Hikayata 2025: Labarai 15 da suka ciri tuta

Asalin hoton, BBC VISUAL JOURNALISM
Bayan tacewa da tankaɗe da rairaya daga cikin labarai kimanin 500 da marubuta mata suka aikowa BBC, alƙalai sun samu nasarar fitar da labarai 15 da suka ce sun ciri tuta.
A cikin labaran 15, uku daga ciki ne suka kasance gwaraza wato gwarzuwa ta ɗaya da ta biyu da ta uku sai kuma sauran 12 da alaƙalan suka ce su ma sun cancanci yabo.
Wannan ne dai karo na 10 da BBC Hausa ke shirya wannan gasar ta rubutun mata zalla, tun bayan fara gasar a shekarar 2016.
Labarai 15
- Kawalwainiya - Hafsat Muhammad Sani
- Jana'izar Shahara - Aisha Mahmoud Shafii
- Ruɗin Zuciya - Hafsat Bature Muhammad
- Baɗi Ba Rai - Rasheeda S. Director
- Haske A Duhu - Hassana Zakariyya Usman
- Zaɓi Ɗaya - Ummi Abba Muhammad
- Shahara - Nafisa Auwal K/Goje
- Tsalle Ɗaya - Fadhila Lamiɗo
- Gobena - Jamila Lawal Zango
- Samarin Shaho - Hafsat Sani Tanko
- Sai Da Na Faɗi - Fareeda Abdullahi
- Ƙarshen Alewa - Maimuna Alewa
- Gobara Biyu - Maryam Ibrahim Liti
- Furen Juji - Fauziyya Sani Jibril
- Kunun Bayan Ludayi - Maimouna Sani
Tsarin gasar
Wata tawagar alƙalai waɗanda ba ma'aikatan BBC ba ne, bisa jagorancin ma'aikacin BBC suka zaɓi gwarzuwa ɗaya da labarinta ya yi nasarar yin na ɗaya sannan za su suka zaɓi ta biyu da ta uku da kuma sauran 12 da suka cancanci yabo.
Kafin tura wa alƙalan labaran don tantancewa an cire duk wani bayani dangane da mai shiga gasa kuma ba a aika masu kowane irin bayani kan masu shiga gasar ba.
Tawagar alƙalan ta zaɓi labarai 30 bayan tantancewa ta farko sannan daga bisani za a sake tantancewa aka fitar da guda 15, inda a tantancewa ta uku aka fitar da ta ɗaya da ta biyu da ta uku sai kuma 12 da suka cancanci yabo.
Waɗanda suka yi nasara za su samu kyautar kuɗi da lambar yabo: wannan ya ƙunshi N1,000,000 (nairan miliyan ɗaya) ga wadda ta zo ta ɗaya, N750,000 (naira dubu ɗari bakwai da hamsin) ga wadda ta zo ta biyu, N500,000 (naira dubu ɗari biyar) ga wadda ta zo ta uku.
BBC za ta watsa labarai 12 da alƙalan suka ce sun cancanci yabo da guda ukun da suka yi nasara a tasharta ta BBC Hausa.
Za a sanar da mutum ukun da suka zamo zakaru a yayin wani bikin karramawa a Abuja, babban birnin Najeriya, a ranar 11 ga watan Disamban 2025.











