Liverpool na son rabuwa da Nunez, Guardiola na neman hanyar gyara Man City

Nunez

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool watakil ta sayar da Darwin Nunez mai shekara 25 a wannan kaka, yayinda matashin daga Uruguay ke fuskantar kalubale a wannan karon a Anfield. (The Athletic - subscription required)

Manchester United ke kan gaba a fafutikar saye ɗan wasan tsakiya a Crystal Palace da Ingila, Adam Wharton, mai shekara 21, duk da cewa Juventus ba ta hakura ba. (CaughtOffside)

Ɗan wasan tsakiya a Ingila, Jack Grealish mai shekara 29, da na Belgium, Kevin De Bruyne mai shekara 33, da mai buga gaba a Portugal Bernardo Silva mai shekara 30, na cikin 'yan wasan Manchester City da za a yi garambawul da su a wannan kaka, yayinda Pep Guardiola ke son sabunta tawagarsa. (Daily Star)

Guardiola na son daidaita lamura a Manchester City, amma idan aka ce ya tafi, ƙungiyar ba za ta wani damu ba. (Telegraph - subscription required)

AC Milan za ta saurari tayi a kan ɗan wasanta mai shekara 25, Rafael Leao daga Barcelona da Chelsea da suka jima suna zawarcin ɗan wasan na Portugal. (La Gazzetta dello Sport in Italian)

Manchester United na son sayen mai kare ragar Atalanta da Argentina, Juan Musso mai shekara 30 - da ke zaman aro yanzu haka a Atletico Madrid - yayinda damuwa ke karuwa kan Andre Onana mai shekara 28 daga Kamaru. (Fichajes - in Spanish)

Manchester United na kuma duba yiwuwar sayen ɗan wasan AC Milan da Faransa, Theo Hernandez mai shekara 27. (Fichajes - in Spanish)

Manchester United na cikin ƙungiyoyin Turai da ke son saye ɗan wasan Sporting da Portugal, Geovany Quenda mai shekara 17, amma har yanzu ba su cimma yarjejeniya da ƙungiyar ko matashin ba. (TeamTalk)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Arsenal ta samu kwarin-gwiwa kan saye mai tsare raga na Sifaniya, Joan Garcia mai shekara 23, a wannan kaka daga Espanyol. (Teamtalk)

Newcastle za ta dauko mai tsaron raga a Burnley da Ingila, James Trafford mai shekara 22, a wannan kaka ko da ƙungiyar ta samu dama shiga Firimiya. (Mail Plus - subscription required)

Newcastle na kuma son ɗan wasan Bournemouth da Ghana, Antoine Semenyo mai shekara 25. (talkSPORT)

Barcelona da Bayern Munich da Paris Saint-Germain dukkaninsu na son saye tsohon ɗan wasan Manchester United Mason Greenwood, mai shekara 23 daga Marseille.(GiveMeSport)

Kocin Chelsea, Enzo Maresca na cigaba da samun goyon-baya daga 'yan wasa da ƙungiyar duk da cewa wasa uku ya ci a cikin 11 daya buga. (Mail Plus - subscription required)

Babu wata yarjejeniya da ta bai wa ɗan wasan Chelsea da Ingila, Cole Palmer mai shekara 22, damar barin ƙungiyar idan suka gaza samu dama a gasar zakarun Turai. (Mail Plus - subscription required)

Kocin Bournemouth, Andoni Iraola ya kasance wanda Tottenham ke son ya maye gurbin Ange Postecoglou idan ɗan Australiar ya yanke hukuncin tafiya. (talkSPORT)

Arsenal ta amince da yarjejeniyar sayen ɗan wasan Scotland, Callan Hamill mai shekara 15, daga St Johnstone a wannan kaka. (Athletic - subscription required)