Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Ƙarin farashin mai da halaka Uban ƙasar Kanya a Kebbi
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi
A cikin makon da ke sallama ne ƴan Najeriya suka wayi gari da sabon farashin litar mai, lamarin da ya zo wa mutane da dama da bazata.
Zagayen da wakilin BBC Aminu Kutama ya yi zuwa wasu gidajen mai mallakar kamfanin mai na Najeriya, NNPCL a Abuja ya nuna yadda ake sayar da man a kan sabon farashi na Naira 1,030 kowacce lita saɓanin yadda ake sayar da shi a baya kan Naira 897 kowacce lita.
Ƙarin na kimanin kaso 15, shi ne na biyu a tsawon wata guda.
Wannan dai na zuwa ne bayan bayanan da suka nuna kamfanin na NNPCL ya zare hannunsa daga dillancin man kamfanin Ɗangote, wani abu da ya nuna cewa akwai yiwuwar farashin man ya ƙara tashi.
Zare hannun NNPCL daga dillanci dai na nufin kamfanin ya daina cikasa giɓin da ake samu ko kuma tallafi na naira 133.
Ku tuba ko mu aika ku lahira - Matawalle ga masu ba ƴanbindiga bayanai
A cikin makon ne dai ƙaramin ministan tsaro, Alhaji Bello Matawalle ya yi gargaɗi ga masu ba ƴanbindiga bayanai da su tuba, ko kuma su aika su lahira.
Matawalle ya yi wannan bayanin ne a ƙauyen Gundume da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni na jihar Sokoto a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin da sojojin ke yi a ranar Alhamis kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ministan ya ce, "wannan ƙauyen a da cike yake da mutane, inda ake gudanar da hada-hada sosai. Ina tabbatar muku cewa za a samu zaman lafiya. Za mu kafa sansanin soji a nan.
"Amma kuma dole ku ji tsoron Allah. Masu ba ƴanbindiga bayanai a kan jami'an tsaro da zirga-zirgar mutane su daina. Ko dai ku daina, ko mu aika ku lahira," in ji shi.
Tun farko kuma a ranar Laraba a wajen ƙaddamar da aikin soji na "Fansan Yamma", ministan ya yi kira da a ba jami'an tsaro haɗin kai domin samar da zaman lafiya a yankin.
Atiku ya caccaki Tinubu kan ƙarin farashin man fetur
Duk dai a cikin makon ne tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya caccaki shugaban Najeriya, Bola Tinubu kan abin da ya kira gazawarsa wajen tafiyar da sha'anin makamashi.
Atiku Abubakar wanda ya yi takara da Tinubu a zaɓen 2023, ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis cewa gwamnatin Tinubu ta lalata al'amura da sunan cire tallafin mai.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya danganta matsalolin da ƴan Najeriya ke fuskanta da irin tsarin gwamnatin Tinubu na "ta ci barkatai" kan yadda take tafiyar da sha'anin makamashi.
Atiku ya kuma bayyana damuwa kan ƙamarin da hauhawar farashi ya yi a ƙasar inda ya ce al'amarin na matuƙar ƙuntata wa ƴan Najeriya.
Yadda ƴan bindiga suka halaka Uban ƙasar Kanya a Kebbi
Al'ummar masarautar Zuru a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, na ci gaba da alhini, bayan mummunan kisan gillar da ƴan fashin daji suka yi wa Uban ƙasar Kanya, Alhaji Isah Daya, a yunƙurin kuɓutar da shi da jami'an tsaro suka yi.
Rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da ceto mutum takwas a ranar Talatar da ta gabata a wani sumame da aka ƙaddamar da nufin ceto mutanen ciki har da marigayi uban ƙasar.
Ƴan bindigar dai sun kai hari ne garin Kanya da ke ƙaramar hukumar Danko-Wassagu ta Jihar Kebbin inda suka yi awon gaba da marigayin a daren Asabar zuwa safiyar Lahadin da ta gabata.
Babban ɗan marigayin Bilal Isah ya shaida wa BBC Hausa cewa mahaifinsa ya rasu ne a lokacin da jami'an tsaro suka shiga daji don ganin sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su tare da mahaifinsa, wanda kuma a nan ne ya gamu da ajalinsa.
Gwamnatin jihar Gombe za ta fara biyan mafi ƙanƙantar albashin N70,000
Gwamnatin jihar Gombe a arewacin Najeriya ta ce a watan nan na Oktoba za ta fara biyan ma'aikatanta sabon mafi ƙanƙantar albahi na naira 70,000.
Mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamatin shiga tsakani kan mafi ƙanƙantar albashi, Manesseh Daniel Jatau, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai ranar Alhamis bayan ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago.
Jaridar Daily Trust ta rawaito Jatau na cewa tuni gwamnatin Gombe ta shirya domin tabbatar da fara biyan albashin, amma suna jiran kwamatin da aka kafa domin fitar da tsarin ya kammala aikinsa cikin kwanaki masu zuwa.
Batun biyan ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu mafi ƙanƙantar albashi na naira 70,000, na ci gaba da janyo muhawara a Najeriya, inda wasu jihohin ke cewa ba za su iya biya ba.
A ɓangare guda kuma, yayin da gwamnatin Najeriyar ta amince da ƙarin mafi ƙanƙantar albashin, sai kuma aka yi ƙarin kuɗin man fetur sau biyu cikin wata ɗaya, lamarin da ya ƙara dasa fargabar tashin farashin kayayyaki a zukatan ƴan Najeriya.