An haramta waƙar 'Warr' ta Ado Gwanja a Najeriya

Hukumar kula da kafafen sadarwa ta NBC a Najeriya ta haramta waƙar 'Warr', wadda sanannen mawaƙin Hausa Ado Isa Gwanja ya yi a baya-bayan nan.

A sanarwar da NBC ta fitar ta ce waƙar 'Warr' ta bayyana rashin tarbiyya da kalaman da ba su dace ba.

Hukumar ta ce ''a cikin waƙar akwai zagi kai tsaye da kuma nuna yadda wasu ke tangadi bayan sun bugu da barasa ko kuma giya.''

NBC ta ma yanko wasu baituka daga wakar da ta ce zagi ne ƙarara a cikinsu, kamar haka;

''....Kafin a san mu ai mun ci kashin Ubanmu...

''...Zani zo bari in shafa hoda, ko kin zo da ke da hodar ku ubanku zan ci, warr...

''...Kowa yace zai hana mu uban sa zan ci...

Baya ga kalaman da ta ce sun saɓa doka, NBC ta ce a hoton bidiyon waƙar ta 'Warr' wadda yanzu haka ta karaɗe shafukan sada zumunta da kuma Youtube, an nuna yadda ake shan barasa kai tsaye.

NBC ta ce hakan ya saɓa sashe na 3.18.2, da kuma na 3.9 na hukumar kula da kafafen sadarwa ta Najeriya.

Bugu da ƙari, NBC ta nuna damuwa kan yadda ake ta yaɗa waƙar a wasu gidajen talabijin na Arewacin Najeriya, wanda hakan ya sa take tunanin cewa kafofin ba su saurari waƙar da kyau ba kafin su saka ta duniya ta gani.

Waƙoƙin 'Warr' da 'Cass' da Ado Gwanjo ya saki a baya-bayan nan na daga cikin waƙoƙin da suka ja hankali sosai a tsakanin matasa a Arewacin Najeriya, musamman irin yadda suke kwaikwayon baitukansu a shafukansu na TikTok.