Faransa ta amince da buƙatar janye sojojinta daga Burkina Faso

.

Asalin hoton, AFP

Faransa ta amince da buƙatar jagororin sojin Burkina Faso na janye dukkan sojojinta daga ƙasar.

Burkina Faso da ke fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi, ta ce tana son kare kanta.

Akwai sojojin Faransa guda 400 a Burkina Faso, waɗanda ke da wata ɗaya kafin su fice daga ƙasar.

A shekara da ta gabata, sojojin Faransa suka janye daga Mali, ƙasar da sojinta suka shafe kusan shekara takwas suna faɗa da masu iƙirarin jihadi.

Faransa dai ta ci gaba da kulla ƙawancen soji da ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka da ke Afirka ta Yamma, inda take taimakon da dama daga cikinsu yaki da masu iƙirarin jihadi waɗanda ke cin karensu ba babbaka a yankin karkashin wani shiri da aka yi wa laƙabi da Operation Barkhane.

Sai dai, zargin da ake yi musu na zuwa da niyyar ɗebe tattalin arzikin ƙasashen abu ne da wasu ke Alla-wadai da shi.

Dukkan ƙasashen Mali da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka na aiki da kungiyar sojojin hayan Rasha na Wagner a yanzu.

Burkina Faso ta musanta rahotanni da ke cewa za ta yi aiki da sojojin hayan Rasha wajen yakar masu iƙirarin jihadi, sai dai, wasu jami’ai daga kungiyar sun riga da sun shiga ƙasar, a cewar kamfanin dillancin labaran AFP.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Faransa, ya tabbatar da cewa gwamnatin Burkina Faso ta aike da buƙatar ganin sojojinta sun fice daga ƙasar.

"Za mu mutunta sharuɗan yarjejeniyar ta hanyar amincewa da buƙatar,’’ a cewar mai magana da yawun ma’aikatar ta wajen Faransa.

Burkina Faso ta ɗauki gomman shekaru tana fama da ayyukan ‘yan tada-ƙayar-baya wanda ya tilasta wa mutum kusan miliyan biyu barin gidajensu.

A baya-bayan nan, wasu da ake zargi masu ikirarin jihadi, sun yi garkuwa da wasu mata guda 60 waɗanda suka je daji neman itace a yankin arewacin ƙasar, sannan a farkon watan nan, an gano gawarwakin mutum 28 da aka harbe a garin Nouna da ke arewa maso yammacin ƙasar. Tuni aka sake matan.

Tun bayan da kaftin Ibrahim Traoré ya kwace iko da mulki a Burkina Faso a watan Satumba, an yi ta yaɗa jita-jitar cewa zai fara aiki da kungiyar sojin hayan Rasha waɗanda takwarorinsu na Ghana suka ce ‘‘abin damuwa ne’’.

Kaftin Traoré ya yi alkawarin sake kwashe iko da yankunan da ke hannun masu ikirarin jihadi da kuma gudanar da zaɓuka a watan Yulin 2024.