Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Faransa ta gama kwashe mutanenta daga Nijar
Gwamnatin Faransa ta ce ta kammala aikin kwashe mutanenta da sauran 'yan ƙasashen waje su 1,079 daga Nijar, ƙasar da sojoji suka yi wa juyin mulki a makon jiya.
Ministan tsaron Faransa, Sebastien Lecornu ya wallafa a shafin Tuwita cewa Faransawa da 'yan ƙasashen waje da aka kwashe "yanzu suna cikin aminci".
Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ƙara da cewa adadin mutanen da ta kwashe ya ƙunshi Faransawa 577.
Faransa tun da farko ta ce ƙiyasin mutum 600 ne Faransawa ke zaune dindindin a Nijar a lokacin da aka yi juyin mulkin.
Rundunar sojin Faransa ta yi amfani da jiragen sama biyar wajen kwashe mutanen.
Faransa na da dakarun soji 1,500 a Nijar waɗanda ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Sahel.
Birtaniya ma ta tabbatar da kwaso rukunin wasu 'yan ƙasar daga Nijar a jiragen Faransa saboda juyin mulkin sojoji a ƙasar ta Afirka ta Yamma. Mataimakin firaminista Oliver Dowden ya ce 'yan Burtaniya 14 ne suka biyo jirgin Faransa ranar Laraba.
Ofishin kula da raya ƙasa, harkokin ƙasashen waje da na rainon Ingila ya ce jami'ansu suna ci gaba da kasancewa a Nijar don tallafa wa "wani ƙanƙanin adadi" na mutanen Burtaniya da ke can.
Ofishin ya ƙara da cewa damuwar tsaron da ake da ita, ta sanya ofishin jakadancin Birtaniya wajen ɗaukar matakin wucin gadi ta hanyar rage adadin ma'aikatansa.
Ƙasashen Turai da yawa sun sanar da kwashe mutanensu yayin da tunzuri ya ƙaru a babban birnin ƙasar da sauran birane.
Ita ma, Amurka ta sanar da shirinta na kwashe jami’an diflomasiyyarta daga Nijar bayan juyin mulkin makon jiya.
Tuni aka kwashe ɗaruruwan ‘yan ƙasashen wajen daga ƙasar.
A ranar Lahadi ne masu zanga-zanga suka kai wa ofishin jakadancin Faransa hari.
Jagoran juyin mulkin Abdourahamane Tchiani ya yi gargaɗi kan duk wani yunƙurin “katsalandan daga ciki ko wajen” ƙasar.
Wannan na zuwa ne lokacin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar ta Afirka ta Yamma, inda ƙungiyar Ecowas ta yi barazanar ɗaukar matakin soji matuƙar ba a saki Shugaba Bazoum ba zuwa nan da 6 ga watan Agusta.
Ecowas ta sanya wa Nijar takunkumai na tafiya da kuma na tattalin arziƙi.
Nijar wadda ke samar da makamashin yuraniyum kuma babbar hanya ce da ‘yan ci-rani ke bi zuwa Arewacin Afirka da kuma tekun Meditereniya.
Kakakin ma’aikatar cikin gidan Amurka, Matthew Miller ya ce, duk da kwashe wasu ma’aikatan da za su yi amma ofishin jakadancin da ke Yamai zai ci gaba da kasancewa a buɗe.
“Mun damu da halin da mutanen Nijar ke ciki da kuma alaƙarmu da su, kuma muna tattaunawa ta fuskar diflomasiyya a matakai daban-daban,” in ji Miller.
Amurka ce ta fi bai wa Nijar agaji da kuma taimako kan sha'anin tsaro, kuma a baya ta yi gargaɗin cewa juyin mulkin zai iya janyo dakatar da ayyukan haɗin gwiwar da suke yi.
Faransa wadda ta yi wa Nijar mulkin mallaka da Tarayyar Turai duka sun sanar da janye tallafin kui da kuma kayayyakin ci gaba da suke bai wa Nijar.
Ecowas ma ta sanya mata takunkumi kan hulɗar kasuwanci tare da kullen dukiyar ƙasar a babban bankin yankin.
A wani bayani ta gidan talbijin ranar Laraba, Janar Tchiani ya ce sabuwar gwamnatinsu ta yi watsi da "waɗannan takunkumai, kuma ba za su yi mana barazana daga ko ina suka fito”.
Ya bayyana waɗannan takunkumai a matsayin “na son rai da rashin adalci” waɗanda aka ƙaƙaba wa Njar da nufin a wulaƙanta dakarun tsaron ƙasar kawai, da mayar da ƙasar maras gwamnati.
Manyan hafsoshin tsaron Ecowas sun haɗu a Najeriya tun ranar Laraba domin tattaunawa a kan yadda za a ɗauki matakan soji, ko da yake sun ce irin wannan matakin sai "tura ta kai bango".
Janar Tchiani jagoran masu tsaron fadar shugaban Nijar, ya ƙwace iko ne a ranar 26 ga watan Yuli, inda ya ce yana son kakkaɓe duk wasu bara-gurbi a Nijar.
Juyin mulkin ya haifar da gagarumar zanga-zangar ƙin jinin Faransa, wadda wasu 'yan ƙasar ke da burin ganin an musanya ta da Rasha, ƙasar da tasirinta a yankin Afrika ke ƙaruwa cikin ‘yan shekarun nan.
A ranar Lahadi ɗaruruwan masu zanga-zanga suka taru a kofar ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai, inda cikin sowa wasu ke cewa "Allah ja zamanin Rasha”, yayin da wasu ke cewa “Allah ja da ran Putin”. Wasu kuwa na kiran a “kori Faransa”.
Daga nan, sun cinna wuta a jikin ƙofar ginin ofishin jakadancin.
Ƙasashen Turai dai tuni suka kwashe mutanensu ƙarƙashin jagorancin Faransa.
Italiya ma ta kwashe ‘yan ƙasarta 87, kuma tuni suka isa birnin Rome.
Cikin wani jawabi da ya yi, Janar Tchiani ya ce mutanen Faransa a Nijar ba su “taɓa zama wata barazana ba”.
Nijar wadda ke da sansanin sojin Faransa da na Amurka, ana mata kallon babbar ƙawar Ƙasashen Yamma a yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.
Bayan da shugabanin sojin da suka yi juyin mulki a Mali mai maƙwabtaka kuma suka sanar da shiga ayyukan haɗin gwiwa da sojojin haya na Wagner da ke aiki da Rasha a 2021, Faransa ta tattara nata-ya-nata ta koma Nijar.