Me ya rage wa Kamala Harris bayan shan kaye a zaɓen Amurka?

    • Marubuci, Courtney Subramanian
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Washington DC
  • Lokacin karatu: Minti 6

Kimanin wata biyu kenan bayan shan kaye a hannun Donald Trump, Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris za ta jagoranci tabbatar da shan kayenta.

A matsayinta na Shugabar Majalisar Dattawan Amurka, a ranar Litinin za ta tsaya a gaban teburin kakakin majalisar wakilan ƙasar, domin jagorantar ƙidaya ƙuri'un wakilan masu zaɓe, wanda a hukumance zai tabbatar da nasarar abokin mahayyarta mako biyu gabanin rantsar da shi.

Lamarin na da ciwo, musamman gareta , wadda ta sha sukar abokin hamayyar tata a matsayin barazana ga dimokraɗiyyar Amurka, to sai dai hadimanta sun dage cewa za ta aiwatar da akinta kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ta ɗora mata.

Ba wannan ne karon farko da ɗan takarar da ya sha kaye ke jagorantar ƙidaya ƙuri'un wakilan masu zaɓe a gaban majalisun dokokin ƙasar ba, Al Gore ya yi haka a 2001, yayin da Richard Nixon ya fara yi a 1961.

Harris da tawagarta a yanzu tattaunawa kan mataki na gaba, inda suke nazarin shawarwari daban-daban, ciki har da batun sake tsayawa takara a 2028, ko kuma tsayawa takarar gwamnan a jiharta ta Califonia.

Yayin da 'yan takarar Democrats da suka sha kaye a baya-bayan nan, Al Gore da John Kerry da kuma Hillary Clinton suka ɗauki matakin sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar, hadiman Harris da manyan abokanta da masu ɗaukar nauyin yaƙin neman zaɓenta, na ganin cewa irin gagarumin goyon bayan da ta samu a zaɓen ka iya ba ta ƙwarin gwiwar sake tsayawa takarar.

Sun buga misali da Donald Trump – tsoho kuma sabon shugaban ƙasar na gaba, wanda ya lashe zaɓe a 2016 da 2024, duk da shan kaye da ya yi a 2020.

Ita kanta Harris ta ce ba za ta yi gaggawar ɗaukar mataki ba, inda ta faɗa wa mashawartanta da magoya bayanta cewa za ta yi nazarin duka shawarwarin da aka ba ta bayan rantsar da sabuwar gwamnati ranar 20 ga watan Janairu.

"Tana da matakin da ya kamata ta ɗauka, kuma ba za ka bayyana shi ba matsawar kana kan muƙamin da ya rage ka ƙarasa, saboda har yanzu tana kan mulki har zuwa ranar 20 ga watan Janairu," in ji Donna Brazile, wani makusanci Harris da ke cikin masu ba ta shawara a yaƙin neman zaɓenta.

To sai dai tambayar da ke ci gaba da yin kara-kaina dangane da yiwuwar tsayawarta takara a 2028, ita ce ko za ka raba gari da Joe Biden – wani abu da ta kasa yi a lokacin yaƙin neman zaɓenta.

Manyan abokanta a jam'iyyar sun ce matakin neman sake tsayawa takara da Biden ya yi tun da farko duk kuwa da damuwar da aka nuna game da shekarunsa, sannan ya janye daga takarar 'yan watanni kafin zaɓen, ya shafi takarar tata.

Duk da cewa Trump ya lashe duka jihohin nan bakwai masara tabbas da ake yi wa laƙabi da 'Swing States', da kuma kasancewar ɗan takarar Republican na farko cikin shekara 20 da ya samu mafi rinjayen ƙuri'un masu zaɓe - tazarar da ya ba ta ba mai yawa ba ce, bayan da Harris ta samu ƙuri'ar masu zaɓe miliya 75, wani abu da magoya bayanta suke ce zai taimaka wajen sake gina jam'iyyar nan da shekara huɗu masu zuwa.

A ɗaya gefen kuma, makusantan Biden sun ce Harris ta sha kaye a wuraren da Biden ya lashe a 2020, wani abu da ya nuna raguwar goyon bayan baƙaƙen fata da 'yan latin.

"Mutanen sun manta da an yi zaɓen fitar da gwani na gaskiya a 2024, da ba za ta taɓa samun nasara ba. Kowa ya san hakan," in ji wani tsohon mashawarcin Biden.

Mashawarcin, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, saboda girman maganar a jam'iyyance ya yaba wa Harris saboda farfaɗo da jam'iyyar Demokrats da kuma taimaka wa manyan 'yan majalisar wakilai, amma ya ce yaƙin neman zaɓen Trump ya yi nasarar daƙile ta kan muhimman batutuwan da suka haɗa da tattalin arziki da batun kan iyaka.

