Abinda ya kamata ku sani kan Euro 2024 da za a fara Juma'a

Asalin hoton, Getty Images
Za a fara gasar cin kofin nahiyar Turai ranar Juma'a gasa ta 17 da ake kira Euro 2024 da Jamus za ta karbi bakunci.
Ana kuma sa ran buga wasan karshe ranar 14 ga watan Yuni, kuma duk wadda ta yi nasara za ta buga wasan karshe da duk wadda za ta lashe Copa America na bana.
Sunan kofin shi ne 2025 CONMEBOL–UEFA Cup of Champions da aka kulla yarjejeniya tsakanin nahiyar Turai da ta Kudancin Amurka .
Za a kara a Euro 2024 tsakanin tawaga 24, inda Georgia ce kadai da za ta fara buga gasar nahiyar Turai a karon farko a tarihi.
Italiya ce mai rike da kofin Euro 2020, bayan da ta doke Ingila a wasan karshe a bugun fenariti a Wembley.
Yadda aka zabi Jamus a matakin mai masaukin baki:
Ranar 8 ga watan Maris din 2017 aka sanar da cewar Jamus da Turkiya na zawarcin gudanar da Euro 2024 - bayan da wa'adin da aka gindaya ga masu takara ya cika ranar 3 ga watan Maris din 2017
Ranar 27 ga watan Satumba a birnin Nyon a Switzerland aka tabbatar da Jamus ce za ta shirya wasannin Euro 2024.
Filayen da za a buga wasannin:

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jamus tana da filaye da dama wadanda suka kai darajar da Uefa ta gindaya cewar daga karamain filin da zai dauki 'yan kallo 30,000 zuwa sama da samar da tsaro da wuraren kwana da hanyaoyi da dai sauransu.
Cikin fili 10 da za a buga Euro 2024, an yi amfani da tara a gasar cin kofin duniya a 2006 da suka hada da Berlin da Dortmund da Munich da Cologne da Stuttgart da Hamburg da Leipzig da Frankfurt da kuma Gelsenkirchen.
Fili na 10 kuwa shi ne Dusseldorf, wanda ba a yi gasar kofin duniya a 2006 ba, amma ya karbi bakuncin gasar kofin duniya a 1974 da kuma Euro 1988.
Sauran filayen da ba a dauka ba a Jamus don buga Euro 2024 ciki sun hada da na Hanover da Nuremberg da Kaiserslautern da kuma na Bremen har da na Borussia Mönchengladbach.
Tikitin kallon wasannin:
Hukumar kwallon kafa ta Turai tana sayar da tikitin kallon wasannin kai tsaye a shafinta na yanar gizo, sannan ta bai wa hukumar kwallon kafar tawaggogin da za su kara a gasar tikitin da za a sayar ga magoya baya.
Tun daga ranar 3 ga watan Oktoban 2023 aka fara sayar da tikiti, yayin da aka ware 10,000 ga magoya bayan tawagogi don kallon wasannin cikin rukuni da kuma tikiti 6,000 ga magoya bayan tawagogi a zagaye na biyu.
Haka kuma Uefa ta tanadi 7,000 ga magoya bayan tawagogi don kallon daf da karshe da kuma tikiti 10,000 ga magoya bayan da za su kalli buga wasan karshe.
An samu bukatar neman sayen tikiti miliyan 50 daga kasashe 206, Bayan Jamus da suka bukaci tikiti da yawa, an samu magoya bayan Turkiya da Hungary da Ingila da Albania da kuma Croatia da suka bukaci tikiti da yawa.
Farashi kan kama daga matsakaici Yuro 30 duk kujerar da za zauna bayan raga a karawar cikin rukuni da kuma Yuro,1,000 a wajen zaman kallon wasan karshe.
Tawagogin da za su buga Euro 2024:

Asalin hoton, Getty Images
Cikin tawagar 24 da za ta buga wasannin da za a fara a Jamus daga ranar Juma'a 14 ga watan Yuni, guda 19 daga cikin sun kara a fafatawar Euro 2020.
Daga cikinsu har da da mai rike da kofin Italiya da wadda ta yi ta biyu Ingila da Faransa da Croatia da kuma Portugal .
Wadanda suka samu gurbin shiga gasar bana ba tare da rashin nasara ba, sun hada da Faransa da Ingila da Belgium da Hungary da kuma Romania.
Albania da kuma Romania sun samu damar shiga gasar bana, bayan da suka kasa halartar ta Euro 2020.
Wannan shi ne karon farko da Serbia da kuma Slovenia za su buga gasar cin kofin nahiyar Turai tun bayan Euro 2000.
Manya a Turai da ba su samu damar shiga gasar bana ba sun hada da Sweden da Rasha da Wales.
Wannan shi ne karon farko da Sweden ba za ta buga gasar ba tun bayan Euro 1996 kuma karo biyu a jere da ta kasa kai bantenta a babbar gasar tamaula ta duniya, bayan gasar cin kofin duniya a Qatar a 2022
An hana Rasha shiga wasannin Euro 2024, sakamakon hare-haren yaki da take ta kai wa Ukraine.
Kasar Yugoslavia ce ta farko da aka hana shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a tarihi a 1992.
'Yan wasan kowacce tawaga:
An kara yawan 'yan wasan da kowacce tawaga za ta je da su Euro 2024 daga 23 sun koma 26.
Tawaga za ta iya mika sunan 'yan wasa daga 23 mafi karanci da kuma 26 mafi yawa, bayan da aka ajiye wa'adin mika sunaye zuwa 7 ga watan Yuni.
Alkala wasan Euro 2024:
Cikin watan Afirilun 2024 aka sanar da rafli 19 da za su busa wasannin 51 a gasar har da wani daga Argentina daga cikin tsarin da aka kulla yarjejeniya tsakanin hukumar kwallon kafa ta Turai da ta Kudancin Amurka.
Haka kuma an sanar da nada rafli 12 da za su taimaka wajen gudanar da aiki da mutum 20 da za su kula da na'urar da ke taimakawa alkalin wasa yanke hukunci wato VAR.
Wasannin cikin rukuni - Tun ranar 10 ga watan Mayu UEFA ta sanar da ranar da za ta raba jadawalin gasar Euro 2024.
An kuma gudanar da bikin jadawalin ranar 2 ga watan Disamba.
Rukunin farko

