Abin da ganawar Atiku da Jonathan ke nufi - Masana

Asalin hoton, Getty Images
Muhawara ta barke a fagen siyasar Najeriya, bayan wata ganawa da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, ya yi da tsohon shugaban kasar Good Luck Ebele Jonathan.
'Yan siyasar biyudai basu fito fili sun yi bayanin abubuwan da suka tattauna ba, amma mutane da dama na alakanta ganawar ta su da shirye shiryen tunkarar zaben shugaban kasar na 2027.
Ana dai rade radin cewa dukkansu, na da sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Ganawar jiga jigan 'yan siyasar ta gudana ne a Abuja inda Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Najeriyar Good Luck Jonathan har gida, duk da irin tsamar siyasar da ke akwai a tsakaninsu, duba da cewa Atikun na cikin wadanda suka jagoranci kifar da gwamnatin Jonathan a zaben 2015.
Masana siyasa a Najeriya dai na da banbancin ra'ayi akan yadda suke kallon wannan ganawa tasu.
Farfesa Abubakar Kari, masanin siyasa ne kuma malami a jami'ar Abuja, ya shaida wa BBC cewa, ba abin mamaki bane manyan 'yan siyasa kamar wadannan su hadu su gana har ma su tattauna.
Ya ce," Ba mamaki da yake ana danganta dukkansu da wadanda za su tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027, to kila so suke su magantu ne don su fahimci juna, wala'ala ko daya ya janyewa daya ko kuma a kulla wata alaka ko hadaka."
Shi kuwa a nasa ra'ayin, Dakta Yakubu Haruna Ja'e, masanin siyasa kuma malami a jami'ar Kaduna, ya shaida wa BBC cewa, ganawar za ta firgita mutane da dama a kasar.
Ya ce," Ganawar zata firgita 'yan siyasa manya da ke son tsayawa takara, sannan kuma ita gwamnati mai ci ita ma wannan ganawa zata firgita ta, kuma akwai yiwuwar cewa suna shirye-shiryen fitar da wanda ya kamata don su kwace mulki daga hannun jam'iyya mai mulki."
"Wannan zama da suka yi ba zai rasa nasaba da shawarar wanda zasu tsayar takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba." In ji shi.
Wannan dai na faruwa ne yayin da wasu bayanai ke cewa tuni tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar ya fara shirin zabar wanda zai masa takarar mataimakin shugaban kasa, inda wasu majiyoyi ke cewa ya na tunanin daukar tsohon dan takarar shugaban kasar na jama'iyyar Labour Peter Obi, ko kuma tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi.











