Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waƙoƙin Hausa 10 da suka fi shahara a 2021
DagaIbrahim Sheme da Abba Muhammad
A kowace shekara, akan samu waƙoƙin da suka ciri tuta a fagen nishaɗantarwa na Hausa. A da, waƙoƙin gargajiya da aka rera da kayan kiɗa irin su kalangu, taushi, goge, ƙwarya, kukuma, garaya, molo da sauransu ne ke riƙe kambin, amma a shekaru masu yawa waƙoƙin zamani, waɗanda ake bugawa da fiyano, su ne ke mamaye fagen.A cikin irin waɗannan waƙoƙin, akwai waɗanda mawaƙansu ke riƙe wuta sama da shekara ɗaya, wato a kasa ture su. Akan sababbin mawaƙa waɗanda ke ɓullowa su shiga cikin jerin mawaƙa goma da waƙoƙinsu suka fi shahara a shekarar.
Mun duba waƙoƙin Hausa 10 da suka fi shahara a 2021 (da sunayen mawaƙansu) kamar haka:
1. 'Fanan' - UMAR M. SHAREEF (tare da Zubaida Mu'azu)
Wannan waƙar ta fito ne a cikin fim ɗin 'Fanan' na babbar furodusa kuma tsohuwar tauraruwa Mansurah Isah.
Fitaccen mawaƙi Umar M. Shareef ne ya rubuta kuma ya rera ta tare da mawaƙiya Zubaida Mu'azu (Zubby) yayin da fitaccen tauraro kuma tsohon mijin Mansurah, Sani Musa Danja, da sabuwar 'yar wasa Sabira Mukhtar ne taurarin shirin waɗanda suka bi waƙar.
'Fanan' waƙa ce tsakanin masoya. A cikin ta, Umar da Zubaida sun nuna ƙwarewa wajen zuba kalmomin soyayya da shauƙi. A bana dai babu wata waƙar soyayya da ta fi ta fice.
Tun farko Mansurah ta fara fitar da waƙar ne a shafin ta na Instagram, inda ta datsi wani ɓangare ta yi gajeren bidiyo ta ɗora a shafin nata, kuma ta rubuta 'We are back'.
Waƙar ta ɗauki hankalin mutane sosai saboda kalaman da ake faɗi a daidai wurin da ta yi bidiyon ya na nuni da cewa kamar sun koma zaman auren su ne da Sani, bayan rabuwar ban-mamaki da su ka yi a bana.
Abokan sana'ar Mansurah da ƙawayen ta da masoya da sauran mutanen gari, musamman mata matasa, kowa ya riƙa ɗora guntun bidiyon da ya ɗauka tare da waƙar ya na ɗorawa a shafin sa. Yanzu an kai tsawon aƙalla wata uku, amma kamar yau aka yi waƙar.
A TikTok, ita ce waƙar Hausa da ta fi kowace waƙa tashe a waƙoƙin soyayya daga arewacin Nijeriya.
Haka kuma a gidajen rediyo da wuya a ɗauki tsawon lokaci ba saka waƙar ba.
2. 'Daina Kuka' - NAZIRU M. AHMAD
Fitaccen mawaƙi Naziru M. Ahmad ya yi waƙar 'Daina Kuka', aka saka ta a cikin fim mai dogon zango na 'Labari Na' wanda ake haskawa a tashar talbijin ta Arewa 24. Nafisa Abdullahi, wadda ta fito a matsayin Sumayya a shirin, ta hau waƙar tare da Naziru M. Ahmad, wanda ya fito a matsayin Sarkin Waƙa kuma ubangidan ta a shirin.
Waƙa ce da ke nuni da irin yaudarar da ke faruwa tsakanin masoya. A labarin, Sumayya na son Muhmud (Nuhu Abdullahi), shi kuma ya koma ya na son Laila (Maryam Waziri). A cikin waƙar, ta bayyana irin son da ta ke yi masa, amma kuma ta yi mamaki da irin yadda ya juya mata baya saboda kuɗi.
An yi waƙar ne a lokacin da Laila ke murnar bikin zagayowar ranar haihuwar ta, inda su ka gayyaci Sarkin Waƙa da ya zo ya nishaɗantar da su a wurin bikin, shi kuma ba tare da sanin abin da ke faruwa ba, sai ya ta taho da Sumayya tunda yarinyar ofishin sa ce, kuma tare su ka yi waƙar bikin.
Ganin Sumayya, sai Mahmud duk ya ruɗe, ya tashi zai fita, sai ita kuma Sumayya ta ƙirƙiri waƙar 'Daina Kuka', shi kuma ubangidan ta ya rufa mata baya.