Asalin hoton, Getty Images
- Germany
- Scotland
- Hungary
- Switzerland
Wasannin da za a buga a rukunin fako:
14 June 2024 Germany da Scotland
Fußball Arena München, Munich
15 June 2024 Hungary da Switzerland
Cologne Stadium, Cologne
19 June 2024 Germany da Hungary
Stuttgart Arena, Stuttgart
19 June 2024 Scotland da Switzerland
Cologne Stadium, Cologne
23 June 2024 Switzerland da Germany
Frankfurt Arena, Frankfurt
23 June 2024 Scotland da Hungary
Stuttgart Arena, Stuttgart
Rukuni na biyu

Asalin hoton, Getty Images
- Spain
- Croatia
- Italy
- Albania
Wasannin da za a buga a rukuni na biyu:
15 June 2024 Spain da Croatia
Olympiastadion, Berlin
15 June 2024 Italy da Albania
BVB Stadion Dortmund, Dortmund
19 June 2024 Croatia da Albania
Volksparkstadion, Hamburg
20 June 2024 Spain da Italy
Arena AufSchalke, Gelsenkirchen
24 June 2024 Albania da Spain
Düsseldorf Arena, Düsseldorf
24 June 2024 Croatia da Italy
Leipzig Stadium, Leipzig
Rukuni na uku

Asalin hoton, Getty Images
- Slovenia
- Denmark
- Serbia
- England
Wasannin da za a buga a rukuni na uku:
16 June 2024 Slovenia da Denmark
Stuttgart Arena, Stuttgart
16 June 2024 Serbia da England
Arena AufSchalke, Gelsenkirchen
20 June 2024 Slovenia da Serbia
Fußball Arena München, Munich
20 June 2024 Denmark da England
Frankfurt Arena, Frankfurt
25 June 2024. England da Slovenia
Cologne Stadium, Cologne
25 June 2024 Denmark da Serbia
Fußball Arena München, Munich
Rukuni na hudu

Asalin hoton, Getty Images
- Poland
- Netherlands
- Austria
- France
Wasannin da za a buga a rukuni na hudu:
16 June 2024 Poland da Netherlands
Volksparkstadion, Hamburg
17 June 2024 Austria da France
Düsseldorf Arena, Düsseldorf
21 June 2024 Poland da Austria
Olympiastadion, Berlin
21 June 2024 Netherlands da France
Leipzig Stadium, Leipzig
25 June 2024 Netherlands da Austria
Olympiastadion, Berlin
25 June 2024 France da Poland
BVB Stadion Dortmund, Dortmund
Rukuni na biyar

Asalin hoton, EPA
- Belgium
- Slovakia
- Romania
- Ukraine
Wasannin da za a buga a rukuni na biyar:
17 June 2024 Romania da Ukraine
Fußball Arena München, Munich
17 June 2024 Belgium da Slovakia
Frankfurt Arena, Frankfurt
21 June 2024 Slovakia da Ukraine
Düsseldorf Arena, Düsseldorf
22 June 2024 Belgium da Romania
Cologne Stadium, Cologne
26 June 2024 Slovakia da Romania
Frankfurt Arena, Frankfurt
26 June 2024 Ukraine da Belgium
Stuttgart Arena, Stuttgart
Rukuni na shida

Asalin hoton, Getty Images
- Turkey
- Georgia
- Portugal
- Czech Republic
Wasannin da za a buga a rukuni na shida:
18 June 2024 Turkey da Georgia
BVB Stadion Dortmund, Dortmund
18 June 2024 Portugal da Czech Republic
Leipzig Stadium, Leipzig
22 June 2024 Georgia da Czech Republic
Volksparkstadion, Hamburg
22 June 2024 Turkey da Portugal
BVB Stadion Dortmund, Dortmund
26 June 2024 Georgia da Portugal
Arena AufSchalke, Gelsenkirchen
26 June 2024 Czech Republic da Turkey
Volksparkstadion, Hamburg











