Shekarau 'ya koma' jam’iyyar PDP

Asalin hoton, Shekarau/Atiku
Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan majalisar dattawa Malam Ibrahim Shekarau ya koma jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya 'yan watanni bayan komawarsa NNPP.
Wata majiya mai karfi da ke da kusanci da tsohon gwamnan ta shaida wa BBC Hausa cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar wa Shekarau da tsare-tsarensa kuma sun amince da su.
Atiku ya isa Kano a yammacin Lahadi amma sai Litinin ake sa ran zai gana da kuma karɓar Shekarau a hukumance zuwa PDP.
Shekarau ya ɗauki matakin komawa PDP sakamakon abin da ya kira "rashin adalci" da Rabiu Kwankwaso ya yi musu, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam'iyyar NNPP.
"Gaskiya ne mun shirya tsaf don tarɓar Atiku a Kano don su nemi hannun Malam bayan Shekarau ya yi wa majalisar Shura bayanin halin da ake ciki a NNPP," a cewar majiyar.
Atiku zai je Kano tare da Shugaban PDP na Ƙasa Iyorchia Ayu da sauran jiga-jigan jam'iyyar.
Sanarwa kawai ake jira ta komawar Shekarau PDP

Asalin hoton, @atiku
Tun bayan da ɓangaren Shekarau ya nuna damuwa game da rashin adalcin da aka yi musu a jam'iyyar NNPP, majalisar tuntuɓa ta tsohon gwamnan - wadda ake shura - ta fara nema wa tsagin makoma ta hanyar tattaunawa da sauran jam'iyyu.
Majiyar da ta zanta da BBC ta ce sun kammala shirin tarɓar Atiku tsaf a Kano ranar Litinin bayan sun yi nazari kan tsare-tsaren da ya gabatar musu.
"Sun gabatar mana da tsare-tsarensu, mun yi nazari a kansu kuma za mu karɓe su. A taƙaice dai sanarwa kawai ake jira."
Sanata Ibrahim Shekarau ya koma jam'iyyar NNPP a watan Mayun da ya gabata daga APC mai mulkin Kano bayan rikici tsakaninsa da Gwamna Ganduje, wanda ya kai ga zaɓar shugabannin jam'iyyar biyu.
Daga cikin dalilan da ya zayyana akwai cewa shugabancin APC a Kano ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka na tafiya tare da shi da magoya bayansa a harkokin jam’iyar.
Kazalika, wannan dalilin ne ya sa zai bar jam'iyyar a yanzu bayan ya zargi Kwankwaso da NNPP da ƙin cika alƙawuran da suka yi kafin su koma jam'iyyar tasu. Sai dai Kwankwaso ya ce Shekarau da jama'arsa sun shigo jam'iyyar "a makare".
Kwankwaso bai yi mana adalci ba - Shekarau

Asalin hoton, Facebook/NNPP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cikin hirarsa da BBC Hausa a farkon makon nan, Shekarau ya ce babu gaskiya a batutuwan da jagoran jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi cewa sun shigo jam’iyyarsa a makare.
Wata majiya ta bayyana cewa tun farko an yi yarjejeniya cewa za a bai wa ɓangaren Shekarau kashi kusan 35 na muƙamai, amma daga baya shi kaɗai aka bai wa tikitin takarar sanata.
A nasa ɓangaren, Kwankwaso ya ce sun shiga jam'iyyar a makare amma sun faɗa wa Shekarau cewa su bari a kafa gwamnati don a daidaita rabon.
Duk da cewa Malam Shekarau bai ambaci ko tabbatar da jam’iyyar da zai koma ba a loƙacin idan ya bar NNPP, ya nuna rashin jin daɗinsa kan hana su wasu muƙamai da kuma hana magoya bayansa damar takara a NNPP ɗin.
"Shi jagoran jam'iyyar Rabi'u ne ya faɗi cewa ba mu shigo jam'iyya da wuri ba, kuma bai yi mana adalci ba," a cewarsa.
"Tun daga loƙacin da aka fitar da sunayen 'yan takarar muka yi ƙorafi kuma aka ce mana za a duba, amma har loƙacin da hukumar zaɓe ta tanada na sauya sunan 'yan takara ya wuce ba a yi komai ba."
Shekarau ya ce babu mamaki kwamitin da aka kafa karkashin ɗan takarar gwamnan Kano a NNPP, Abba Kabiru Yusuf, su ne suka dinga jan kafa.











