Ko jinkirin gyara dokar zaɓe zai iya sa a ɗage zaben 2027?

Zaɓe

Asalin hoton, INEC

Lokacin karatu: Minti 6

Jam’iyyun siyasa na adawa da kuma wasu kungiyoyin fararen hula a Najeriya na ci gaba da nuna damuwa kan abin da suka kira jan kafa wajen yin gyara ga dokokin zaben kasar.

Wasu daga cikin wadannan jam’iyyu sun fara zargin cewa jinkirin zai iya janyo tsaiko ga manyan zaɓukan ƙasar na 2027.

Fitattun ƴan Najeriya, ciki har da tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya kuma jagoran ƴan hamayyar ƙasar, Atiku Abubakar, wanda ya yi zargin cewa "da gangan majalisa ke jan ƙafa kan aikin gyaran dokar zaɓen" ta Najeriya.

Atiku Abubakar ya yi gargaɗin cewa ci gaba da jinkirin aikin gyaran dokar zaɓen zai iya shafar ingancin babban zaɓen ƙasar na 2027 kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X.

Har yanzu dai a doka, ana amfani ne da dokar zaɓe ta 2022, wadda aka sanya wa hannu a cikin watan Fabrairun 2022 wajen gudanar da zaɓuka a Najeriya.

Yanzu haka wannan doka tana a gaban majalisar dokokin ƙasar, inda ake nazari da muhawara a kai da nufin gyara sassan da aka gano cewa suna da matsala ta la'akari da abubuwan da suka faru a lokacin babban zaɓen Najeriya na 2023.

'Abin da zai faru idan lokaci ya ƙure'

Masani kan shari'a, kuma malami a kwalejin horar da lauyoyin Najeriya, Dr Sulaiman Santuraki ya ce babu wata matsala game da fargabar da ake yi kan cewa yin gyara ga dokar zabe a kurarren lokaci zai iya jinkirta lokacin zaben “sai dai idan a cikin guare-gyaren ne aka canza lokacin yin zaben”.

A cewarsa ana gudanar da gyare-gyaren ne bayan an gano akwai ɓangarorin dokar da ke buƙatar gyaran.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Gyare-gyare ne da ake yi lokaci bayan lokaci, ana kuma yi ne bayan nazarin zaɓen da aka yi a baya. Bayan nazarin ne za a gano irin matsalolin da aka samu, sai a ce kafin zaɓe na gaba, akwai buƙatar a yi garambawul domin a gyara kura-kuren da aka samu."

A game da fargabar rashin aiwatar da gyaran, lauyan ya ce, "Idan ba a yi gyara ba har wani zaɓen ya zo, yana nufin za a yi amfani ne da tsohuwar dokar zaɓen, wadda aka yi amfani da ita a zaɓen baya. Wannan na nufin cewa duk kura-kuren da aka samu a wancan zaɓen, da suka kamata a gyara, ba za a gyara ba ke nan, da su za a sake wani sabon zaɓen."

A game da fargabar jinkiri kuwa, masanin shari'ar ya ce "Idan ba a kammala gyara cikin lokaci ba, wato har lokacin zaɓe ya yi, da tsohuwar dokar za a yi amfani. Amma idan an gama gyara, amma lokaci ya ƙure, zai shafi aiwatar da sababbin shirye-shiryen zaɓen."

Sai dai ya ce jinkirin kammalawa da fara aiki da sabuwar dokar na ta'allaƙa ne da irin gyare-gyare.

"Idan an yi gyara kan ɓangarorin da suke buƙatar lokaci mai tsawo kafin fara aiki, to Hukumar INEC za ta iya buƙatar ɗaga lokacin zaɓe."

Sai dai ya ce sauya lokacin zaɓe ya danganta ne da INEC, "amma ai lokacin zaɓen ma sai an kammala gyare-gyaren za a gani.

''Amma bisa yadda ake hasashen ana so a yi zaɓen da wuri, ina tunani za a kammala aikin da wuri."

Sai dai idan har lokacin ya ƙure, "INEC ta ga ba za ta iya gudanar da zaɓe a lokacin ba, ita ce za ta iya neman a ɗaga lokacin zaɓen, amma dole ta yi a cikin wa'adin gwamnatin.

Ya ce hakan zai iya kai zaɓen ya koma dab da wa'adin gwamnati mai ci, amma a cewarsa, dole ɗaga zaɓen ya zama bai wuce wa'adin gwamnatin ba.

A game da ko za a iya kammala gyare-gyaren kafin zaɓen, masanin shari'ar ya ce ya danganta da irin aikin da aka yi, domin a cewarsa za a iya kammalawa a cikin ƙanƙanin lokaci.

Sai abin da majalisa ta yi - INEC

Wani mai zaɓe

Asalin hoton, INEC

A game da irin shirye-shiryen da hukumar zaɓen Najeriyar ke yi, BBC ta zanta da mai magana da yawun hukumar, Hajiya Zainab Aminu, wadda ta ce a hukumance, suna jiran sabuwar dokar ne domin amfani da ita.

A cewarta, INEC hukuma ce mai amfani da dokokin zaɓe da dokokin ƙasa, "kuma majalisa ce ke yin dokokin da ma kwaskwarimar da ake buƙata''.

''Da farko hukumar ce da masu ruwa da tsaki da kwamitin majalisun kan zabe za su zauna su tattauna a duba wuraren da ake buƙatar gyare-gyare."

