Har yanzu ana neman ƙananan yara shekaru biyu bayan girgizar ƙasar Turkiyya

Emir Gultekin, Asel Kilic da Sercan Hasan Kosar
Bayanan hoto, Tsawon shekara biyu dangin Emir Gultekin mai shekara huɗu (a hagu), da Asel Kilic, mai shekara biyar (a tsakiya) da Sercan Hasan Kosar mai shekara biyu (a dama) na ta nemansu
    • Marubuci, Berza Simsek
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Turkish
  • Lokacin karatu: Minti 5

Lokacin da bala'in girgizar ƙasa na biyu ya faɗa wa kudancin Turkiyya ranar 6 ga watan Fabarairun 2023, tare da hallaka mutum sama da 53,500, an shiga aikin ceto ba ji ba gani. To amma har yanzu shekara biyu bayan balai'in akwai gomman iyalai da har yanzu suke neman 'ya'ya da 'yan'uwansu. Aƙalla 30 daga cikin waɗanda suka ɓatan yara ne.

Amir mai shekara huɗu yana gida tare da iyaye da 'yan'uwansa lokacin da aka yi girgizar ƙasar. An samu gawar mahaifiyarsa da mahaifinsa da kuma ɗan'uwansa mai shekara 10 a cikin ɓuraguzan gidansu a birnin Antakya da ke kan iyaka da Syria. To amma har yanzu ba wata alama tasu.

Gwaggonsa Nursen Kisa ta isa gidan da ya rushe bayan sa'a ɗaya da aukuwar girgizar ƙasar, inda ta shafe mako biyu tana jira yayin da ake ci gaba da neman.

Ta ce sun yi tsammanin za a gan shi ko kuma aƙalla wani tsumma na kayan da yake sanye da su, ko dai wani abu na alamunsa. To amma ba a ga komai ba, a cikin ɓuraguzan ko daga cikin gawarwakin.

Ege da Emir na wasa a gida
Bayanan hoto, Emir (a dama) na wasa a gida tare da wansa Ege, rana ɗaya kafin girgizar ƙasar

Tun daga wannan lokaci, Nursen ta duƙufa domin tabbatar da ganin ana gano shi.

Ta kai rahoton ɓatansa a ofishin 'yansanda, inda sai bayan wata uku ta samu bayani daga hukumomi a kan Emir, inda suka ce babu wani bayani da ke nuna cewa Emir ya ɓace ne.

Wannan ya sa aka fara aikin neman tun daga farko , yayin da a yanzu Nursen ta sanya hotunan Emir ɗin a dukkanin shafukan sada zumunta da muhawara da zummar ko wani zai gane shi. Sannan ta ziyarci gomman gidajen marayu a faɗin ƙasar ta Turkiyya.

Hatta kabarin 'yar'uwarta wato mahaifiyar Emir sai da aka tono inda aka ɗebi ƙwayoyin halittarta aka gwada da na gawarwakin mutanen da aka ayyana a matsayin waɗanda ba a gano asalinsu ba. To amma duk da haka ba wani bayani da aka samu kan Emir.

Yara nawa ne suka ɓace?

Bayan shekara biyu da wannan bala'i na girgizar ƙasa har yanzu babu ana samun rahotanni masu karo da juna a kan yawan mutanen da suka ɓace.

A watan Afirilu na 2023, wato wata biyu bayan girgizar ƙasar, an shigar da rahoto kan ɓatan mutum 297, inda 86 daga cikinsu yara ne, kamar yadda ministan harkokin cikin gida na lokacin ya bayyana.

A watan Nuwamba na 2024, ministan cikin gida na yanzu, Ali Yerlikaya, ya sanar da cewa har zuwa lokacin ba a ga mutum 75 da girgizar ƙasar ta rutsa da su ba. Kuma ya ce talatin daga cikinsu yara ne.

Wata 'yar tsana a cikin ɓuraguzan wani gini

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bayan shekara biyu da bala'in har yanzu ana samun rahoton da ke karo da juna a kan yawan mutanen da suka ɓace

Sai dai babbar jam'iyyar hamayya a ƙasar ta Turkiyya ta ce tana da jerin sunayen mutum 140 da suka ɓace, kuma 38 daga cikinsu yara ne. Jam'iyyar ta ce ta nuna wa Mista Yerlikaya sunayen, amma ba ta samu wata amsa ba daga gare shi - kamar yadda ta sheda wa BBC.

