Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sabon farashin litar mai a gidajen man NNPCL ya koma N1,030 a Abuja
Zagayen da wakilin BBC Aminu Kutama ya yi zuwa wasu gidajen mai mallakar kamfanin mai na Najeriya, NNPCL a Abuja ya nuna yadda ake sayar da man a kan sabon farashi na naira 1,030 kowacce lita saɓanin yadda ake sayar da shi a baya naira 897 kowacce lita.
Ƙarin na kimanin kaso 15, shi ne na biyu a tsawon wata guda.
Wannan dai na zuwa ne bayan bayanan da suka nuna kamfanin na NNPCL ya zare hannunsa daga dillancin man kamfanin Ɗangote, wani abu da ya nuna cewa akwai yiwuwar farashin man ya ƙara tashi.
Zare hannun NNPCL daga dillanci dai na nufin kamfanin ya daina cikasa giɓin da ake samu ko kuma tallafi na naira 133.
Wakilin BBC, Aminu Kutama ya ce daga zagayen da ya yi a Abuja cewa ana sayar da man a wasu gidajen man ƴankasuwa daga naira 1,040 zuwa sama.
Me ya sa NNPCL ya zare hannunsa daga dillanci?
Wata majiya daga NNPCL ta tabbatar wa BBC cewa kamfanin ya zare hannunsa a matsayin mai shiga tsakanin 'yankasuwa da Dangote sakamakon yadda Ɗangote yake musu kallon yunƙurin hana shi ruwa gudu.
"Gaskiya dole ce ta sa za mu janye hannunmu domin yana yi mana kallon za mu hana shi cimma abin da yake son cimma. To gaskiya mu mun zare hannunmu yadda za mu bar ƴan kasuwa su yi mu'amala da shi kai tsaye." In ji wata majiya a NNPCL.
An dai ƙulla yarjejeniyar tsakanin kamfanonin biyu wadda ta ƙunshi cewa NNPCL ne kaɗai zai dinga sayen man Dangote, inda su kuma 'yankasuwa za su saya a hannun kamfanin.
Masana harkokin man fetur sun ce an yi hakan ne da zimmar daidaita farashi, abin da ake fargabar a yanzu ba zai yiwu ba da zarar 'yankasuwa sun fara sayen man kai-tsaye daga matatar Dangote.
A watan Satumba ne NNPCL ya ƙara farashin litar man daga N617 zuwa N897 tun kafin ya fara sayen man daga Dangote, yana mai cewa yana fama da ƙarancin kuɗi.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kare matakin da wanda "ya zama dole saboda a samu kuɗaɗen gina ƙasa", kodayake ya amince cewa hakan na jawo tsadar rayuwa ta hanyar hauhawar farashi.
Rahotanni sun nuna cewa tuni NNPCL ya sanar da gwamnatin Najeriya cewa ba zai samu damar biyan wasu haraje-haraje ba saboda kuɗin da yake kashewa wajen sauƙaƙa farashin man ga 'yan ƙasa - wato tallafin mai a taƙaice.
A madadin haka, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta amince wa kamfanin ya yi amfani da kason da ya kamata a ba ta na ribar da aka samu wajen sayar da man a rabin farashinsa da NNPCL ɗin ya kamata ya sayar wa 'yan ƙasa.