Tinubu ya buƙaci a bi doka da tsari a zaɓukan Abuja

Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci mazauna birnin Abuja su fito domin kaɗa ƙuri'un cikin tsari da bin dokokin hukumar zaɓe.
Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar a ranar Juma'a, shugaban ƙasar ya buƙaci masu kaɗa ƙuri'a su kauce wa tayar da fitina.
''Shi tsarin dimokraɗiyya ana jin daɗinsa ne kawai ta hanyar kwanciyar hankali, nutsuwa da kuma mutunta juna'', in ji sanarwar.
Haka ma shugaban ƙasar ya buƙaci hukumar INEC ta bi tsari ta hanyar tabbatar da tantance masu zaɓe a kan lokaci.
Sannan ya yi kira ga hukumar ta tabbatar ta yi aiki da sabbin dokokin zaɓe na 2026 da aka yi wa gyaran fuska.

