Waƙar ta yi wa 'yan mata da dama daɗi, musamman irin waɗanda samari su ka yaudara. Da yawan su sun riƙa yin gajeren bidiyo su na ɗorawa a soshiyal midiya, musamman a 'WhatsApp Status', inda sun tabbata wanda su ka ɗora waƙar domin shi zai gani. Sai kuma shafin Instagram.
Wannan ya sa waƙar ta yi fice a wannan lokacin sosai.
3. 'MallakiNa' - KHAIRAT ABDULLAHI
Khairat Abdullahi ita ce kan gaba a cikin mawaƙa mata a yanzu. Waƙar ta, 'Mallaki Na', waƙa ce ta soyayya da babu muryar namiji a cikin ta.
Mawaƙiyar ta antayo kalaman soyayya da ke nuni da cewar ta na yi wa masoyin ta ne. Waƙar ta yi tasiri matuƙa, musamman a wurin masoya.
Khairat ta yi bidiyon waƙar tare da jarumi Umar Bigshow. Idan har mutum ya saurari kalaman waƙar, zai samu sanyin zuciya, musamman idan sabon ango ne.
4. 'Ina Son Aure' - MG BOY
Zaharaddin Auta, wanda aka fi sani da MG Boy, sabon mawaƙi ne da tauraron sa ya fara haske daga wajen ƙarshen shekarar 2020. A yau ya na ɗaya daga cikin mawaƙan da ke tashe, domin kuwa a bana in ka ɗebe Umar M. Shareef babu mawaƙin da waƙoƙin sa ke yawo a gari kamar sa.
Farin jinin da waƙar MG Boy ta 'Baba Ka Yi Mini Aure' ta yi ya tabbatar da bunƙasar da ya yi a bana.
Waƙar ta yi tasiri a wurin matasa, musamman 'yan mata, don sun yi ta maimaita ta a kafafen sada zumunta na Instagram da TikTok inda su ke nuna su aure su ke so a yi masu, don sun isa aure.
MG Boy ya yi bidiyon waƙar tare da Musa Alhassan (Kallah) a matsayin mahaifin sa, yayin da Hajiya A'isha NTA ta fito a matsayin mahaifiyar sa.
5. 'Mai Waƙa' - ALI JITA
'Mai Waƙa' waƙa ce da fitaccen mawaƙi Ali Isah Jita ya yi inda ya ke faɗin hujjojin mawaƙa na yin waƙa tare da zayyano wasu daga cikin abokan sana'ar sa.
Sannan ya yi magana game da yadda wasu su ke ci masu fuska, har su na kiran su da 'yan nanaye. Shi kuma a waƙar ya ke tambayar su da cewa su kuma 'yan wanene?
Baitin da ya fi tsuma masu sauraren waƙar shi ne inda ake cewa, "Na faɗa na ƙara, / Wanda ya so ka ka so shi, / Wanda ya ƙi ka ka ƙyale shi, / Hassada babban ciwo a zuciyar mai ƙulla ta, / Na gaba tuni ya yi gaba, / Haka Allah ya hukunta..." Mutane jama'a da dama sun ɗauki waɗannan kalamai su na yi wa abokan hamayyar su martani, musamman idan akwai wata jiƙaƙƙa a tsakanin su.
Shi ma an yaɗa bidiyoyi da dama a Instagram da TikTok a kan waƙar.
6. 'Mamar-Mamar' - ADO ISAH GWANJA
An fi sanin Ado Gwanja a matsayin mawaƙin matan biki, har ta kai ana yi masa laƙabi da Limamin Mata. A bana, da waƙar 'Mamar-Mamar' ne Gwanja ya fi cin kasuwa, domin kuwa a wuraren biki ita ta fi tashe.
Gwanja ya zuba basira sosai a waƙar kamar yadda ya kan yi domin mata a kowane lokaci.
Duk da yake akwai batsa a ciki - wanda ba sabon abu ba ne a waƙoƙin Gwanja - abin da ya fi jan hankalin mutane shi ne inda ya ke cewa, "Allah ka aika munafikin mu ƙarshen nesa, / Tafiyar ƙasa ko da lafiya ko babu, / Kai shi garin da ko kuyanga babu, / Bar shi a can ko da arziki ko babu, / Mu mun sha Tabara mun sha Yasin, / Kuma mun sha rigakafin Allah-tsine, / Allah bar mu da mata namu, / Mu yi ta kiɗa irin na ƙwatar 'yanci".
