An bankaɗo laifukan cin zarafi biyar a rundunar 'yan sandan London

Hoton yan sandan London

Asalin hoton, Getty Images

An fitar da wani rahoto da ya bankaɗo tarin shedun abubuwan cin zarafi da waɗanda ba su dace ba da ake aikatawa a rundunar 'yan sandan birnin London, waɗanda suka nuna taɓarɓarewar aikinta.

Binciken ya nuna ƙarara yadda ƴan sanda ke nuna wariya ga mata da yara sannan kuma ita kanta rundunar ba ta iya binciken kanta ba bugu da ƙari mutane ba su da ƙwarin gwiwa a kan ƴan sanda, kamar yadda rahoton Baroness Louise Casey ya nuna.

Ga wasu fitattun abubuwa guda biyar da rahoton mai shafi 362 ya bankaɗo:

An yi watsi da binciken fyaɗe saboda lalacewar firji

Binciken ya nuna cewa yanayin aikin rundunar ƴan sandan ya taɓarɓare ta yadda hakan yake jefa rayuwar mata da yara cikin haɗari sosai saboda gazawar fannin binciken ƙwararru a kan irin waɗannan laifuka.

Binciken ya ce a wani lokaci ƴan sandan sai da suka yi fama wajen rufe wani tsohon firji da ke ɗauke da tarin kayan sheda na fyaɗe da cin zarafin mata, sannan sukan ɗauki dogon lokaci suna jiran sakamakon bincike.

A wani lokaci da aka yi tsananin zafi a shekara ta 2022, ana ji ana gani ba yadda za a iya wasu abubuwan da aka adana a cikin firji, waɗanda suka hada da majina da jini da kamfai suka lalace saboda firjin ya samu matsala.

Wannan na nufin ba yadda za a iya dole ta sa aka haƙura da binciken laifin da ake yi na cin zarafi na lalata da fyaɗe, kamar yadda wani ɗan sanda da ya nemi a ɓoye sunansa ya faɗa wa masu binciken.

Wani jami'in ƴan sandan da aka sakaya sunansa wanda a nan za mu iya bayyana shi da jami'i G, ya sanar da masu haɗa rahoton cewa akwai lokacin da sai da ƴan sanda uku suka taru domin rufe wani firji maras kyau saboda ya cika da kayan shedar zargin aikata fyaɗe.

An tilasta wa ɗan sanda mabiyin addinin Indiya na Sikh aske gemu saboda ya zama kamar abin dariya

Rahoton ya gano tarin gallazawa da ake yi wa wasu ƴan sandan misali inda wasu jami'an ke ƙyamar mata da nuna wariyar jinsi da kuma tsanar masu neman jinsi ɗaya da ke aikin.

Daga cikin irin waɗannan ƙorafe-ƙorafe akwai inda ake ce wani ɗan sanda mabiyin addinin Indiya na Sikh ta kai sai da ya rage gemunsa saboda wani jami'in yana ganin gemun ya zama kamar wani abin ban dariya.

Haka kuma wani ɗan sandan shi ma mabiyin Sikh wata rana ya samu rawaninsa a cikin wurin ajiye takalmi an sauya masa wuri daga inda ya saba ajiyewa.

Hoton 'yan sanda da masu zanga-zanga

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kwanan addu'a kan kisan da Sarah Everard da wani dan sandan London ya yi wa Wayne Couzens

Shi kuwa wani ɗan sandan Musulmi wata rana ya samu naman alade ne an sa masa a cikin takalminsa na aiki. Ya ce abin ya ba shi tsoro sosai to amma bai faɗa wa kowa ba saboda gudun abin da hakan zai iya haifarwa na ramuwar gayya.

Akwai kuma wani ɗan sandan baƙar fata wanda ɗan luwaɗi ne, da ba ya ɓoye wannan halayya ta sa, inda a wani lokaci wasu abokan aikinsa suka riƙa masa zambo suna zolayarsa a gaban sauran abokan aiki, inda a wani lokaci aka ɓoye kayansa aka kuma lalata wajen da yake kulle kayansa.

Binciken ya gano cewa aƙalla ɗaya daga cikin biyar na jami'an ƴan sandan na London waɗanda ke yin halayyar neman jinsi ɗaya sun taɓa fuskantar tsangawama.

Wani ko wata daga cikin masu wannan halayya da ta fada wa abokan aikinta a kan abin da aka yi mata, ta ce abin ya ba ta tsoro har ma tana ganin rundunar ƴan sandan ba abar da za ta amince da ita ba ce.

Ana tilasta wa mata cinye tarin cukwi

An bai wa 'yan kwamitin binciken bayanin yadda ake kunyata kananan jami'ai ta hanyar sanya su cikin wani abu da za a iya cewa tamkar wata kungiya a cikin aikin ɗan sandan.

Wata mace ƴar sanda da ke aiki a ɓangaren ƙwararru ta yi bayanin yadda manya ke cin zarafin ƙanana abin da ta ce ya ƙazanta sosai.

