Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilanmu na haramta yaɗa waƙar 'Tell Your Papa' ta Eedris Abdulkareem - Gwamnati
Gwamnatin Najeriya ta haramta yaɗa waƙar 'Tell Your Papa' ta fitaccen mawaƙin kudancin Najeriya, Eedris Abdulkareem.
A waƙar, mawaƙin ya yi kira ne ga ɗan shugaban ƙasar, Seyi Tinubu da ya faɗa wa mahaifinsa cewa, "mutane suna mutuwa" saboda ƙuncin rayuwa da rashin tsaro, sannan ya ƙara da cewa, "akwai yunwa" a ƙasar.
A wata wasiƙa da hukumar kula da kafofin labarai ta Najeriya wato NBC ta fitar, ta buƙaci kafofin yaɗa labarai na ƙasar da su guji saka waƙar domin a cewarta, ta saɓa da dokokin yaɗa labarai na Najeriya.
NBC ta ce lafuzzan da aka yi amfani da su a waƙar ta Tell Your Papa "ba su dace ba", sannan ta ƙara da cewa waƙar ta saɓa da tarbiyyar ƙasar.
Waƙar wadda aka fitar a farkon makon nan da ake ciki, ta samu karɓuwa matuƙa musamman a kafofin sadarwa na zamani a Najeriya, sannan ta haifar da zazzafar muhawara game da matsalar tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasar.
A watan Mayun 2023 ne Tinubu ya ɗare karagar mulki, inda a lokacin ya sanar da cire tallafin man fetur, wanda ya jawo tsadar rayuwa a ƙasar.
Haka kuma akwai fargaba da barazanar rashin tsaro a ƙasar, musamman garkuwa da mutane da ƴanbindiga suke yi, da kuma matsalar rikicin Boko Haram da ake fargabar suna sake dawowa da ƙarfinsu.
Me Eedris Abdulkareem ya ce a waƙarsa?
A waƙar, wadda mawaƙain ya yi amfani da Ingilishi da Yoruba da Pidgin, Abdulkareem ya ce Seyi Tinubu ya faɗa wa mahaifinsa cewa, "ba ya ƙoƙari" kuma ya "kasa cika alƙawuran da ya ɗauka."
Mawaƙin ya kuma shawarci Seyi Tinubu da ya riƙa tafiyte-tafiye a mota maimakon jirgin sama domin ya fahimci halin da ƴan Najeriya suke ciki.
Ya ce: Seyi, ka yi ƙoƙari ka riƙa tafiya ta hanyar titi ba tare da jami'an tsaro ba saboda ka ji takaicin da sauran ƴan Najeriya ke ji...Wasu daga cikin ƴan Najeriya da ke tafiya ta ƙasa tamkar an yanke musu hukuncin kisa ne," in ji Abdulkareem.
Haka nan Eedris ya ambato wani ɓangare na turka-turkat siyasa da ake fama da ita a ƙasar, ciki har da rikicin da ya kaure tsakanin shugaban majalisar dattijan Najeriya Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Abdulkareem ne mawaƙin da ya yi waƙar Nigeria jaga jaga a shekarar 2003, wadda ta yi fice matuƙa a zamanin shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.