A game da ko za su iya aiwatar da gyare-gyare ko da lokaci ya ƙure, Zainab ta ce majalisa na sane da yanayin lokacin da ma duk sauran abubuwan da suke da muhimmanci game da zaɓen.

"Harkar zaɓe tana buƙatar lokaci domin aiwatar da tsare-tsare, amma majalisa na sane da matsalar lokaci''.

''Ai suna amfani da tsohuwar dokar ne wajen gyare-gyare, don haka duk gyara da za su yi, za su duba abin da Inec za ta iya ne," a cewar Zainab Aminu.

Dokokin zaɓen da ake son yi wa gyara kafin 2027

ma'aikatan INEC

Asalin hoton, Getty Images

  • Tilasta bai wa INEC kuɗin zaɓe da wuri

Dokar zaɓen 2022 ta yi tanadin cewa gwamnati ta bai wa hukumar zaɓe kuɗin gudanar da zbuka aƙalla shekara guda kafin ranar zaɓe.

To amma sabuwar dokar ta yi tanadin cewa ''dole'' ne gwamnati ta yi hakan shekara guda kafin ranar zaɓen.

  • Bai wa fursunoni damar yin zaɓe

A karon farko a tarihin Najeriya, dokar na son bai wa ɗaurarru da fursunoni dmar kaɗa ƙuri'unsu a lokacin zaɓe.

Sabon ƙudurin ya yi tanadin bayar da damar yi wa ɗaurarrun rajistar zaɓe domin su zaɓi wanda suke so.

  • Hukunci mai tsauri ga masu maguɗin zaɓe

Sabuwar dokar ta tanadi hukunci mai tsauri ga waɗanda aka samu da laifin maguɗin zaɓe.

Haka kuma ta buƙaci a mayar da sayen ƙuri'a a matsayin babban laifin da za a tanadar masa tarar miliyan biyar ga wanda aka kama yana aikatawa.

A baya dai dokar zaɓe ta tanadi tarar naira 500,000 da ɗaurin shekara biyu, da kuma haramta wa mutum tsayawa takara na tsawon shekara 10.

  • Soke takarar saboda ƙarya

Sabuwar dokar ta kuma yi tanadin cewa idan ɗan takara ya gabatar da bayanan ƙarya game da kansa , kuma kotu ta gano cewa karya ya yi, kotun za ta soke takararsa da kuma jam'iyyar da ya tsaya takarar.

''Duka jam'iyyar da ta tsayar da ɗan takarar da bai cancanta za ta fuskanci tarar aƙalla naira miliyan 10'', kamar yadda sabuwar dokar ta nuna.

  • Tantance alamomin jam'iyyu da sunaye a kan lokaci

Sabuwar dokar ta kuma yi tanadin cewa dole ne INEC ta bai wa jam'iyyu aƙalla kwana 60, domin ta rubuta wa kowace jam'iyya ta gayyato su tare da ƴantakararsu domin su duba sunayensu da alamomin jam'iyyunsu ko yadda aka rubuta sunayen jam'iyyun akan takardun zaɓe.

Haka kuma sabuwar dokar ta ce jam'iyyun na da kwana biyu domin bai wa INEC amsa kan buƙatar dubawa.

A dokar 2022 kwana 20 kawai INEC ke bai wa jam'iyyu domin zuwa su duba sunayen nasu, amma a sabuwar dokar an tanadi kwana 60.

  • Tura sakamakon zaɓen kowace rumfa ta na'ura

A yanzu manyan jami'an zaɓe a kowace rumfa za su ''tura'' sakamakon zaɓen kowace rumfa da adadin mutanen da aka tantance, zuwa cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta gaba ta hanyar amfani da na'ura.

Dokar zaɓen 2022 ta yi tanadin kai sakamakon zaɓen a rubuce, bayan sanya hannun wakilan jam'iyyu da sauran masu ruwa da tsaki a matakin rumfar zaɓe.

  • Damar INEC ta sake nazarin sakamako kan sharaɗi biyu

Sabuwar dokar ta kuma bai wa INEC damar sake nazarin sakamakon zaɓe tare da soke shi cikin kwana bakwai, amma bisa sharaɗi guda biyu.

INEC ta samu rahoto daga jami'inta sannan ta tabbatar cewa an bayar da sakamakon ne bisa ''tursasawa'' da tabbatar da cewa an saɓa ƙa'idojin tattara sakamakon zaɓe.

A baya kotu ce ke da alhakin dubawa tare da soke sakamakon da jami'in zaɓe ya bayar.

  • Taƙaita kuɗin da ake kashewa da na tallafi

Sabuwar dokar ta buƙaci a taƙaita abin da jam'iyyu ke kashewa wajen yaƙin neman zaɓe.

Dokar ta ƙara kuɗin da za a iya kashewa a yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa daga naira biliyan 5 zuwa naira biliyan 10.

Ga masu neman kujerar gwamnan an ƙara kuɗin da za su iya kashewa a yaƙin neman zaɓe daga nira biliyan 1 zuwa naira biliyan 3.

Kujerun ɗan majalisar dattawa kuwa an ƙara kuɗin yaƙin neman zaɓensu daga naira miliyan 100 zuiwa naira miliyan 500, sai majalisar tarayya daga naira miliyan 70 zuwa naira miliyan 250.

Yayin da aka ƙara kuɗin yaƙin neman zaɓen ɗan majalisar jiha daga naira miliyan 30 zuwa naira miliyan 100, sai shugaban ƙaramar hukumar daga naira miliyan 30 zuwa naira miliyan 60.