Ƙayatattun hotuna daga faɗin duniya na 2023

Mutum sama da miliyan ɗaya ne suka gudanar da zanga-zangar yaƙi da ƙudirin mayar da shekarun ritaya daga aiki zuwa 64 daga 62 a Faransa. Kimanin mutum 80,000 ne suka yi macin a birnin Paris, yayin da aka hau tituna asauran biranen ƙasar kusan 200.

Asalin hoton, YOAN VALAT/EPA

Bayanan hoto, Mutum sama da miliyan ɗaya ne suka gudanar da zanga-zangar yaƙi da ƙudirin mayar da shekarun ritaya daga aiki zuwa 64 daga 62 a Faransa. Kimanin mutum 80,000 ne suka yi macin a birnin Paris, yayin da aka hau tituna asauran biranen ƙasar kusan 200.
Dubun dubatar mabiya ɗariƙar Katolika ne suka yi bankwana da gawar Fafaroma Benedict XVI a wurin da aka ajiye shi na Basilica da ke farfajiyar St. Peter's a Fadar Vatican. Ya mutu ne a jajiberin sabuwar shekara yana da shekara 95.

Asalin hoton, CHRISTOPHER FURLONG/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Dubun dubatar mabiya ɗariƙar Katolika ne suka yi bankwana da gawar Fafaroma Benedict XVI a wurin da aka ajiye shi na Basilica da ke farfajiyar St. Peter's a Fadar Vatican. Ya mutu ne a jajiberin sabuwar shekara yana da shekara 95.
A woman walks alone among destroyed buildings in Hatay. Girgizar ƙasa ta kashe dubban Turkawa tare da raunata wasu da yawa bayan ta afka wa kudu maso gabashin ƙasar da ke iyaka da Syria a watan Fabrairu.

Asalin hoton, CHRIS MCGRATH/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Girgizar ƙasa ta kashe dubban Turkawa tare da raunata wasu da yawa bayan ta afka wa kudu maso gabashin ƙasar da ke iyaka da Syria a watan Fabrairu. Nan, wata mata ce ke wucewa ta gaban wasu gine-gine da suka lalace a yankin Hatay.
Mutum sama da 750 ne suka rasa muhallansu sakamakon zaftarewar ƙasa, yayin da wasu 40 suka mutu a kusa da birnin Sao Paulo na Brazil.

Asalin hoton, AMANDA PEROBELLI/REUTERS

Bayanan hoto, Mutum sama da 750 ne suka rasa muhallansu sakamakon zaftarewar ƙasa, yayin da wasu 40 suka mutu a kusa da birnin Sao Paulo na Brazil.
Michelle Yeoh ta zama 'yar nahiyar Asiya ta farko da ta lashe kyautar 'yar fim mafi hazaƙa yayin da fim ɗinta na Everything Everywhere All at Once ya mamaye bikin Oscars. Fim ɗin ya lashe kyautuka bakwai.

Asalin hoton, JEFF KRAVITZ/FILMMAGIC/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Michelle Yeoh ta zama 'yar nahiyar Asiya ta farko da ta lashe kyautar 'yar fim mafi hazaƙa yayin da fim ɗinta na Everything Everywhere All at Once ya mamaye bikin Oscars. Fim ɗin ya lashe kyautuka bakwai.
Lyubov Vasilivna mai shekara 71 ke nan take bayani game da dalilin da ya sa ta ƙi barin gidanta a ƙauyen Semenivka da ke yankin Donetsk na Ukraine. Tun daga lokacin da Rasha ta ƙaddamar da mamaya a Ukraine a Fabrairun 2022, ɓangarorin biyu ke zargin juna da karya dokokin yaƙi.

Asalin hoton, VIOLETA SANTOS MOURA/REUTERS

Bayanan hoto, Lyubov Vasilivna mai shekara 71 ke nan take bayani game da dalilin da ya sa ta ƙi barin gidanta a ƙauyen Semenivka da ke yankin Donetsk na Ukraine. Tun daga lokacin da Rasha ta ƙaddamar da mamaya a Ukraine a Fabrairun 2022, ɓangarorin biyu ke zargin juna da karya dokokin yaƙi.
Gobara na ci ganga-ganga a wajen unguwar Appa Pada da ke birnin Mumbai na Indiya. Gidaje sama da 1,000 ne suka lalace a gobrar.

Asalin hoton, DIVYAKANT SOLANKI/EPA

Bayanan hoto, Gobara na ci ganga-ganga a wajen unguwar Appa Pada da ke birnin Mumbai na Indiya. Gidaje sama da 1,000 ne suka lalace a gobrar.
Trump

Asalin hoton, CHANDAN KHANNA/AFP

Bayanan hoto, Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump na barin wani taron manema labarai a gidansa da ke Mar-a-Lago a Palm Beach na Florida, bayan ya bayyana a gaban kotu kan zargin rashawa. Trump ya musanta tuhuma 34 da aka gabatar masa game da yin ƙarya a takardun kasuwancinsa.
Dubban magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli ne suka nuna farin cikinsu a birnin Naples bayan sun lashe kofin gasar Serie A karon farko cikin shekara 33.

