Ƙasar da ta fi kowacce haɗari ga mata

Asalin hoton, BBC/ Phil Pendlebury
- Marubuci, By Nawal Al-Maghafi and Jasmin Dyer
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service, reporting from Port-au-Prince
- Lokacin karatu: Minti 6
Gargaɗi: Wannan labarin na ɗauke da bayanin fyaɗe da sauran laifuka da za su iya tayar wa masu karatu hankali.
Helene na da shekaru 17 lokacin da wasu gungun ƴan daba suka kai hari unguwarsu a babban birnin Haiti, Port-au-Prince.
Tana lallaba ƴarta, wadda take bacci, nda take bayanin yadda wasu mutane masu makamai suka yi garkuwa da ita yayin da take ƙoƙarin guduwa, kuma suka riƙe ta tsawon sama da watanni biyu.
"Sun yi min fyaɗe kuma sun buge ni kullum. Mutane da dama. Ban ma san sunayensu ba, suna rufe fuskarsu," a cewar matar mai ƙarancin shekaru, wadda muka canza sunanta don kare ta. "Wasu abubuwan da suka yi min na da ciwo sosai da ba zan iya faɗa muku ba."
"Na samu juna biyu, sun yi ta faɗa min cewa sai na zubar da cikin kuma sai na ce ʼaʼaʼ. Wannan jaririyar ka iya zama guda ɗaya da zan iya samu a rayuwarta."
Ta samu ta tsira yayin da ƴan daban suke faɗa don riƙe wuraren da suke da su a garin. Yanzu mai shekaru 19, ta kwashe tsawon shekara guda tana rainon ƴarta a wani ɓoyayyen gida da ke wajen birnin.
Gidan yana bai mata marasa shekaru da yawa mafaka, inda suke bacci a ƴan gadaje da ke ɗakuna masu fenti mai kyau.
Helene ce ta fi shekaru a wurin. Mafi ƙaranci tana da shekaru 12. Yayin da take wasa da rawa sanye da shuɗiyar riga, shekarunta ba su nuna a fuskarta ba, kuma ta yi fama da rashin abinci mai gina jiki a baya. Maʼaikatan wurin sun faɗa mana cewa an yi mata fyaɗe ba sau ɗaya ba.

Asalin hoton, BBC/ Phil Pendlebury
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Fyaɗe da cin zarafi na ƙaruwa a Haiti kuma ƴan daba na ƙara yaɗa ikonsu a Port-au-Prince da sauran wurare.
Kasar da ke Caribbean na fuskantar rikici kala kala tun bayan kisan tsohon Shugaban Kasa, Jovenel Moise.
Zai yi wahala a iya ƙiyasta girman cin zarafi. Kungiyar Medecins Sans Frontieres (MSF) na da wani asibiti a tsakiyar Port-au-Prince don matan da suka fuskanci cin zarafi. Alƙaluma da BBC ta samu sun nuna cewa gungun ƴan daba da dama na yi wa mata fyaɗe. Daga abubuwan da waɗanda aka ci wa zarafi suka faɗa, akwai shaidar cewa gungun ƴan daba na amfani da fyaɗe don razana alʼumma.
BBC ta nemi jin baʼasin gungun ƴan daban dangane kashe-kashe da fyaɗen. Wani ya faɗa mana cewa ba su da iko kan abubuwan da ƴan ƙungiyarsu suka yi. Wani kuma ya ce "idan muna faɗa hankalinmu ba ya jikinmu - mu ba mutane ba."
"Marasa lafiya sun fara ba da labarin yanayin da suka shiga mai matuƙar wahala tun daga 2021," a cewar Diana Manilla Arroyo, shugabar MSF a Haiti.
"Waɗanda suka tsira suna maganar maganar masu cin zarafi biyu ko huɗu har zuwa 20,", ta ƙara da cewa ana yi wa mata barazana da makami ko kuma a sumar da su yanzu.
Mata na kuma ƙara ba da rahoton cewa masu ci musu zarafi ba su kai shekaru 18 ba, ta ƙara da cewa.

