Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda gobara ta kashe almajirai 17 a Zamfara
A garin Ƙauran Namoda da ke jihar Zamfara, an yi jana'izar almajirai 17 waɗanda suka rasu sanadiyyar wata gobara.
Gobarar wadda ta tashi da daddare a ranar Talata a wata makarantar allo da ke garin ta cinye ilahirin gidan almajiran.
Haka nan gobarar ta yi raunata mutane da dama wadanda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.
Daya daga cikin mutanen da suka shaida yadda lamarin ya faru, Yahaya Mahi ya ce gobarar ta fara ne daga wani gida da ke maƙwaftaka da makarantar almajiran kafin daga baya ta yaɗu zuwa inda suke.
"Da farko an kashe ta, har mutane sun watse sai kuma gobarar ta sake tashi, ta tashi ne a daidai ƙofar inda almajiran suke, wannan ya sanya ta tare ƙofar da za su iya fita," in ji Mahi.
Ya ƙara da cewa "almajirai 17 suka rasa ransu, guda 12 kuma suka samu raunuka".
Ɗaya daga cikin iyayen da suka ransu a cikin lamarin ya shaida wa BBC cewa yanzu haka suna cikin jimami kan lamarin da ya faru.
"Mun bar wa Allah ikonsa, da muka ji lamarin ba mu ji daɗi ba, amma muna fatan Allah ya tsayar da abin haka."
Me ya haifar da gobarar?
Har yanzu babu tabbas kan ko mene ne ya haddasa gobarar sannan hukumomi ba su ce uffan ba kan batun.
Mazaunin yankin ya ce "gobarar ta tashi ne daga gidan maƙwafta, kuma ba mu san yadda aka yi ta taso a gidan maƙwaftan ba."
Karatun allo babban lamari ne a arewacin Najeriya, inda iyaye ke kai su garuruwa daban-daban domin neman ilimin addini.
Sai dai sau da yawa masana na yin ƙorafi kan irin rayuwar rayuwar da yaran kan tsinci kansu a ciki.
'Hukumomi za su ɗauki mataki'
Shugaban ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda, Madaru Muhammad Maidara ya nuna damuwa da faruwar lamarin sannan ya ce hukumomi za su sanya ido domin ganin an kawo gyara a tsarin karatun tsangaya.
"Wannan zai ƙara mana ƙwarin gwiwa wajen bin duk irin waɗannan makarantu domin tabbatar da cewa mu ga an rarraba ɗalibai ta yadda ba a samu cunkoso ba."