Asalin hoton, GUGLIELMO MANGIAPANE/REUTERS

Bayanan hoto, Dubban magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli ne suka nuna farin cikinsu a birnin Naples bayan sun lashe kofin gasar Serie A karon farko cikin shekara 33.
Sarki Charles III da Sarauniya Camilla na tsaye a barandar Fadar Buckingham bayan bikin naɗinsu. Charles ya zama sarki a ranar 8 ga watan Satumban 2022 bayan mutuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.

Asalin hoton, P VAN KATWIJK/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Sarki Charles III da Sarauniya Camilla na tsaye a barandar Fadar Buckingham bayan bikin naɗinsu. Charles ya zama sarki a ranar 8 ga watan Satumban 2022 bayan mutuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.
Sojojin Sama na Colombia suna lura da wani jariri da ya tsira daga hatsarin jirgin sama. Yara huɗu ne suka ɓata bayan hatsarin na ranar 1 ga watan Mayu, amma an gano su a raye bayan kwana 40 a cikin daji bayan an jiyo koke-kokensu.

Asalin hoton, COLUMBIAN AIRFORCE/REUTERS

Bayanan hoto, Sojojin Sama na Colombia suna lura da wani jariri da ya tsira daga hatsarin jirgin sama. Yara huɗu ne suka ɓata bayan hatsarin na ranar 1 ga watan Mayu, amma an gano su a raye bayan kwana 40 a cikin daji bayan an jiyo koke-kokensu.
super moon, known as the Blue Moon, from a mountain in Mogan

Asalin hoton, BORJA SUAREZ/REUTERS

Bayanan hoto, Jonay Ravelo na zaune a kan dokinsa, Nivaria, yana kallon wata na musamman da ake kira da Blue Moons a Turance daga kan wani dutse a Mogan da ke kudancin Canaria, Sifaniya ranar 31 ga watan Agusta.
Baƙin-haure na jiran a ba su abinci bayan sun isa iyakar Amurka da Mexico yayin da suke jiran tantancewa a San Diego.

Asalin hoton, MIKE BLAKE/REUTERS

Bayanan hoto, Baƙin-haure na jiran a ba su abinci bayan sun isa iyakar Amurka da Mexico yayin da suke jiran tantancewa a San Diego.
Wasu 'yan Afghanistan ne suka taru a kan ɓaraguzai bayan girgizar ƙasar da ta auku a Herat. Girgizar ta faru sau biyu cikin kwana huɗu a yammacin ƙasar, inda ta kashe mutum akalla 1,300.

Asalin hoton, JAFAR MOSAVI/AFP

Bayanan hoto, Wasu 'yan Afghanistan ne suka taru a kan ɓaraguzai bayan girgizar ƙasar da ta auku a Herat. Girgizar ta faru sau biyu cikin kwana huɗu a yammacin ƙasar, inda ta kashe mutum akalla 1,300.
Hadas Kalderon mazauniyar Nir Oz na Isra'ila, wadda aka sace 'ya'yanta biyu, ta ɓarke da kuka lokacin da take kallon gidan mahaifiyarta da aka ƙona a harin da mayaƙan Hamas suka kai ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Asalin hoton, DAN KITWOOD/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Hadas Kalderon mazauniyar Nir Oz na Isra'ila, wadda aka sace 'ya'yanta biyu, ta ɓarke da kuka lokacin da take kallon gidan mahaifiyarta da aka ƙona a harin da mayaƙan Hamas suka kai ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Makamin garkuwa na Isra'ila mai suna Iron Dome ke nan lokacin da yake kakkaɓe makamai masu linzami da aka harba daga Zirin Gaza.

Asalin hoton, AMIR COHEN/REUTERS

Bayanan hoto, Makamin garkuwa na Isra'ila mai suna Iron Dome ke nan lokacin da yake kakkaɓe makamai masu linzami da aka harba daga Zirin Gaza.
Wata Bafalasɗiniya Inas Abu Maamar take rungume da gawar 'yar 'yar uwarta mai shekara biyar, Saly, wadda harin Isra'ila ya kashe a Asibitin Nasser da ke Khan Younis na Zirin Gaza.

Asalin hoton, MOHAMMED SALEM/REUTERS

Bayanan hoto, Wata Bafalasɗiniya Inas Abu Maamar take rungume da gawar 'yar 'yar uwarta mai shekara biyar, Saly, wadda harin Isra'ila ya kashe a Asibitin Nasser da ke Khan Younis na Zirin Gaza.
Icelandic town of Grindavik, hit by earthquakes

Asalin hoton, MARKO DJURICA/REUTERS

Bayanan hoto, Girgizar ƙasa ta haifar da wani babban rami a Grindavik na ƙasar Iceland. An kwashe dubban mutane saboda fargabar aman wutar dutse a yankin.
Hayaƙi na tasowa daga Villarrica, wanda ƙanƙara ta lulluɓe, a Pucon na ƙasar Chile saboda aman wutar dutse.

Asalin hoton, CRISTOBAL SAAVEDRA ESCOBAR/REUTERS

Bayanan hoto, Hayaƙi na tasowa daga Villarrica, wanda ƙanƙara ta lulluɓe, a Pucon na ƙasar Chile saboda aman wutar dutse.