Yadda 'yantawayen M23 ke iko da muhimman ma'adanai da ake haɗa wayoyin salula da su

Asalin hoton, Hassan Lali / BBC
- Marubuci, Paul Njie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Rubaya
- Lokacin karatu: Minti 4
A kwanan nan mayaƙan M23 suka bai wa BBC damar shiga wata babbar mahaƙar ma'adanai a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo mai muhimmanci wajen harhaɗa wayar salula.
Dubban masu haƙa ne ke karakaina a wurin mai cike da ramuka.
Sukan fito da dutsen coltan mai daraja da ake amfanin da shi wajen harhaɗa na'urorin lantarki, sai su kai shi wajen wankewa da kuma tacewa da hannu.
"Akasari mukan samu ma'aikata 10,000 ko fiye da ke aiki a nan kullum," a cewar Patrice Musafiri, wanda ke kula da mahaƙar tun bayan da 'yantawayen suka ƙwace iko da ita.
Wuri ne mai sarƙaƙiya, sai da tawagarmu ta yi amfani da sandunan dogarawa saboda kada taɓo ya kayar da su.
"Lokacin da muke can cikin rami, zafi yana hauhawa sosai - haƙo dutsen ma abu ne mai wahala sosai...ga kuma sauran abubuwa," kamar yadda wani ma'aikaci Peter Osiasi ya faɗa wa BBC.
"Wani lokacin sai an huro mana iska mai sanyi cikin ramin domin mu iya ci gaba da aiki," a cewarsa.
"Rayuwata ta sauya. Haƙar ma'adanai ta taimaka min matuƙa."
Dutsen kan taimaka wa gungun 'yanbindiga daban-daban wajen samun kuɗi bayan kowannensu ya kame iko da shi, ciki har da sojoji.

Asalin hoton, Hassan Lali / BBC
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mun isa mahaƙar mai nisan kamar kilomita 10 da ke wajen garin Rubaya bayan kwanaki da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Amurka tsakanin Kongo da Rwanda da zimmar kawo ƙarshen yaƙin shekara da shekaru.
Abubuwan da suka haddasa rikicin na da sarƙaƙiyar wajen fahimta.
Akwai maganar ƙabilanci, inda rukunin 'yantawaye da yawa ke aiki a nan cikinsu har da 'yan Hutu da aka alaƙanta da kisan ƙare-dangi a Rwanda na 1994.
Dukkansu sun amince su ajiye makamansu a ranar 27 ga watan Yuni da kuma umartar mayaƙan da ɓangaroriin biyu ke mara wa baya.
Sai dai ƙungiyar M23 ba ta cikin yarjejeniyar. Akasarinsu 'yan Tutsi ne kuma su ne ke iko da yanki mai girma na Bukavo da filayen jirgin sama biyu. Ana yawan zargin Rwanda da mara wa M23 baya. Amma gwamnatin ƙasa ta sha musanta ba su kuɗi da makamai.
Alamu sun nuna Amurka ta shiga sasanta rikicin ne domin ta samu damar haƙar ma'adanai a Kongo, kodayake dai har yanzu ba a bayyana hakan a hukumance ba.

Asalin hoton, Hassan Lali / BBC
An ba mu damar shiga wurin na tsawon minti 45, inda a nan ne mai kula da wurin da M23 ta naɗa ya dinga yi mana bayanin irin aiikin da suka yi.
"Mun gyara abubuwa da yawa tun bayan zuwanmu," in ji Mista Musafiri.
"Muna da sashen kula da haƙowa da kuma lafiyar ma'aikata, kuma yakan sasanta rikici tsakanin ma'aikata. Idan rami ya zama mai haɗari sai a faɗa wa mutane bar wurin."

Asalin hoton, Hassan Lali / BBC
A watan Disamba, wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana yadda M23 ke samun dubban daloli duk wata daga harajin da take karɓa na haƙar coltan, kuma akasarinsa ana kai shi Rwanda ne - amma M23 da Rwanda sun musanta hakan.
Wa'adi na biyu na gwamnatin Shugaban Amurka Trump ya daidai da loakcin da M23 ta ƙwace akasarin Arewaci da Kudancin Kivu.
Mai sharhi kan al'amura Akramm Tumsifu ya ce Kongo ta yi amfani da ma'adananta wajen tattaunawa domin samun taimakon Amurka, wanda ta daɗe tana nema.
Saboda zaman lafiyar da aka samu, ya faɗa wa BBC cewa kamfanonin Amurka za su samu damar "zuba jari mai yawa" a fannin ma'adanan wanda a yanzu China ta mamaye.
Mai kula da mahaƙar ta Rubaya ya faɗa mana za su yi maraba da kuɗaɗen jari, amma waɗanda za su taimaka wajen inganta tattalin arzikin yankin za su karɓa.
"Kowane mai zuba jari daga ƙasar waje zai iya shigowa matuƙar dai zai kawo wa mutanenmu ci gaba ta hanyar inganta albashin masu haƙr ma'adanai," a cewar Mista Musafiri.
Duk da irin arzikin ma'adanai da ƙasar ke da shi, yankunan da ake haƙar ma'adanai ba su fiya samun kayayyakin more rayuwa ba.
Mista Tumsifu na ganin kasancewar Amurkawa a wurin zai iya zama wata katanga da za ta hana dawowar rikici.
Amma kuma babu tabbas game da ɓangaren da mai zuba jari zai yi hulɗa da shi idan ya kawo kuɗinsa ganin cewa har yanzu M23 ce ke iko ad gabashin ƙasar.
Wani shirin shiga tsakanin da ƙasar Qatar ke yi tsakanin 'yantawayen da gwamnatin Kongo zai iya samar da tabbaci a 'yan watanni masu zuwa.
M23 wadda ɗaya ce cikin gungun tawaye na Congo River Alliance, ta ce yarjejeniyar ta Amurka ba ta magance tushen matsalar ba. Tana cewa tana kare haƙƙin 'yan ƙabilar Tutsi marasa rinjaye a Kongo.











