Iran: Me dakatar da hulɗa da hukumar sa ido kan nukiliya ta duniya ke nufi?

    • Marubuci, BBC News Persian
  • Lokacin karatu: Minti 5

Majalisar dokoki ta Iran ya amince da wani ƙudiri da ke neman yanke hulda da hukumar kula da nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya saboda hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa tashoshinta.

Matakin zai ta'azzara rashin jituwa tsakanin Iran da hukumar ta International Atomic Energy Agency (IAEA) wanda kuma zai iya zama giɓi a ɓangaren sa ido kan shirin Iran na nukiliya.

Ƙudirin da aka amince da shi a ranar Laraba, zai hana sa ido, da ayyukan tattara bayanai, da kuma bayar da rahoto da ma'aikatan IAEA ke yi a Iran.

Duk da cewa sai majalisar shura ta Iran ta amince da ƙudirin kafin ya zama doka, hakan na ƙara fito da matsayin Iran game da shirinta na nukiliya.

Ɗanmajalisa Ebrahim Rezaei, mai magana da kwamatin majalisar, ya ce an ɗauki matakin ne da zimmar jaddada 'yancin Iran kan abin da ya kira "hukumar da aka siyasantar da ita".

Haka kuma, ƙudirin zai iya zama wata damar tattaunawa a hannun Iran, musamman yanzu da ake ganin ƙasashen Yamma na neman a ci gaba da tattaunawa tsakaninsu da ƙasar.

Me ya sa a yanzu?

Matakin ya biyo bayan yaƙin kwana 12 da Iran ta yi ne da Isra'ila, inda kuma Amurka ta kai wa tashoshin nukiliyar uku hare-hare da suka ƙunshi Fordo, da Natanz, da Isfahan.

Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami kan Isra'ila da kuma sansanin sojin Amurka na Qatar.

Ana kallon matakin majalisar a matsayin martani a siyasance kan hare-haren da kuma matakin IAEA na kwanan nan da ya zargi Iran da ƙin bin dokokin yarjejeniyarta.

Ta bayyana matsayar tata ne kwana ɗaya kafin Isra'ila ta fara kai wa Iran hare-hare, inda ta kashe wasu manyan janar-janar ɗinta.

Me IAEA ke yi a Iran?

IAEA ta taka rawa mai yawa wajen saka ido kan shirin nukiliyar Iran tsawon shekara 20.

A 2015, Iran ta amince da wata yarjejeniya kan shirin nata da rukunin ƙasashe shida - Amurka, Rasha, Faransa, Birtaniya, China, Jamus.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, Iran ta amince ta rage yawan makamashin Uranium da take ingantawa kuma ta bar masu saka ido su dinga dubawa, a madadin haka za a cire wa Iran ɗin takunkuman da aka ƙaƙaba mata.

A 2018, Donald Trump ya cire Amurka daga yarjejeniyar kuma ya sake ƙaƙaba wa Iran takunkuman da aka cire. Daga nan kuma Iran ta fara yin watsi da tanadin yarjejeniyar.

Sai ta fara ƙara yawan ingancin Uranium, ta rage wa masu sa ido damar duba ayyukan nata, har ma ta kashe wasu kyamarori na hukumar IAEA a tashoshin.

IAEA ta ci gaba da saka ido kaɗan ba tare da cikakken iko kamar a baya ba, kuma an yi hakan ne kawai saboda Iran na cikin yarjejeniyar ta Non-Proliferation Treaty (NPT).

Kafin rikicin na baya-bayan nan, masu sa ido na IAEA na Iran kuma lokaci na ƙarshe da suka saka ido kan makamashin mai nauyin 400kg an riga an inganta su zuwa kashi 60 cikin 100, wanda saura ƙiris su kai yawan wanda za a iya haɗa makamai da su.

A ranar 12 ga watan Yuni, majalisar ƙoli ta IAEA ta fitar da matsayinta tana sukar Iran da gazawa wajen bin ƙa'idojin yarjejeniyar NPT ta hanyar hana masu sa ido zuwa tashoshi, da ƙin bayyana yawan Uranium a wasu tashoshi da ta ɓoye.

