Wane tasiri shigar Atiku ADC zai yi ga siyasar Najeriya?

Atiku Abubakar

Asalin hoton, Atiku Abubakar/Facebook

Lokacin karatu: Minti 4

A safiyar wannan rana ta Litinin 24 ga watan Nuwamba ne tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya karɓi katin shiga jamʼiyyar ADC a hukumance a mazaɓarsa ta Jada da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya.

Wannan matakin da ya ɗauka ya kawo ƙarshen tsawon lokacin da aka ɗauka ana maganar yaushe zai bayyana makomarsa a hukumance bayan tun bayan da ya bar jam'iyyar PDP.

Atiku ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, inda ya wallafa hotunansa riƙe da katin sabuwar jami'yyarsa, sannan ya wallafa gajeren rubutu da ke nuna ya shiga jam'iyyar a hukumance.

A ranar 14 ga watan Yulin 2025 ne tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar ya fitar da sanarwar ficewa daga PDP, jam'iyyar da ya yi takarar shugaban Najeriya tare da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a zaɓen 2023.

Atikun ya kuma ce wajibi ne ya raba gari da jam'iyyar a yanzu bisa la'akari da yadda ta sauka daga abin da aka assasa ta na asali.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka muhawara kan ƴantakara da za su shiga zaɓe domin fafatawa da shugaban Najeriya Bola Tinubu a babban zaɓen 2027.

A wata hira ta musamman da BBC Hausa, Atiku ya ce yanzu kafa jam'iyyar ADC ta haɗakar 'yan adawa ce a gabansa ba maganar takara ba.

Atiku ya yi mataimakin shugaban Najeriya tsakanin 1999 zuwa 2007, Atiku ya kuma bayana dalilin da ya sa ya fice daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP.

Atiku Abubakar ya shafe kusan shekara 40 a fagen siyasar Najeriya, inda ya fara neman takarar shugaban ƙasa tun daga shekarar 1993 a jam'iyar SDP.

Hasashen PDP za ta rikice?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Domin jin ko me hakan yake nufi, mun tuntunɓi Dr Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano, CAS kuma masanin kimiyyar siyasa a Najeriya, wanda ya ce jiga-jigan na ADC sun yi irin abin da Hausawa suke kira ne da "ja da baya ga rago."

Masanin siyasar ya ce ƴan hamayyar sun yi wani irin tsari ne da hasashe na jiran ganin yadda za ta kaya a jam'iyyar PDP kafin su ɗauka mataki na gaba.

Malamin ya ƙara da cewa Atiku ya yanki katin ne a daidai lokacin da ƙarfin PDP ya ragu, musamman ganin yadda suka rasa gwamnoni da ƴan majalisa da wasu jiga-jiganta zuwa APC.

"Dama sun yi hasashe ne kan abubuwan da za su iya faruwa da jam'iyyar PDP, sun yi tunanin za a kai wata gaɓa da abubuwa za su lalace. Shi ya sa sai suka bari har aka kai wannan gaɓar, abubuwan da suka yi hasashe suka faru kafin suka fara sanar da matsayarsu a hukumance."

Sufi ya ce irin wannan jiran dakon da jinkirin ɗaukar matakin da suka yi zai taimaka wa jam'iyyar wajen ƙara mata farin jini, domin a cewarsa, "mutane za su fahimci cewa suna da tsari da tunani mai kyau."

Ya ce wataƙila da a ce Atikun da wasu jiga-jigan na hamayya sun shiga ADC tun a baya, da wasu ba za su shiga ba, "amma yanzu kuwa zai iya samun wasu waɗanda suka gaji da rikice-rikicen PDP, za su iya koma ADC ɗin."

Gaggawa ko jinkiri?

Sai dai bayan karɓar katin da Atiku ya yi, sai aka fara muhawara kan cewa ya yi gaggawa, a yayin da wasu kuma suke cewa ai ya ja ƙafa da yawa.

A game da wannan ne Kabiru Sufi ya ce yanzu ne daidai lokacin da ya kamata Atiku da wasu jiga-jigan hamayyar su koma ADC.

Ya ce yanzu ne lokacin da ya fi dacewa su shiga sabuwar jam'iyyar su fara aikin gyara ta domin fuskantar zaɓen da ke gabansu.

A game da zargin da ake yi cewa babbar jam'iyya mai mulki a ƙasar na katsalandan wajen hana jam'iyyu hamayya takaɓus, masanin siyasar ya ce duk da cewa akwai wannan zargin, amma akwai lokacin da za a iya kwatantawa da irin lokacin da Hausawa ke cewa "a juri zuwa rafi."

"Ita ma kanta babbar jam'iyyar za a kai lokacin da za ta fara fuskantar rikici saboda mutane da yawa sun shiga, kuma kowa na da nasa bukatar. Don haka idan ba ta yi da gaske ba, idan idan aka fara fita daga cikinta, sai ya fi zafi," in ji shi.

Sai dai ya ƙara da cewa bai kamata jam'iyyun hamayya suna rikice-rikice da yi wa juna maganganu marasa daɗi ba a wannan lokacin matuƙar suna so su samu nasarar da suke buƙata.

A game da jam'iyyar da ta fi cancantar jagorantar hamayya a Najeriya, Sufi ya ce, "har yanzu dai idan aka lura da masu riƙe da madafun iko, za a iya cewa PDP ce ke gaba. Amma idan aka duba irin jiga-jigan da suke shiga ADC ɗin, ciki har da Alhaji Atiku Abubakar da Abubakar Malami da sauransu, ita ma ba baya ba a yanzu. Don haka wataƙila za su iya yin gogayya da juna har zuwa lokacin da za a tunkari zaɓe."