Tawagar yaƙin neman zaɓen Trump sun yarda cewa Harris ta fi Biden zame musu barazana a manyan batutuwa, kamar tattalin arziki a wajen masu zaɓe.

Haka kuma babu shakka zaɓen fitar da gwanin jam'iyyar Democrats a 2028 zai zama fafatawa mai matuƙar tsauri, musamman yadda jam'iyyar ke da manyan ƙusoshi masu tasowa kamar gwamnar Michigan, Gretchen Whitmer da gwamnan Illinois, JB Pritzker da gwamnan California, Gavin Newsom, waɗanda dukansu ke zawarcin takarar.

Dan haka ne wasu ke ganin cewa Harris ka iya janye jikinta daga sabgar siyasa gaba ɗaya, domin mayar da hankalinta wajen gudanar da gidauniyarta ko kafa wata cibiyar siyasa a jamai'ar da ta kammala, wato Jami'ar Howard.

Tsohuwar mai shigar da ƙarar, ka iya zama sakatariyar harkokin wajen Amurka, ko babbar lauyar gwamnati a gwamnatin Democrats ta gaba. Kuma tana da zaɓi idan tana son rubuta littafi.

Yayin da take da duka waɗannan zaɓi, Harris ta shaida wa hadimanta cewa tana buƙatar ci gaba da ganinta a fagen siyasa a matsayin jagorar jam'iyyar.

A cikin kwanakin ƙarshe na gwamnatin Biden daHarris, tana shirin fara balaguro zuwa ƙasashen duniya, zuwa yankuna da dama, a cewar wata majiya da ta saba da tsare-tsaren, wanda ke nuna sha'awarta ta ci gaba da taka rawa a fagen duniya.

Ga Harris da tawagarta, makonni bayan shan kaye a zaɓe sun kasance masu haƙuri cikin baƙin ciki da ƙwarin gwiwa.

Bayan zaɓen, Harris da mijinta, Doug Emhoff, sun shafe mako guda a Hawaii tare da kaɗan cikin tawagawar hadimanta domin hutawa da kuma tattauna makomar siyasarta.

Mashawarta da abokanta sun ce za ta ci gaba da nazarin abubuwan da suka faru, sannan ta jira domin ganin kamun ludayin sabuwar gwamnati da za ta fara cikin watannan kafin ta ɗauki mataki na gaba.

Inda za ta kasance ɗaya daga cikin manyan masu sukar manufofin gwamnatin Trump.

Duk da cewa ba ta da wani tasirin tun bayan shan kayen, Harris ta nuna jajircewarta a wani taron ɗalibai a jami'ar Prince George da ke Maryland a watan Decembar da ya gabata.

"Gangamin ƙungiyoyn kare haƙƙin biladama da masu rajin kare mata da masu kare haƙƙin ma'aikata da ita kanta Amurkan ba za su kai matsayin da suke ba, idan mutane suna haƙura haƙkoƙinsu bayan hukuncin kotu da cin su da yaƙi ko faɗuwa a zaɓe'', in ji ta.

"Dole ne mu tsaya a yaƙin da muke yi'', kalaman da ta riƙa maimaitawa tun bayan samun nasarar sama Sanata a 2016.

Sai dai abin da kalaman nata ke nufi bai fito fili ba tukunna. Wasu masu ba da gudummawa da magoya bayanta da ke ''cikin yaƙin" na iya fassara kalaman nata da takarar gwamnan California a 2026, lokacin da gwamnan jihar barin gado, Gavin Newsom zai yi murabus kuma zai iya biyyana burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Zaman gwamnan jihar California - mai ƙarfin tattalin arziki ka iya jefa ta rikici kai tsaye da Trump, wanda ya sha sukar manufofin gwamnatin jihar kan manufofinta na tattalin arziki.

Mulkar babbar jihar irin California ba ƙaramin aiki ba ne, sai dai hakan zai kawo mata cikas ga burinta na tsayawa takara, domin za a rantsar da ita ne a matsayin gwamnan jihar, a daidai lokacin da ya kamata ta ƙaddamar takarar shugabancin ƙasa.

Waɗanda suka yi magana da Harris sun ce har yanzu ba ta yanke shawara game da takarar gwamna ba, wanda wasu abokanta suka bayyana a matsayin wani abu mai yiwuwa a gareta.

Ta taɓa riƙe muƙamin babbar lauyan California har sau uku, sannan ta zama 'yar majalisar dattawan.

To amma nasararta a gujerar gwamna zai ba ta wani matsayi a tarihi na zama mace ta farko baƙar fata da ta zama gwamna a Amurka.