Ƴan Barcelona huɗu ne cikin tawagar Sifaniya a Euro 2024

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Sifaniya tana cikin waɗanda za su buga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a fara cikin watan nan a Jamus, wato Euro 2024.
Za a fara wasannin daga 14 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yuli, kuma Italiya ce ke rike da kofin Euro 2020 da ta lashe a Wembley, bayan cin Ingila a bugun fenariti.
Ƴan wasa hudu ne daga Barcelona da za su wakilci kasar da koci, Luis de la Fuente ya gayyata da ya hada da Pedri da Fermin Lopez da Ferran Torres da kuma Lamine Yamal.
To sai dai kuma Pau Cubarsi daga Barcelona bai samu shiga cikin waɗanda za su buga gasar ta kakar nan ba.
Ranar Asabar Sifaniya ta buga wasan sada zumunta, inda ta doke Ireland ta Arewa 5-1 daga nan ta je Jamus.
Wadanda suka ci mata ƙwallayen sun hada da Pedro Gonzalez Lopez da ya zura biyu a raga sai Alvaro Morata da Fabian Ruiz da kuma Mikel Oyarzabal da kowa ya ci ɗaya.
To sai dai Ireland ta Arewa ce ta fara cin ƙwallo a minti biyu da take leda ta hannun Daniel Ballard a karawar da aka yi a filin Real Mallorca da ake kira Son Moix.
Tawagar Sifaniya za ta fara wasa ranar 15 ga watan Yuni, inda za ta fuskanci Croatia a Berlin a rukuni na biyu da ya hada da Albania da mai rike da kofin Italiya.
Filin da Sifaniya za ta kara da Croatia a Berlin a nan ne Barcelona ta doke Juventus ta lashe Champions Legue na biyar jimilla.
Tawagar Sifaniya 26 da za su buga Euro 2024 a Jamus
Masu tsaron raga:
- Alex Remiro (Real Sociedad)
- David Raya (Arsenal)
- Unai Simon (Athletic Bilbao)
Masu tsaron baya:
- Alex Grimaldo (Bayer Leverkusen)
- Aymeric Laporte (Al Nassr)
- Dani Carvajal (Real Madrid)
- Daniel Vivian (Athletic Bilbao)
- Jesus Navas (Sevilla)
- Marc Cucurella (Chelsea)
- Nacho (Real Madrid)
- Robin Le Normand (Real Sociedad)
Masu buga tsakiya:
- Alex Baena (Villarreal)
- Fabian Ruiz (France Paris Saint-Germain)
- Fermin Lopez (Barcelona)
- Martin Zubimendi (Real Sociedad)
- Mikel Merino (Real Sociedad)
- Pedri (Barcelona)
- Rodri (Manchester City)
Masu cin ƙwallaye:
- Alvaro Morata (Atletico Madrid)
- Ayoze Perez (Real Betis)
- Dani Olmo (RB Leipzig)
- Ferran Torres (Barcelona)
- Joselu (Real Madrid)
- Lamine Yamal (Barcelona)
- Mikel Oyarzabal (Real Sociedad)
- Nico Williams (Athletic Bilbao)