Asalin hoton, BBC/ Phil Pendlebury
"An kai wa unguwarmu hari, na koma gida sai na tarar da an kashe mahaifiyata, da ƴar uwata, da mahaifina, duk an kashe su. Sun kashe su kuma suka ƙone gidan suna ciki", wata mata ta faɗa.
Bayan ta zagaye gidan da aka lalata, ta kusa barin unguwar kenan ta haɗu da ƴan dabar. "Sun yi min fyaɗe - Ina tare da yarinyata mai shekaru shida tare da ni. Ita ma suka yi mata fyaɗe," ta ƙara. "Sai kuma suka kashe ƙanina a gabanmu.'
"Duk lokacin da ƴata ta kalle ni, sai ranta ya baci ta fara kuka."
Wasu matan sun faɗi wasu hare-haren da ke kama da nata - kisa, fyaɗe da kuma ƙone-ƙone.
Cin zarafi ɗaya ne cikin rikice-rikicen da suka addabi Haiti. Majalisar Dinkin Duniya ta ce a ƙalla mutane miliyan 1.3 sun tsere daga gidajensu kuma rabin mutanen ƙasar na fama da yunwa.
Haiti ba ta da tsayayyar gwamnati tun bayan kisan Moise. An ɗora nauyin dawo da ƙasar kan turba a kan wata Majalisar Mulkin Kasa.
Kungiyoyin ƴan daba sun haɗa kai, kuma suna yaƙar gwamnatin Haiti, maimakon junansu.
Tun bayan da muka kai ziyara a Disamba, yanayin ya ƙara lalacewa. Dubun dubatar mutane sun rasa muhallansu. Sama da mutum 4,000 aka kashe a farkon shekarar 2025, idan aka haɗa da 5,400 a gaba ɗaya 2024, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Asalin hoton, Guerinault Louis/Anadolu/Getty Images
Ana ƙiyasin cewa ƴan daban sun ƙara ikon da suke da shi da babban birnin daga kaso 85% zuwa 90%, kuma sun karɓe iko da wurare masu muhimmanci duk da ƙoƙarin da sojojin MDD ke yi.
Mun bi wannan runduna yayin da suke sintiri a unguwar da ke ƙarƙashin ikon ƴan daba, kuma a ƙanƙanin lokaci aka harbi tayar ɗaya daga cikin motocin, daga nan aka haƙura da aikin.
Sojojin rundunar ba su fiya barin motocinsu masu sulke ba. Masana sun ce Yan daban na ƙara samun makamai masu ƙarfi na zamani.
A watannin bayan nan, hukumomi a Haiti sun nemi sojojin haya su taimaka musu.
Wata majiyar tsaro a Haiti ta faɗa wa BBC cewa kamfanonin tsaro, har da wani daga Amurka na aiki a ƙasar kuma suna amfani da jirage marasa matuƙa don kai hari kan shugabannin ƴan daban.
Ya nuna mana bidiyon yadda aka kai wa wani shugaba, Ti Lapli hari. Ya ce Ti Lapli na cikin mawuyacin hali, sai dai BBC ba ta tabbatar da hakan ba.

Asalin hoton, BBC/ Phil Pendlebury
Amma a faɗin birnin, ana ci gaba da fargabar ƴan daban. A unguwanni da dama, ƴan sa kai sun ɗauki doka a hannunsu, lamarin da ya ƙara yawan matasa maza masu makamai a hannunsu.
"Ba za mu bar su [ƴan daban] su zo su kashe mu ba - ko su sace duk abin da muke da shi, su ƙona gidajenmu, kashe yaranmu,ʼ wani mutu mai suna "Mike" ya faɗa.
Yana jagorantar wani gungun ƴan sa kai a Croix-des-Pres, wata kasuwa da ke kusa da inda ƴan daba ke da iko da shi.
Yayin da ake harbe-harbe, mutane ba sa motsawa. Sun saba da jin harbin bindiga.
Ya ce ƴan daban na biyan ƙananan yara don su bi su, kuma suna kafa shingaye inda suke karɓar kuɗi wurin mutane.
"Tabbas kowa na tsoro," ya faɗa mana. ʼMuna jin mu kaɗai ne a ƙokarin kare mata da yara. Yayin da ƴan daban ke yaɗuwa, mun san wurinmu ne na gaba."

Asalin hoton, BBC/ Phil Pendlebury
Kungiyoyin ba da agaji sun ce yanayin na taɓarɓarewa kuma mata na cikin waɗanda ya fi shafa, yayin da da yawansu ke fuskantar cin zarafi da rasa muhalli.
Lola Castro, shugabar yankin ta Shirin samar da abinci da Majalisar Dinkin Duniya ta ce Port-au-Prince ne "wuri mafi hatsari da za ki iya kasancewa mace a duniya."
Mata a nan kuma za su cutu sakamakon zaftare tallafi da ake yi, ta ƙara.
Haiti ta kasance cikin mafi samun tallafi daga USAID, wadda Shugaba Donald Trump ya zaftare, lamarin da ya kira "asara".
Lokacin da muka kai ziyara a Yuni, Ms. Castro ta ce WFP na raba abinci na ƙarshe da suka samu daga Amurka.
Samar da abinci na kare mata, ta yi bayani, saboda yana kare su daga bara a titi ko neman abincin.
Maʼaikatan agaji na kuma fargabar cewa zaftare-zaftaren ka iya shafar gidaje kamar inda Helen take zama.
Helene da sauran mata da ke gidan kan zauna su yi hira tare suna kallon garin Port-au-Prince, amma da yawansu na tsoron barin gidan.
Ba ta san yadda za ta taimaki ƴarta yayin da take girma ba.
"Na yi burin zuwa makaranta, na koyi wani abu don amfanin kaina," ta ƙara. "Na san cewa zan samu haihuwa, amma ba da wannan yarintar ba."