Ƙasashe 19 daga cikin 35 da ke cikin majalaisar ƙoli ta IAEA - ciki har da Birtaniya da Faransa da Jamus - sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da matsayar. Sai kuma Rasha da China da Burkina Faso da suka ƙi amincewa.

Iran ta siffanta matsayar da cewa na siyasa ne, sai kuma kwana ɗaya bayan haka Isra'ila ta fara kai hare-hare.

Munafurci?

Ɗaya daga cikin damuwar Iran da IAEA ita ce nuna wariya.

Lokacin da dakarun Rasha suka mamaye tashar nukiliya ta Zaporizhzhia a Ukraine a 2022, shugaban IAEA rafael Grossi ya fitar da sanarwar gargaɗi yana zargin Rasha da "wasa da wuta".

Akasin haka, lokacin da Isra'ila ta kai wa tashar Iran hari, Grossi bai ambaci Isra'ila ko Amurka ba, kawai dai ya yi gargaɗi game da kai harin.

Grossi ya kare matakin a wata hira da ya yi da CNN a farkon makon nan, inda ya ce: "Jefa zargi ba shi ne aikina ba. Karewa da daƙile bala'i shi ne aikina. Na sha yin gargaɗi cewa bai kamata a kai wa wata tashar nukiliya hari ba."

Grossi ya nemi a ci gaba da tattaunawa bayan ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

"Ci gaba da tattaunawa da IAEA, ita ce babbar hanyar cimma matsaya ta difilomasiyya," a cewar Grossi a dandalin X.

"Na nemi na haɗu da Ministan Harkokin Waje na Iran Abbas Araghchi cikin gaggawa."

IAEA ta ce masu saka ido suna Iran a lokacin yaƙin amma sun guje wa yin aikinsu saboda kare lafiyarsu, amma yanzu sun shirya domin ci gaba da aiki.

Buƙatar gaggawa kan IAEA

Da yake magana a Austria ranar Laraba, Grossi ya ce "babban abin da ya sa a gaba" shi ne dawo da ma'aikan IAEA bakin aiki a tashoshin Iran - musamman waɗanda aka kai wa hari ranar 13 ga watan Yuni - domin ganin irin ɓarnar da aka yi.

Da aka tambaye shi kan makamashin da ta riga ta ingata, Grossi ya ce Iran ta aika masa wasiƙa ranar 13 ga watan Yuni cewa za ta ɗauki matakai "na musamman" domin kare yaɗuwar sinadarai da kuma kayan aiki.

Amma ya ce wasiƙar ba ta ƙunshi wasu cikakkun bayanai ba.

"Ba su yi cikakken bayani kan abin da hakan ke nufi ba, amma dai suke nufi kenan. Za mu iya cewa sinadaran suna wurin," a cewarsa game da tunanin cewa ba a lalata su ba.

A wani taron na daban, Grossi ya tabbatar cewa akwai sinadarai da aka gano sun yaɗu a cikin tashoshin Fordo da Natanz amma ba su yaɗu zuwa waje ba.

"Bai kamata a kai wa wata tashar nukiliya hari ba saboda haɗarin da ke tattare da yaɗuwar sinadarai masu guba," in ji Grossi.

Idan ta soke duka hulɗa da IAEA, ƙasashen duniya za su rasa bayanai akai-akai da suke samu daga shirin ƙasar.

Jami'an difilomasiyyar ƙasashen Yamma na nuna damuwa cewa hakan zai jawo ficewa ta farko daga hukumar tun bayan wadda Koriya ta Arewa ta yi a 2003.

Yanzu makomar hukumar ta dogara ne kan abubuwa biyu: ko hukumomin Iran za su aiwatar da ƙudirin dokar, ko kuma yunƙurin Grossi zai yi amfani kafin lamarin ya ɓaci gaba ɗaya.