Hanyar shigar da jami'ai cikin wannan tsari shi ne kamar ta hanyar gasar cin abinci, inda za a tilasta wa mata cin cukwi babba har sai sun yi amai, kamar yadda ta ce.

Hoton dan sandan London

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Binciken kwamitin Casey ya bayyana rundunar ƴan sandan London a matsayin mai nuna wariyar jinsi da ƙyamar mata da masu neman jinsi ɗaya

Rahoton ya bayyana rundunar ƴan sandan ta London da cewa tana nuna wariyar launin fata da kyamar mata da tsanar masu neman jinsi ɗaya.

An sheda wa jagorar binciken yadda aka ci zarafin wani jami'i ta lalata a wajen wanka a matsayin wata hanya ta shigar da shi wannan tsari.

Abin da ta ce ya zama kamar wata al'ada inda ake maganar abin a tsakanin jami'an ƴan sandan kuma a fili.

Dukkanin waɗanda suka ƙi yarda a yi musu haka ana ƙyamatarsu ana musu kallon kamar waɗanda ba sa cikin wannan ayari na musamman na ƴan sandan.

Akwai ma rahotannin da ke nuna cewa ana yi wa wasu fitsari a jiki a wajen wanka.

Ana sa ƴan sanda goge WhatsApp ɗinsu

A watan Fabarairu a shekarar da ta wuce an rika aikawa da wasu saƙonnin WhatsApp na nuna wariya inda jami'an ƴan sanda da ke chaji ofis na Charing Cross suka aika shi.

Sai kuma aka ƙaddamar da wani kamfe (Not In My Met)a tsakanin ƴan sandan na neman ƙarfafa wa jami'an gwiwa da su fito fili su yi magana kan wariyar da aka nuna musu.

Wata ƴar sanda ta ce an riƙa ƙarfafa musu gwiwa kan su goge saƙonnin WhatsApp na wariya a lokacin wani taro na kamfe ɗin.

Hoton hedikwatar ƴan sandan London

Asalin hoton, Getty Images

Ta ce akwai wasu abokan aikinta da aka riƙa tura musu wannan saƙo a wasu tarukan.

Rahoton ya ce ana amfani da shafin WhatsApp wajen ƙoƙarin ɓoye miyagun abubuwan da ake yi a rundunar ƴan sandan domin kada su bayyana.

A wata daga cikin rundunar musamman ta ƙwararru ta ƴan sandan na London, wadda ke kula da harkokin da suka shafi bindigogi, wato MO19, rahoton ya ce akwai wani saƙo na sirri da ake turawa a tsakanin mambobi idan an gano ana bincike a kan wani lamari, inda nan da nan suke tura saƙo a tsakanin waɗanda ke cikin masu ta'ada a cikinsu.

A saƙon za su ce kowa ya yi sauri ya goge WhatsApp ɗin kungiyar tasu domin kada a gano su a binciken.

Binciken ya gano cewa za su rubuta wata kalma ta sirri LANDSLIDE, inda da ganin wannan kowa sai ya yi sauri ya goge saƙonnin da ke ciki ya goge WhatsApp din su ƙirƙiri wani sabo.

An rasa inda wani yaro da ke neman taimako yake bayan da ƴan sanda suka kama shi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An nuna damuwa kan yadda ƴan sandan na London ke binciken yara, bayan abin da wasu ƴan sanda suka yi wa wata yarinya baƙar fata a shekarar da ta gabata, inda jami'ai biyu suka tuɓe yarinyar lokacin da suke binciken ta kuma ya kasance tana al'ada a lokacin.

Rahoton ya nuna yadda ake nuna wariya ta launin fata inda ake ɗaukar yara baƙar fata tamkar manya idan ana bincike a kansu.

A wani lamari wani yaro baƙar fata ya gaya wa wani ƙwararre wanda ba ɗan sanda ba ne ya ce yana yawo da wuƙa domin kare kansa, kuma yana cikin wata ƙungiyar ɓata-gari, amma kuma yana son a taimaka masa ya fita.

Bayan nan wata rana sai wani babba ya muzguna wa yaron, sai wannan ƙwararre ya kai rahoton muzgunwar da aka yi wa yaron ga ƴan sanda ya kuma miƙa musu wuƙar.

To amma sai wani sashe daban na ƴan sandan ya je wurin ya kuma kama yaron.

''Mun rasa yaron gaba ɗaya, ya fita daga ƙungiyar gaba ɗaya,'' kamar yadda aka gaya wa masu hada rahoton.

Masu binciken sun ce akwai sheda da ke nuna cewa ga alama rundunar ka iya binciken kura-kurai da jami'anta ke yi na nuna wariya a kan yara baƙaƙen fata.

To amma kuma harwa yau akwai alama ta nuna rashin damuwa wajen zurfafa bincike ko waɗannan matsaloli na nuna wariyar launi sun fi girman da aka gani.