Ma'aikatar cikin gidan ba ta yi la'akari da sunayen mutanen da suka ɓace ba, waɗanda 'yan'uwansa a hukumance suka amince cewa sun rasu, in ji Sema Gulec, mai magana da yawun wata gidauniya da aka kafa domin neman bayani kan mutanen da suka ɓace.

Ta ce, tana ganin wannan ne dalilin da ya sa ake samun alƙaluma masu karo da juna.

Bayan girgizar ƙasar akwai zargi da dama akan ɓatan yaran da aka ceto da rai daga cikin ɓuraguzai, wanda hakan ke nuna cewa ƙila an sace su ne.

To amma hukumomi sun musanta hakan.

A watan Janairu na 2024, jam'iyya mai mulki da abokiyar haɗakarta sun ga bayan wani yunƙuri a majalisar dokoki na kiran a yi bincike kan yaran da suka ɓace.

Ta yaya hukumomi suke neman waɗanda suka ɓace?

A shekarar da ta gabata an kafa wata hukuma ta bincike kan mutanen da suka ɓace, a ƙarƙashin ma'aikatar cikin gida.

Wannan hukuma na amfani da hanyoyi da dabaru da dama wajen neman mutanen da suka ɓace in ji SEma Gulec, wadda ita ma ɗanta mai shekara 24 na daga adanda suka ɓace.

Mutane sun tattaru domin tunawa da waɗanda suka rasa a girgizar ƙasar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mummunar girgizar ƙasar biyu ta hallaka sama da mutum 53,500 a kudancin Turkiyya da sama da 5,500 a Syria

To amma jagororin hamayya na zargin hukumomi da aikata ba daidai ba ko rashin iya aiki, inda suka bayar da misalin wata matashiya, wadda aka binne da wani suna daban, wadda kuma aka tono ta bayan shekara ɗaya aka gano ainahin bayaninta saɓanin na da.

''Akwai wataƙila gomman mutanen da aka binne da wani suna daban,'' in ji Nermin Yildirim 'yarmajalisa ta jam'iyyar hamayya.

Hak kuma ta ce an kwashe ɓuraguzan wasu gidajen, kafin gudanar da hoto ko binciken da ya dace, inda ta bayar da misalin wani gida a Antakya inda har yanzu babu wani bayani a kan wasu mutum 48.

BBC ta nemi tattaunawa da hukumomin ƙasar da abin ya shafa amma sun ƙi cewa komai.

Bayanai masu tayar da hankali

Har yanzu cikin ƙunci da damuwa iyalan waɗanda suka ɓace na neman bayani kan 'yan'uwan nasu.

"Ba su gudanar da bincike sosai ba, kafin su kwashe ɓuraguzan, kuma ba ta yadda za mu hana su," in ji Ayse Ambarcioglu wadda ta rasa 'yar'uwarta da kuma jaririyar 'yar'uwar tata, waɗanda har yanzu ba labari a game da su.

Ta ce yanzu bayan shekara biyu, me ya kamata hukumomi su yi? Aƙalla ya kamata a ce ko da wani ɗan ƙashi guda ɗaya sun kawo sun nuna mana su ce wannan na 'yar'warki ne - ta faɗi hakan cike da alamu na rashin ƙwarin guiwa.

Hotunan wasu daga waɗanda ake nema har yanzu
Bayanan hoto, Har yanzu ba wani bayani kan neman tagwaye Duru da Ipek Koyuncu, masu shekara huɗu da Irem Karaca mai shekara 12 da Umay Kisacam mai wata shida

"Ko da ƙashi ɗaya aka samu nasu hankalinmu zai kwanta, to amma ba abin da aka samu," in ji Caner Yurdakul, wadda 'yar'uwarta da mijin 'yar'wartata da kuma tagwayensu masu shekara huɗu suka ɓace a girgizar ƙasar.

Biranen da wannan bala'i ya faɗa wa a kudancin Turkiyya na cike da irin wannan alhini na rashin samun bayani game da 'yan'uwa. To amma dangi da dama da suka rasa 'yan'uwan su ƙudiri aniyar ci gaba da neman bayani.

''Ba wani abu da zai tabbatar cewa ɗan 'yar'uwata Emir ya rasu ko yana da rai," in ji Nursen Kisa. "Ba zan taɓa miƙa wuya ba da matsin lamba in bayar da rahoton cewa ya rasu ba."