Wace dokar zaɓe ake taƙaddama a kai kuma me ya sa aka ƙi amincewa da ita?

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar litinin ne ƙungiyoyin fararen hula da ƴan adawa da kuma na mata suka bazama kan titunan Abuja , babban birnin Najeriya domin nuna adawa da ƙin amincewa da - sashen da ya tilasta aika sakamakon zaɓe ta na'ura - da majalisar dattijan Najeriya ta yi.

Hakan na zuwa ne bayan da majalisar ta amince da yi wa dokar zaɓe ta 2022 garanbawul a makon da ya gabata.

Masu zanga-zangar sun ce muddin ana son kawo ƙarshen maguɗin zaɓe, to dole sai an aika sakamakon zaɓe ta na'ura zuwa rumbun tattara sakamakon zaɓe na iRev, wanda kuma hakan zai ƙara ƙarfafa wa al'umma gwiwa kan fitowa su kaɗa kuri'a.

Sashe na 60, ƙaramin sashe na 3 na dokar zaɓen Najeriya, ya bayyana cewa hukumar zaɓe ta aika sakamakon zaɓe ta na'ura.

Mutane da dama na ganin hukumomi na son yin rufa-rufa kan gyaran fuska da aka yi wa dokar zaɓe, kuma hakan zai iya shafar sahihancin zaɓuka da za a gudanar a ƙasar.

Yayin wani jawabi a Abuja ranar Asabar wajen ƙaddamar da wani littafi, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, ya ce ba a haramta tura sakamakon zaɓe ta na'ura ba, sai dai an cire wurin da aka ce tura sakamakon zaɓen "kai-tsaye".

Sai dai ƙungiyoyin fararen hula sun yi fatali da hakan, inda suka ce ba za ta saɓu ba.

A ɗaya gefen, a watan Disamba ne majalisar wakilan Najeriya ta amince da wasu gyare-gyare na wasu sassa na dokar zaɓen.

Ta ce ta yi gyaran fuskar ne domin ƙara wa hukumar zaɓe ta INEC ƙarfi da kuma cike giɓin da aka samu a zaɓukan ƙasar da suka wuce.

Yayin zaman majalisar, ta yi wa sashe na 3, 5 da kuma 6 gyare-gyare domi tafiya da tsarin zaɓuka da kuma dokoki.

Ɗaya daga cikin gyare-gyaren da majalisar wakilan ta yi shi ne cewa daga yanzu duk wasu ƙorafe-ƙorafen bayan zaɓe babbar kotun tarayya na jihohi ne ke da alhakin kula da su.

Ta ce an yi haka ne domin ƙauce wa masu shigar da ƙararrakinsu a wasu kotunan Abuja ko kuma na jihohi waɗanda ba su da hurumin sauraron su.

Ƙarƙashin garanbawul ɗin da majalisar ta amince da shi, akwai kuma gabatar da tsauraran hukunce-hukunce ga waɗanda aka samu da laifin tafka maguɗi, har ma da hukuncin zaman gidan yari na shekara biyar ga jami'in sanar da sakamakon zaɓe da ya sanar da sakamakon ƙarya.

Wane sashe ne ya janyo taƙaddamar?

Sashen dokar da ya janyo taƙaddamar shi ne wanda ta wajabta aika sakamakon zaɓe kai-tsaye ta na'ura bayan tattara shi a kowace rumfar zaɓe.

Tun da farko majalisar wakilan ƙasar ta amince da duka ƙudurorin dokar, ba tare da ware wani ba.

Kuma bisa tsarin dokar Najeriya, ƙudiri kan zama doka ne kawai idan duka majalisun dokokin ƙasar biyu suka amince da shi.

Sai dai a majalisar dattawan, sashen da ya buƙaci wajabta aika sakamako ta na'ura ya fuskanci turjiya.

Inda ƴanmajalisar suka kafa hujja da rashin samun intanet a wasu ƙauyukan ƙasar.

Me ake nufi da aika sakamako ta na'ura?

An kwashe gomman shekara ana zargin tafka magudi a zaɓukan Najeriya, musamman lokacin tattara sakamakon zaɓe.

A lokacin zaɓe galibi zaɓuka kan tafi yadda ya kamata a rumfunan zaɓe, to amma galibi matsalar kan taso ne idan aka bar rumfunan zaɓe aka tafi cibiyar tattara sakamako, haka ma cibiyar tattara sakamako kan zama wata matattarar maguɗi kamar yadda wasu ke zargi.

Domin magance wannan matsala, a zaɓen 2023 hukumar INEC ta gabatar da na'urorin fasahar zamani, kamar ta BVAS da ke tantance masu kaɗa ƙuri'a, da kuma buɗe shafin tattara sakamako da ake kira iReV.

Manufar hakan shi ne idan aka kammala tattara sakamakon zaɓen sai a aika shi cikin wannan shafi da kowa zai iya gani.

Aika sakamakon zaɓen ta na'ura zai bayar da dama a aika sakamakon zaɓen da aka tattara a kowace rumfa zuwa cikin wannan shafi, wanda kuma kowa zai iya gani daga ko'ina idan ya shiga shafin.

Ana ganin hakan zai rage matsalolin da ke tasowa a cibiyar tattara sakamakon zaɓe.

To sai dai babu wata dokar ƙasa da ta wajabta aiki da waɗannan na'urori ya sa amfani da su bai zama tilas ba, wannan matsala ta rashin wajibcin doka a kan na'urorin ya haifar da manyan matsaloli a zaɓukan 2023.

Ga mafi yawan ƴan Najeriya, matsalar fasaha da aka samu a zaɓukan baya, ko zaɓin amfani da su, ya zama wata alama ta gazawar tsarin zaɓukan ƙasar.

Masu suka na zargin cewa barin 'aika sakamakon zaɓe ta na'ura' a matsayin zaɓi, ya bai wa wasu ƴansiyasa damar samun ƙarfin iko maimakon masu zaɓe.

To sai dai masu goya wa majalisar baya sun kafa hujja da matsalolin tsaro da rashin kayan aiki da kuma rashin intanet a ƙauyuka a matsayin dalilin rashin wajabtar dokar

Majalisa ta kira taron gaggawa

Majalisar dattawan ta sanar da cewa za ta yi wani zama na gaggawa ranar Talata, 10 ga watan Fabrairun 2026.

A wata wasiƙa da akawun majalisar ya fitar, ya ce shugaban majalisar na umartar kowane ɗan majalisa ya hallara yayin wannan zama.

Babu dai wani bayani kan abin da za a tattauna a taron, sai dai ba zai rasa nasaba da batun rashin amincewa da aika sakamakon zaɓe ta na'ura ba da majalisar ta ki amincewa da shi.

Masu sharhi dai na cewa muddin ana son gudanar da zaɓuka cikin gaskiya, to amincewa da aika sakamako ta na'ura shi zai fi alfanu - hakan kuma zai sa a yaba wa ƙasar bisa ƙoƙarinta na ganin ɗorewar dimokraɗiyya.

Sai dai, a halin yanzu za a zuba ido don ganin yadda za ta kaya tsakanin majalisar dattawan da kuma masu zanga-zangar.