Wane laifi Abubakar Malami ya yi aka tura shi gidan maza?

..

Asalin hoton, Malami/

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Talata ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN, tare da mai ɗakinsa da kuma ɗansa Abubakar Abdulaziz Malami a gidan yarin Kuje, bayan da suka ƙi amince wa da tuhume-tuhume 16 da Hukumar Yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gabatar a kansu.

EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami da ɗan nasa da kuma mai ɗakinsa, Hajiya Asabe Bashir, masu alaƙala da halasta kuɗaɗen haram da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7.

A cewar hukumar, ana zargin waɗanda ake tuhuma da amfani da asusun banki da dama tare da kamfanoni a tsawon kusan shekaru goma, domin mallakar kuɗaɗen da ake zargin sun samo su ta hanyoyin da ba su dace da doka ba.

Kotu da ƙi amince wa da buƙatar belin mutanen uku a ranar Talata inda llƙali Emeka Nwite ya ce hakan zai zama katsalandan ga hukumar EFCC da ke shari'a da Malami.

Malami da iyalan nasa za su kasance a gidan yarin na Kuje har zuwa ranar 2 ga Janairun 2026, lokacin da lauyoyinsa za su yi jawabi kan buƙatar belinsa a rubuce.

Hotunan Malami da iyalansa a Kotu

Malami na sanye da korayen kaya mai haɗe da babbar riga.

Asalin hoton, EFCC/Facebook

Bayanan hoto, Abubakar Cika Malami lokacin da ake zaman kotu a ranar Talata a Abuja.
Hajiya Asabe tana sanye da baƙaƙen kaya inda ta lulluɓe rabin fuskarta.

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK

Bayanan hoto, Mai ɗakin Abubakar Malami, Hajiya Asabe Bashir lokacin zaman kotu a Abuja ranar Talata.
Abdul'aziz Malami na sanye da dogayen kaya da hula da gilas da kuma biro a bakin aljihu.

Asalin hoton, EFCC/FACEBOOK

Bayanan hoto, Abubakar Abdulaziz Malami wanda ɗa ne ga tsohon minista, Abubakar Malami yayin zaman kotun na ranar Talata a Abuja.

Jerin laifukan da EFCC ke tuhumar Malami

EFCC dai ta ce tana binciken tsohon ministan ne kan laifukan da ake zargin sa da su guda uku da suka haɗa da:

  • Amfani da muƙami ba bisa ƙa'ida.
  • Safarar haramtattun kuɗade.
  • Laifuka masu alaƙa da kadarorin tsohon shugaban ƙasa, Sani Abacha da aka karɓo daga ƙasashen waje da suka kai dala miliyan 346.2.

Sai dai kuma tsohon ministan ya yi watsi da zarge-zargen inda ya alaƙanta abin da yake fuskanta daga hukumar ta EFCC da bi-ta-da-ƙullin siyasa.

Bugu da ƙari, Malami ya zargi shugaban hukumar EFCC, Ola Kayode da ƙoƙarin daƙile gaskiyar rahotan da tsohon ministan ya saki kansa a cikin rahoton Ayo Salami.

Shugaban EFCC ya musanta zargin Abubakar Malami, inda ya ce hukumar na aiki ne ba tare da sani ko sabo ba.

Kadarorin Abubakar Malami da EFCC ta bankaɗo

..

Asalin hoton, BBC COLLAGE

A makon da ya gabata ne hukumar EFCC ta ce ta gano wasu kadarori guda 41 da kuɗinsu ya kai naira biliyan 212 da ta ce tana zargi mallakin tsohon ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ne.

Jaridar TheCable mai zaman kanta a Najeriya ta ruwaito labarin, inda ta ce daga cikin kadarorin akwai otel-otel da gidajen zama da fulotai da makarantu, sannan ta ce ta gano su ne a Abuja a Kano da jiharsa ta Kebbi.

Jaridar ta ce hukumar yaƙi da masu yi tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta gano kadarorin da aka ƙiyasta sun kai na naira biliyan 162,195,950,000 a jihar Kebbi, sai na naira biliyan 16,011,800,000 da Kano, da kuma na naira biliya 34,685,000,000 a Abuja.

Bi-ta-da-ƙulli ake yi min - Malami

A sanarwar da mai magana da yawun Abubakar Malami ya saki, tsohon ministan ya ce a lokacin da yake ministan Shari'a gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti ƙarƙashin Ayo Salami domin binciken zarge-zargen rashawa da cin hanci da kuma amfani da muƙami ba bisa ƙa'ida ba a hukumar EFCC.

Ya kuma ƙara da cewa Olukoyede ya yi aiki a matsayin sakatare na kwamitin amma kuma rahoton musamman sashe na 9 ya same shi da laifi.

Hakan ne ya sa Malami ya kokwanta cewa hukumar EFCC wadda Ayo Olukayode ke jagoranta ba za ta yi masa adalci ba, inda ya nemi wata hukumar ta karɓi binciken.

Wane ne Abubakar Malami?

Sunansa Abubakar Chika Malami kuma ya riƙe ministan Shari'a na Najeriya a shekaru takwas na mulki tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari.

Lauyan mai muƙamin SAN mai shekaru 58 ya yi karatun lauya a jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto.

Malami ya samu tabbacin lauya a 1992 sannan ya zama babban lauya ko kuma SAN a 2008.

Abubakar Malami ya yi takarar gwamnan jihar Kebbi a ƙarƙashin jam'iyyar APC a shekarar 2014 amma bai yi nasara ba, kuma bayan nan ne marigayi Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin ministan Shari'a.