Ƙirƙirarriyar basira za ta shafi kashi 40 na ayyukan yi a duniya, cewar IMF

AI

Asalin hoton, GETTY IMAGES

    • Marubuci, Annabelle Liang
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar Kasuwanci

Ƙirƙirarriyar basira na shirin yin tasiri ga kusan kashi 40 na dukkan ayyukan yi, a cewar wata sabuwar nazari da Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya yi.

Manajar darakta a IMF, Kristalina Georgieva ta ce "a mafi yawan ɓangarori, mai yiwuwa ne ƙirƙirarriyar basira za ta janyo taɓarɓarewar harkokin daidaito tsakanin al'umma".

Kiristalina Georgieva ta ƙara da cewa kamata ya yi masu tsara manufofin gwamnati su yi ƙoƙarin shawo kan wannan "lamari mai tayar da hankali" don "hana ƙere-ƙere ƙara rura wutar rikici tsakanin jama'a",

Ƙarin bazuwar ƙirƙirarriyar basira ya sake sanya duniya cikin nazari kan alfanu da haɗurranta.

Asusun Lamuni na Duniya ya ce mai yiwuwa ne ƙirƙirarriyar basira zai shafi wani gagarumin kaso na ayyuka - waɗanda suka kai kashi 60 - a ƙasashe masu ci gaban tattalin arziƙi.

A rabin irin waɗannan wurare, ma'aikata za su iya sa ran samun amfani daga cakuɗa harkarsu da ƙirƙirarriyar basira, wadda za ta inganta ƙwazon ayyukansu.

A wasu lammuran kuwa, ƙirƙirarriyar basira za ta samu ƙwazon yin muhimman da a yanzu ɗan'adam ne yake yin su. Abin da zai rage buƙatar ƙwadago, kuma zai shafi biyan albashi kai har ma zai iya shafe ayyuka.

A lokaci guda kuma, IMF ya yi hasashen cewa ƙere-ƙere za su shafi kashi 26 na ayyuka ne kawai a ƙasashe masu ƙarancin samun kuɗin shiga.

Nazarin ya ƙara ƙarfafa wani rahoto ne na cibiyar hada-hadar kuɗi ta Goldman Sachs a 2023 wanda ya yi ƙiyasin cewa ƙirƙirarriyar basira na iya maye gurbin abin da ya daidai da cikakkun ayyuka miliyan 300 - amma ya ce akwai yiwuwar samun sabbin ayyuka tare da samun bunƙasar ƙwazon aiki.

Misis Georgieva ta ce "da yawan waɗannan ƙasashe ba su da ababen more rayuwa ko ƙwararrun ma'aikata don cin moriyar amfanin ƙirƙirarriyar basira, abin da ya bijiro da hatsarin cewa nan da wani lokaci ƙere-ƙeren da na iya sanya ƙazancewar rashin daidaito tsakanin ƙasashe".

Ƙarin wani abu mai girma shi ne, matasan ma'aikata masu karɓar babban albashi na iya samun wani ƙari da ya zarce na saura a albashin da suke ɗauka bayan sun rungumi fasahar ƙirƙirarriyar basira.

Tsofaffin ma'aikata da kuma masu ƙaramin samu na iya fuskantar koma-baya, kamar yadda IMF ta yi imani.

"Muhimmin abu ne ga ƙasashe su ɓullo da babban tsarin ba da tallafi ga iyalai masu rauni da kuma sake horas da ma'aikatan da ke cikin kasada," a cewar Kiristalina Georgieva. "Ta hanyar yin wannan, muna iya shigo da kowa cikin tsarin canza harkoki zuwa na ƙirƙirarriyar basira, don kare rayuka da shawo kan rashin daidaito."

Nazarin Asusun Lamuni na Duniya na zuwa ne daidai lokacin da shugabannin duniya da na kasuwanci suka haɗu a Taron Tattalin Arziƙi na Duniya a birnin Davos na ƙasar Switzerland.

Ƙirƙirarriyar Basira wani batu ne da ake tattaunawa a kansa, bayan shaharar da manhajoji kamar ChatGPT ko Kwazai ta yi.