Wannan baiti shi ke ƙara tsuma masu saurare, domin a gidan biki ana kan zuwa baitin kowa zai ɗauka ya na bi. Haka kuma an yi amfani da shi a soshiyal midiya sosai, domin hatta abokan sana'ar sa ba a bar su a baya ba.
7. 'Da Ma' - NAMENJ da HAMISU BREAKER ƊORAYI
'Da Ma' waƙar soyayya ce da fitaccen mawaƙi Ali Jubril, wanda aka fi sani da Namenj, ya rera da kalaman soyayya masu tausasa zuciya waɗanda duk wani masoyi ya yi wa masoyiyar sa iyakar ta kenan. Kuma sai ya samu tallafin fitaccen mawaƙi Hamisu Breaker Ɗorayi, wanda ya ƙara wa waƙar armashi.
Duk wanda ya san Namenj ya san shi da sake tsofaffin waƙoƙin shekarun baya, irin na su Yakubu Muhammad, Sadi Sidi Sharifai, Adamu Hassan Nagudu da sauran su. A wannan karon sai ya zo da sabon salo da waƙar soyayya, kuma ta karɓu matuƙa a wurin matasa.
Ita ma 'Da Ma' ta yi tashe a soshiyal midiya a bana kamar yadda sauran waƙoƙi su ka yi. Babu inda ya ɗauki hankalin mutane irin amshin waƙar, wato "Da ma da ke na fara haɗuwa, da na yi aure tun tuni".
8. 'Supa'- DJ A.B. da MR. EAZI
Waƙar 'Supa' ta Haruna Abdullahi (DJ A.B.) da Mr. Eazi ce kan gaba a wannan shekarar a cikin rukunin waƙoƙin hip-hop. An yi ta ne da ingausa, wato kwaɗon Hausa da Turanci.
Ficen waƙar ya samu tagomashi daga abokin sana'ar DJ A.B., fitaccen mawaƙin nan Deezell, wanda ya shirya guntun bidiyo ɗauke da wata farar kwat da wandon ta a hannun sa, ya na maimin wurin da A.B. ke faɗin, "Na je na dawo, / Kalli abin da na kawo".
A lokacin, DJ A.B. bai fitar da waƙar ba ma, don wasu ma sun ɗauka sabuwar waƙar Deezell ɗin ce.
Tun daga wannan bidiyon sai Instagram da TikTok su ka ɗauka, wanda har zuwa yanzu kasuwar waƙar na ci a soshiyal midiya, musamman cikin wannan wata na Disamba. Har 'yan Kannywood maza da mata sun yi ta yin bidiyo da daidai wurin "Na je, na dawo, kalli abin da na kawo."
9. 'Rigar So' - LILIN BABA
Fitaccen mawaƙi Shu'aibu Ahmed Abbas, wanda aka fi sani da Lilin Baba kuma furodusa kuma jarumi a yanzu, shi ne ya yi wannan waƙar ta 'Rigar So' a daidai lokacin da ya ke shirya fim ɗin sa mai suna 'Wuff', wanda shi ne jarumin da ke jan fim ɗin.
Waƙar soyayya ce da ya ɗauki bidiyonta tare da fitacciyar jaruma Ummi Rahab, wadda ya zazzaga kalaman soyayya masu ratsa zuciya.
Amshin waƙar ya ja hankalin masoya, waɗanda suka yi ta ɗaukar kan su da wayoyinsu suna bin amshin waƙar sannan su ɗora a shafukansu na zumunta. Duk wanda ya ɗora a shafinsa na Instagram sai ya maƙala sunan mawaƙin, shi kuma sai ya yaɗa a nasa shafin.
10. 'Ƙaddarar Rayuwa' - SALIM SMART (tare da KHAIRAT ABDULLAHI)
Jigon 'Ƙaddarar Rayuwa' shi ne soyayya, amma ba irin wadda aka saba ji ba ce.
A waƙar, budurwa ce ke ba da labarin irin son da take yi wa saurayinta, wanda ita ta ɗauki lamarin a matsayin ƙaddarar rayuwa a gare ta, shi kuma saurayin a baitinsa haƙuri yake ba ta, inda har ya nuna a rayuwarsa in babu ita tamkar mutuwa ce.
Ita ma 'Ƙaddarar Rayuwa' ta samu shiga zuciyar matasa, musamman 'yan mata, domin kuwa sun yi ta karakainar yin bidiyon wani ɓangare na waƙar, suna sakawa a soshiyal midiya.
An saka waƙar a cikin fim mai dogon zango na 'Labari Na' da ake nunawa a tashar talabijin ta Arewa 24.