Mece ce ƙungiyar G20 kuma me shugabanninta ke tattaunawa?

Banners for the G20 summit in Bali, Indonesia

Asalin hoton, Getty Images

Shugabannin ƙasashe 20 mafi ƙarfin tatalin arziki ta G20 sun fara taronsu na shekara a birnin Bali na Indosiya ranar 15 ga Nuwamba.

Maƙasudin taron shi ne taimaka wa wajen farfaɗo da tattalin arzikinsu bayan annobar cutar korona, amma tashin hankalin da ake ciki a Ukraine ka iya kawo tsaiko ga tattaunawar.

Mece ce ƙungiyar G20?

Ƙungiyar G20, mai mambobi ashirin, ƙungiya ce ta ƙasashen da ke haɗuwa suna tattauna tsare-tsaren tattalin arzikin duniya.

A tsakaninsu, ƙasashen G20 ne suka mallaki kashi 85 cikin 100 na tattalin arzikin duniya da kuma kashi 75 cikin 100 na kasuwancin duniya. Suke da kashi biyu cikin uku na yawan al’ummar duniya.

Mambobin sun haɗa da ƙasashe 19 na ƙungiyar tarayyar Turai da Ajantina da Australiya da Brazil da Canada da China da Faransa da Jamus da Indiya da Indonesiya, Italiya da Japan da Mexico da Rasha da Saudiyya da Afirka ta Kudu da Koriya ta Kudu da Turkiyya da Birtaniya da kuma Amurka.

Ita kuwa Spaniya a ko yaushe a kan gayyace ta ne a matsayin baƙuwa.

Akwai kuma wata ƙaramar ƙungiyar mai mambobi bakwai mafiya girman masana’antu wato G7.

G20 a lambobi

Me ƙungiyar take tattaunawa a kai?

Battuwan da shugabannin G20 ke tattaunawa a kai sun haɗa da tattalin arziki da sauyin yanayi, makamashi mai ɗorewa, da yafe bashi ga ƙasashen duniya da kuma karɓar haraji daga manyan kamfanonin duniya.

A kowace shekara, wata mamba daga cikin ƙasashen G20 ce ke karɓar shugabancin taron tare da tsara jadawalin abin da za a tattauna a wajen taron.

A shekarar 2022 mai masaukin baƙin Indonesiya na son taron ya mayar da hankali a kan ɗaukar matakan lafiya da farfaɗo da tattalin arziki biyo bayan annobar cutar korona. Tana kuma so a bunƙasa tabbatar da amfani da makamashi mai ɗorewa.

Kazalika taron wata dama ce ga shugabannin ƙasashen tu gana da juna a wasu ƙananan taruka a wajen don tattaunawa.

Gabanin taron dai shugaban Amurka Joe Biden ya gana da shugaban China Xi Jinping don tattanawa wasu jerin batutuwa da suka haɗa da yaƙin Ukraine da kuma matsayar Taiwan.

Wa yake halartar taron?

Rikicin siyasa ka iya daƙile armashin taron.

Ma’aikatar harkokin wajen Ukraine ta nemi da a kori Rasha daga cikin ƙungiyar G20, sbaoda kutsen da ta yi a Ukraine.

Gwamnatin Indonesiya ta ce Shugaba Putin ba zai halarci taron ba.

Angela Merkel pictured with Emmanuel Macron and Donald Trump at the 2017 G20 meeting in Hamburg

Asalin hoton, Getty Images

Ana kuma tsammanin Shugaban Amurka Joe Biden ba zai gaisa da yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman ba.

Shugaba Biden ya zargi Saudiyya da taimaka wa Rasha wajen ba ta kuɗi don yaƙar Ukraine ya kuma ce ƙasashen biyu suna aiki tare don ƙara farashin ɗanyen man fetur.

Me ya sa shugabannin ke ɗaukar hoto tare?

Shugabannin ƙasashen yawanci sukan ɗauki hoto a tare.

Ana amfani da hakan a matsayin wata dama ta tallata duk wata yarjejeniya da shugabannin suka cimma – amma yawanci kafafen yaɗa labarai sun fi mayar da hankali kan rashin jitiwar diflomasiyya da hton ke bayyanawa.

A shekarar 2018, bayan kisan ɗan jarida Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santambul na Turkiyya, shugabannin ƙungiyar da dama sun yi biris da Yarima Mohammed bin Salman a wajen taron, inda suka tilasta masa tsayawa can nesa da su a cikin hoton da suka ɗauka tare.

Saudi Crown Prince Mohammed bin Salman looks out as leaders arrive for a family photo at the G20 in Buenos Aires

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, US president Joe Biden may refuse to meet Saudi Crown Prince Mohammed bin Salman at the summit

Ko G20 na yin nasara?

A wajen tarukan shugabannin a shekarun 2008 da 2009 a lokacin da ake cikin wani yanayi na taɓarɓarewar tattalin arziki, shugabannin sun amince da wasu matakai don ceto tsarin kuɗaɗe na duniya.

Amma tarukan da suka biyo baya ba su zama masu tsari sosai kamar haka ba, ana ganin hakan ya faru ne saboda sa-in-sar da ta ɓarke tsakanin manyan ƙasashen duniyar masu adawa da juna.

A wajen taron ministocin kuɗi da shugabannin manyan bankunan ƙasashen G20 na bana,ba a cimma wasu abubuwa masu yawa ba saboda musun da ya kaure tsakanin Rasha da ƙsashen yamma kan kutsen Ukraine.

Haka kuma, yawanci ƙsashe kan cimma yarjejeniya a wajen ganawar ɗaiɗaiku da sukan yi da juna a wajen taron.

A shekarar 2019 a birnin Osaka na Japan, shugaban Amurka na lokacin Donald Trump da na China Xi Jinping, sun yarda su koma teburin tattaunawa don sasantawa a kan wani gagarumin rikicin kasuwanci.

Riot police clash with protesters outside the G20 summit in Hamburg in 2017

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Riot police clash with protesters outside the G20 summit in Hamburg in 2017

Ko tarukan na jawo zanga-zanga?

Yawanci a kan gudanar da zanga-zanga a dalilin tarukan shugabannin.

Dubban masu zanga-zanga ne suka yi maci a birnin Buenos Aires na Ajantina a shekarar 2018 don nuna adawa da tsare-tsaren tattalin arziki na G20.

Masu adawa da tsarin jari hujja sun yi bore a wajen taron 2017 a Hamburg, kuma dubban masu zanga-zanga ne suka yi maci a wajen taron G20 a Rio de Janeiro a 2018 da kuma a Toronto a 2010.

A shekarar 2009 an kashe wani mai sayar da jarida Ian Tomlinson a kan hanyarsa ta zuwa gida bayan tashi daga wajen aiki a lokacin da zanga-zangar adawa da taron G20 ta rutsa da shi a London.

Cikakkun mambobin ƙungiyar G20: Ajantina da Australiya da Brazil da Canada da China da Faransa da Jamus da Indoya da Indonesiya da Italiya da Japan da Mexico da Rasha da Saudiyya da Afirka ta Kudu da Koriya ta Kudu da Turkiyya da Birtaniya da Amurka da kuma Ƙungiyar Tarayyar Turai.