Abin da harin bam da ƴanbindiga suka kai a Zamfara ke nufi

Asalin hoton, Getty Images
Bayan harin bama-bamai da rahotanni ke cewa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane aƙalla 11 a babbar hanyar Dansadau zuwa Gusau a jihar Zamfara ta Arewa maso yammacin Najeriya, ƴan Najeriya sun fara bayyana damuwa kan yadda harin ya faru da kuma abin da zai iya biyo baya.
Shaidu sun tabbatar da cewa tashin bama-baman ya ritsa da babbar mota ɗaukar kaya da kuma Babura, lamarin da ya jefa tsoro a zukatan jama'ar yankin.
Gwamnatin Zamfara ta hannun ɗaya daga cikin masu magana da yawun gwamnan, Mustapha Jafaru Kaura ta tabbatar wa BBC faruwa lamarin, amma a nata ɓangaren ta tabbatar da mutuwar mutum bakwai.
Gwamnatin dai na zargin wannan wani salon harin ramuwar gayya ne ƴanbindigar suka ƙaddamar bayan kisan da ƴan sa-kai suka yi wa wasu daga cikin su a makon jiya a yankin.
Harin bama-baman da ƴanbindigar suka kai ya ɗauki hankali sosai, domin kuwa a baya ba a san su da kai harin bam kan mutane ko ababen hawa ba.
Me kai harin bama-bamai ke nufi?
Yayin da ake ci gaba da hasashen waɗanda suka ɗana waɗannan bama-bamai da kuma abin da hakan ke nufi, masana tsaro irin su Dr Audu Bulama Bukarti, babban mai nazari kan harkokin tsaro a yankin Sahel na gannin cewa ko wace ƙungiya ce ta tayar da bama-bamai lallai manuniya ce ta wani babban abin tashin hankali.
Masanin tsaron na ganin cewa ko wace ƙungiya ce a cikin waɗanda ake zargi da kai wannan hari, wato Lakurawa da kuma sauran ƴanbindiga da ke ayyukan su a wannan yanki, to akwai abubuwa biyu da harin ke nunawa:
- Sabon ilimi ko sabuwar dabara - Dr Audu Bulama ya yi bayanin cewa a bisa sanin da aka yi wa ƴanbindiga da ke ayyukan su a wannan yanki, suna kai hare-hare ne ta amfani da bindigogi da sauran makamai amma ba tayar da bama-bamai ba, don haka watakila sun samo sabon ilimi ne wanda zai iya sauya salon kai hare-haren nasu.
- Dabarar haɗa bama-bamai ko hanyar samun su - Masanin tsaron ya ce harin na iya zama manuniya cewa ''kodai su Lakurawa ko ƴam bandits sun koyi yadda ake haɗa bama-bamai, ko kuma sun samo wata hanyar samo bama-bamai.'' ya yi bayanin cewa ''musamman su bandits, sun ɗauki lokaci suna neman koyon yadda ake hada bam, su kuma Lakurawa ganin cewa dama daga iyakar Mali da Nijar da Burkina Faso suka taho, ba abin mamaki bane idan dama sun iya haɗa bama-baman.
Hanyoyin da ƴan ta'adda ke samun bama-bamai
Dr Audu Bulama ya ce akwai hanyoyi uku da ƴan ta'adda ke samun bama-bamai a Najeriya kamar haka:
- Hadawa da kansu -Masanin tsaron ya kuma yi ƙarin haske kan hanyoyin da ƴan ta'adda ke samun bama-bamai a Najeriya, inda ya ce ''yawancin bama-baman da ake tayarwa a Najeriya, ciki harda waɗanda aka tayar a Kaduna da Abuja da sauran su ba wai bama-bamai ne da ake yin su a kamfani a kawo su ba, su kansu yan ta'addan ne, ma'ana ƴan Boko Haram suke haɗa waɗannan bama-bamai.'' Ya ce suna haɗa bama-baman ne ta hanyar amfani da abubuwa irin su fetir da taki da tukwanen gas da sauran sinadarai da ake iya samu cikin al'umma.
- Kai hare-hare kamfanonin fasa duwatsu - Wata hanyar samun bama-bamai da ƴan ta'adda ke bi ita ce kai hari a kamfanonin fasa duwatsu masu amfani da abubuwan fashewa wajen gudanar da ayyukansu. Masanin tsaron na ganin cewa ta wannan hanyar ƴanbindiga da Lakurawa na iya samun bama-bamai domin ''mun san cewa akwai irin waɗannan kamfanoni na fasa duwatsu a Zamfara, kuma babu mamaki idan suka sato makamai daga can.''
- Kai hare-hare kan sojoji - Haka nan kuma Dr Bulama na ganin cewa ƴan ta'addan na iya samun bama-bami daga irin hare-haren da suke kai wa cibiyoyin jami'an tsaro, musamman sojoji, inda idan suka yi nasara sai su kwashe makaman da ke cibiyoyin.
Amma Dr Audu Bulama ya ce a yanzu ba za a iya yanke hukuncin ko ta wace hanya aka samu bama-baman da aka kai harin na Zamfara ba har sai an tantance ko wane irin bam ne aka tayar, wanda kuma shi ne zai bayar da damar sanin hanyar da aka samo shi. Sai dai ya jaddada cewa ko wane irin bam ne, babban abin tashin hankali ne saboda tayar da bam ko wanne iri ne sai wanda ke da ilimin sarrafa shi ne zai iya tayar da shi.
Ya kuma yi gargaɗin cewa dole a ɗauki matakin gaggawa kan wannan sabon salo domin gudun kada ya ƙara yaɗuwa a tsakanin sauran ƴanbindigar, waɗanda ya ce ''suna da group ɗin whatsapp da suke yaɗa labaran ayyukan junan su.''











