"Ina ganin abu mai wuya ne, mutane su fahimci abin da maguna ke nufi ta hanyar karkada jiki, idan aka kwatanta da karnuka," in ji Kristyn Vitale, mai karatun digirin digirgir kan halayyar maguna.

Asalin hoton, Getty Images
Dalilin da zai sa karnuka su ka fi samun kulawarmu fiye da mage, shi ne kan wani bincike da aka yi a jami'ar Portsmouth, inda aka gano hakan na faruwa saboda karnuka sun iya kwaikwayon wasu abubuawa.
Misali wani abu da yara ko jarirai ke yi, wanda ke tunzura son sanin halin da suke ciki da abin da suke so.
Labari maras dadi kan mage? Mage ba ta da karsashi irin na karnuka. Tana da wani yanayi da idan ta kalle ka, zai dauki hankali musamman idan su na kallon juna, akwai wani sanyi a idanunsu.
Wani bincike da aka yi a jami'ar jihar Oregon da ke Amirka, inda aka rufe karnuka da maguna a daki guda, daga baya iyayen gidansu suka dawo.
"Abin ban sha'awar shi ne yawancin magunan da suke zaune gida tare da iyayen dakinsu, suna shiga sai suka taro su tamkar dai suna musu maraba lale ko gaisuwa.
Sannan suka sake komawa cikin dakin su na watayawa, ba su damu su sanya ido kansu ko za su tafi su bar su. Karnuka ma haka suka yi."
"Idan kare ya yi guje-guje a dakin, da yin wasa da kaya, lokaci zuwa lokaci ya kadan dawo ya kada jela a kusa da ubangidansa, sannan ya sake komawa a ci gaba da tsalle-tsalle, wannan ba abin damuwa ba ne."
Masu binciken sun kira hakan da "Shakuwa tsakanin ubangida da yaronsa" - nutsuwa da samun kwanciyar hankali har ma da farin ciki a duk lokacin da suka waiwayo tare da ganin iyayen gidansu ba su tafi ba.

Asalin hoton, Getty Images
'Magen da ba ta tare da gajiya, tana da dadin mu'amala'
Hiestand ta ce rashin samun tarihi ko bayanai kan dangantakar mage da iyayen gidansu tun da fari, shi ya sa ba a san hakan ba. Kuma karnukan sai suka mamaye rayuwarmu ta yau da kullum.
"A shekarar 2007 na halarci wani taro, da fari na dauka shirme ne.
An yi ta bayanai ma su muhimmanci akan Mage da ban taba sani ba, kama daga batun su na son a zuba musu abinci a kwano daban, da na ruwa, ba sa son kazanta, su na son a dinga nuna musu kulawa.
Wannan binciken wani babi ne na daban, da ban san da shi ba sai da muka zo wannan taron, na yi matukar karuwa."
Misali, yadda mage ke goga jikinta a jikin ubangidanta, alamun soyayya ce.
Amma idan suka yi wa wani na daban, alamu ne na kokarin kulla akala, ta hanyar shafawa mutumin kamshin jikinta.
A lokaci guda kuma magen na kokarin samun wani bangare na kamshin jikin mutumin saboda nan gaba idan sun hadu za ta yi saurin gane ka.
Yawanci maguna na yin haka da takwarorinsu da suke da alaka da su.
A karshe Hiestand, ta karkare da cewa, mage mai kwanciyar hankali, ta fi saurin sabo fiye da wadda ke rayuwa a wuri maras tsafta.
''Suna son a tsaftace kwanon abincinsu, a zuba ruwa mai tsafta, sannan wurin kwanciyarsu, sannan a sanya abin da za su yi fitsari ko bayan gida a gefe, da zarar sun samu wannan nutsuwar, ai fa shi kenan sai tsalle-tsalle da son kulla abota.
Don haka, duk ranar da ka ga mage a wani gida tana nade kan kujera tana kallon ka, ko ta nuna alamun gajiya ta na hamma, kar ka damu, abin da ta ke nufi shi ne, ''ina farin ciki da kasancewarka tare da mu.''











