Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
City da Utd na hamayya kan Wharton, Ko Zidane zai koma Juventus?
Manchester City da Manchester United na hamayya kan ɗanwasan tsakiya na Crystal Palace da England Adam Wharton, mai shekara 21. (Teamtalk)
Real Madrid na shirin ƙwace wa Arsenal ɗanwasan tsakiya na Real Sociedad da Spain Martin Zubimendi, mai shekara 26 da take hari, a sabon zubin da Madrid ke shiri wanda ya ƙunshi har da ɗanwasan baya na Liverpool Trent Alexander-Arnold da kuma ɗanwasan Bournemouth Dean Huijsen. (AS, via Teamtalk)
Ɗanwasan gaba na Napoli da Nigeria Victor Osimhen, mai shekara 26, wanda yanzu ke taka leda a Galatasaray a matsayin aro, na son ya koma Juventus a bazara . (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Manchester United na son yin sabon zubin maciya raga inda take harin ɗanwasan Turkiya da Juventus Kenan Yildiz, mai shekara 19 da kuma na RB Leipzig da Netherland Xavi Simons, mai shekara 21. (Florian Plettenberg)
Arsenal za ta sabunta kwangilar ɗanwasanta Ethan Nwaneri, mai shekara 18, domin hana wa Chelsea da Manchester City da ke buƙatar ɗanwasan na Ingila. (Mail)
Barcelona na iya sayar wa Aston Villa ɗanwasan gabanta na Spain Ferran Torres, mai shekara 25, kan fam miliyan 30 yayin da Liverpool da Manchester United ke tsohon ɗanwasan na Manchester City. (Fichajes - in Spanish)
Tottenham za ta ware fam miliyan 40 kafin karɓo ɗanwasan baya na Algeria Rayan Ait-Nouri, mai shekara 23, yayin da Liverpool da Arsenal da Manchester United ke ribibin ɗanwasan na Wolves. (Football Insider)
Juventus na iya ɗauko tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane, mai shekara 52, idan ta raba gari da kocinta Thiago Motta, mai shekara 42, inda tsohon ɗanwasan na Faransa ya shafe shekara biyar a matsayin ɗanwasa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Ɗanwasan baya na Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 32, ya nanata cewa ba ya da niyyar barin Real Madrid duk da ƙungiyar Saudiyya ta Al-Nassr na buƙatarsa. (90min)